← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 41

Sashe 7

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ihun da hosana tayi na ƙarshe wanda ya karaɗe ko'ina harya sa Hafsat dake kwance ɗakinta saman gadonta farkawa a firgice, ta diro daga saman gadonta jiki na rawa ta fito ta tunkari inda sautin ke fita cikin hanxari ta faɗo ɗakin,
  gabanta ne yayi wani irin bugu ganin Momynta a tsaye tana huci kamar wata zakanya, ga kuma twins ɗin da Omar ya kawo a baje ƙasa jina jina musamman hosana an zubda jini
   Hankali tashe hafsat tace "Mommy me nake gani haka !! Me kika yi masu ne !! Kashe su Ki kayi da hannun ki !!!
   tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa "Eh kashe su nayi,akwai magana ne ! babu ruwanki dani ki koma ɗakinki zai fi miki,"
  Cikin rauni hafsat tace "mommy duk rashin imani na bazan iya aikata abunda kika aikata ma yaran nan ba, ashe baki da Imani ko misƙala zarratin ! Kisan kai da hannun ki........'
  Bata idasa maganar ba saboda jin saukar wani irin zazzafan mari a kuncinta, tashin hankali da ba'a sama shi rana,
    Saboda zafin marin da aunty babba tayi ma hafsat yasata dafe kumatun ta ido jawur take faɗin "Mommy yau ni kika mara da hannun ki"?
    "Naje na mara ! duk kece sular da kika 6atamin raina harna aikata abunda na aikata yanzu!!"
    shiru hafsat tayi yayin da idonta ke fitar da wasu irin siraran hawaye masu zafin gaske,
  Jikin aunty babba ne yayi mugun sanyi ganin hawayen dake fita a idon hafsat ƴarta tilo,
    Cikin tashin hankali tace "ba da son raina nayi hakan ba ! Hafsat ke kika 6atamun rai da 6acin ranki na kwanta, cikin daren nan na fito saboda zuciyata batamun daɗi kawai naga yarinyar nan jahad ta nufo ɗakin nan shine na biyota in ga mai zatayi ashe wasiƙa zata rubutama Omar akan abunda muke aikata musu, da nufin inyazo su bashi.......yanzu yaya zanyi hafsat....na kashe su ba'a hayyacina ba...In Omar yazo bansan me zan faɗa masa ba......" tayi maganar tana yarfa hannunta idonta cike tab da hawaye cikin tashin hankali,
   Murya na rawa hafsat tace "Mommy kin ja mana masifa da bala'e duka, ni banji xafin marin da kikayi mun ba, domin wannan kaɗanne akan Marin da zamu kar6a ni dake a wurin Yaya Omar wlh bazai ƙyale mu ba !! Yadda kika kashe su ke ma haka zaisa ayi maki hukuncin kisa babu ruwana ......
   Cikin shesshekar kuka aunty babba tace "Hafsat yanzu don na kashe waɗan nan tsintattun marasa galihu nima sai Omar yasa akashe ni?
   A tsiwace hafsat tace "Eh.!! dama menene alaƙarki da Shi da zai tausaya miki? Kwarama Ni zan tsira ke kuwa Yayansa kawai kike aure !! Wlh mommy kin shiga uku gaki can an garƙame ki a cell ƙarshe a yanke maki hukuncin ɗaurin rai da rai har sau biyu saboda rai biyu kika kashe.......
    Hannu aunty babba ta aza akanta tana faɗin "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un nashiga Uku Ni LAILA naja ma kaina mutuwa a lokacin da ban shirya ba,
      Jiki a mace aunty babba ta zuƙunna inda hosana take kwance a mace tana faɗin "kee!!!kee!!! tashi !! Maza ki tashi don ubanki ! Wlh baxa ku jamin bala'i ba, hafsat ɗauko mun robar ruwa a fridge dan Allah in yayyafa musu ko sun tashi
    tayi maganar tana kallon hafsat, fuce wa hafsat tayi da sauri sai gata ta dawo hannun ta ɗauke da bottle water ta miƙa mata, kar6a Aunty babba tayi jiki na rawa ta cizge murfin tashiga yayyafa ma hosana ruwan ajikinta,
   Gabansu ne ya faɗi atare ganin hosana ko motsi batayi duk sanyin da ruwan yayi hakan na nufin ta mutu kenann !!!!!!
  tuni fuskar aunty babba tayi jawur kamar wadda aka nannausa saboda tashin hankali
A ruÉ—e tace "Hafsat mun shiga uku !! Mun lalace !! Wlh ta mutu wayyo Allah na ni laila......
