← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 41

Sashe 24

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ga wanda ba suyi payment ba su hanzarta su biya before end of this week👍 Yanzu littafi Zai fara 🔥🔥🔥 (08103884440) ayimun magana direct

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 17-18

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️

*Mallakin Hafsat Bature Moh'd*
~BossBature~
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• bayan Jahad ta kammala wankan ta canza kaya ixuwa doguwar riga, hawa tayi itama saman gadon kusa da hosana suna daf da juna tace "hosana me kike tunani game da hafsat da mommynsu? Anya ba wani abu suka shirya mana ba? Kada fa ace so suke yi su kashe mu ko su zubar damu shiyasa suka tsara mana hakan,' tayi maganar cikin nuna damuwa a fuskarta,
Hosanna tace "jahad ni nasan abunda mommynsu hafsat ta shirya mana, fuska biyu tayi mana wlh, so take ta nuna mana kulawa sosai don mu saba da ita yadda in yaya Omar yazo yace zai tafi damu muƙi binsa saboda sun nuna mana kulawa.........' dakatawa tayi da maganar jin alamun tunkarowar mutun ɗakin da suke ciki,
Hafsat ce ta shigo ciki fuskarta É—auke da murmushi tace "sannunku My sisters ya jikin naku"? Ta tambaya ayayin da take samun wuri saman room sofa É—in tazauna,
"Alhamdulillah da sauƙi" suka bata amsa atare, mayar da idonta tayi gefen kujerar da take zaune leda ce ajiye wadda taba Jahad ta ruƙe mata bayan ta fito daga store, hannu tasa ta ɗauki ledar tana cewa "Lahh Jahad wannan ae naku ne na siya maku, Chocolate ne da sweet ko bakwa so ne"? ta tambaya tana kallonsu,
Suka haÉ—a baki wurin cewa "muna so," sannan jahad ta sauko daga saman gadon tasanya hannu biyu takar6a tana fadin "mungode Aunty hafsat,"
Murmushi hafsat tasaki tare da cewa "Naji daÉ—in sunan nan da kuka kira ni dashi, amma nafison ku kira ni da Sister Hafsat akan aunty hafsat zanfi jin daÉ—in hakan,"
Murmushi su kayi su dukan su, kafin daga bisani Jahad ta curo musu chocolate cookies ɗin data siya musu, guda biyu ta curo ta ɗauki ɗaya sannan ta miƙa ma hosana suka 6are suna sha,
Har lokacin idon hafsat na akansu kallonsu takeyi gwanin burgewa, dama tun ranar farko data fara cin karo dasu sun burgeta kawai baƙin hali ne irin nata yasa bata nuna ba,
ÆŠagowa su kayi jin alamar shigowar mutun, AUNTY BABBA ce ta shigo fuskarta É—auke da murmushi tana kallonsu tace "Ya jikin naku My daughters?
haɗa baki su kayi wurin cewa "da Sauƙi Alhamdulillah,"
Jinjina kanta tayi kafin daga bisa ni ta kuma cewa "Yakamata ku fito mana kuzauna a palour ko kallo ne kuyi zai É—ebe muku kewa kuma zaku samu nishaÉ—i,"
Amsa mata sukayi da "Toh" sannan suka sauko daga saman gadon hannun jahad ruƙe da ledar choculate ɗinsu,
A falon suka samu wuri saman gujera mai mazaunin mutun biyu su ka zauna tare da mayar da hankalin su Wurin kallon shirin da akeyi a tashar Bollywood, tuni kallon ya ɗauke musu hankali saboda daɗin dramar da suke yi ta india, dama kuma ga chocolate ɗinsu suna sha sai abun yaƙara nutsar dasu gaba ɗaya,
AUNTY BABBA kuwa wuri tasamu ta zauna agefen gadon tana fuskantar hafsat tace "Sannu Madam,"
tashi hafsat tayi zaune tana cewa "Mommy dama ina son magana dake! Wannan canjin dana gani a tattare dake shin dagaske ne? Ko duk shiri ne? ta tambaya tana kallonta don jin amsar da zata bata,
ɗan ƙayataccen murmushi AUNTY BABA tasaki tare da cewa "Hafsat kenan ! Ke naso ki fara faɗamun gaskiyar lamarin nan shin dagaske ne yanzu kin fara jin tausayin yaran nan?
"Mommy da gaske ne, natausaya musu sosai saboda bugun rashin imanin da kika yi musu, kuma ayanzu bana son wani yaƙara ƴunƙurin cutar dasu daga ni har KE !
Ajiyar zuciya aunty babba tasaki tana mai jinjina kai tace "Shin ya maganar matar da kika amsar ma kuÉ—i kusan miliyan shidda? Mayar mata su zakiyi kenan.....?
Hafsat tace "wannan ni tashafa mommy, zan san yarda zanyi da ita, in ma bazaiyiyu ba just zan mayar mata da kuÉ—inta ne,"

ɗan ta6e baki AUNTY BABBA tayi daga bisani tace "Shikenan Daughter but lemme remind u something, kin manta da uban bashin da Ake bin ki kenan u ave to think about it, how can u pay all ur debt? Dole ki buƙaci kuɗi ....................tana kai ƙarshen maganarta, ta tashi ta fuce tana faman sakin shu'umin murmushi aranta tana cewa "Yarinya kenan! Naki wasa ne,"
**********💪💪💪***************
Chapter 24 · 0% Book details