    Hafsat dake tsaye hankali atashe itama aruɗe tace "wlh Mommy laifinki ne, kece saurin fushin tsiya ga zafin zuciya gashi nan kin kashe su, To ni wlh babu ruwana aciki, dama ban da wata alaƙa dake haihuwata kawai kikayi.......
   ɗagowa aunty babba tayi ta kalle ta ido jawur cikin disashewar murya tace "Hafsat ni kike ce ma baki da wata alaƙa dani, saboda ƙaddara da tsautsayi sun rutsa dani.....'
   Cikin kuka hafsat tace "Ae gaskiya na faɗa mommy ! ina bacci na kin katse mun shi da wannan tashin hankalin, Allah mommy ba abunda zai hana Omar yasa a garkame ki a cell , har na hango ki cikin kayan gidan yari Allah bazasu yi maki kyau ba yadda kike haka ɗin nan........' tayi maganar tana nuna aunty babba dake zuƙunne agaban hosana kamar buhun masara,
  "Yanzu ya zamuyi ? Hafsat kar6i robar ruwan ki yayyafa ma ɗayar muga in ita zata tashi, wataƙil ita In tafarka sai in samu sassauci awurin yanke mun hukuncin......
   Cikin sauri hafsat ta kar6i robar ruwan dake hannun aunty babba ta ƙarasa inda jahad take tashiga yayyafa mata shi a fuskarta, Wani irin dogon numfashi jahad taja kafin tace "La'ila ha illallah Muhammad rasulillah....
    Ganin jahad tafarka yasa aunty babba tashi tsaye ta tunkare ta tana faɗin " Alhamdulillah saura ɗayar yaya zamuyi hafsat ? Kodai kawai mu binne gawarta a cikin garden ɗin gidan nan ne?
   Wani irin kallo hafsat tayi mata tare da cewa "ashe mommy hankalin ɗiyar roba ke gare ki? mu binne gawa acikin gidan nan ? Idan fatalwarta ta tashi fitowa ke zata fara ziyarta Allah,
   Hannu aunty babba ta aza akai tana faɗin "Ya salam duk ni naja ma kaina"
   daker jahad ta buɗe idonta wanda suka kumbura sukayi jawur, ga le6anta sunyi sutum sutum inda aunty babba takai mata naushi,
   Idonta bai sauka akan kowa ba sai kan hosana dake baje ƙasa jini duk ya wanke fuskarta......
  Da ƙarfi ta furta "Hosanaaaa !!!!!!!!!,' tamkar bakinta zai tsage yunƙurawa tayi ta tashi a tsananin razane ta ƙarasa inda hosana ke kwance ta zube saman guiwowinta tana faɗin "hosana ki tashi ! mai ya faru dake ne? Wa yayi maki haka !! Innalallahi'wa'inna ilaihirraji'una .....ta ƙarasa maganar tare da kifa kanta jikin hosanar tajima bata ɗago ba sai daga baya ta ɗago da kan nata tana faɗin "Dan Allah ku kaita asibiti kada ta mutu !! Kada narasa ƴar uwata,"
  Kallon juna su kayi sai yanzu suka mayi tunanin zuwa asibiti don sam basuyi tunanin hakan ba,
   Jiki na rawa hafsat tace "mommy ki ɗauko ta, bari naje room ɗina naɗauko mukullin mota mu tafi,"
   Aunty babba tace "Toh,ki tahomun da mayafi dan Allah"
  fucewa hafsat tayi tana faɗin "kiyi sauri mommy,"
   Cikin hanzari aunty babba ta ƙarasa jiki na rawa, ta cuccu6i hosana ta aza aka faɗarta ta fuce da ita daga ɗakin, itama jahad ta bisu abaya
    Fitowa hafsat tayi itama a lokacin har aunty babba ta buɗe back seat na motar ta kwantar da Hosana aciki itama jahad tashiga ciki sannan ta rufe,
   Su kuma suka shiga front seat hafsat na a mazaunin driver ita kuma tana a gefenta,
   Da gudu hafsat ta tada motar taja ta a tsiyace suka nufi hanyar fita daga gate ɗin gidan
   Nan take sojojin dake gadin gidan suka tunkaro su don jin ba'asi
  Aikuwa a masifance aunty babbba ta ɗaga murya tana cewa "Nice nan zan fita kar in ga wani shege ya tare mun ƙopa Wlh in bi takansa....'
  Jin muryarta yasa su kayi baya baya suka bata hanya ta wuce.......... da gudu suka miƙi titi sai asibiti, kuma duk da haka sai da sojojin nan suka biyo su abaya saboda aikinsu ne basu tsaro musamman acikin daren nan,

Suna isa asibitin gudu gudu sauri sauri Aunty babba ta É—auki hosana suka shiga ciki,da hanzari reception nurses suka karbe ta aka shiga da ita ciki, anci sa'a an samu likitan dake a bakin aiki, cikin gaggawa suka shiga duba hosana,
  Su kuwa su aunty babba da hafsat suna atsaye sai faman zagaye suke kowa cike da zullumin abunda zai biyo baya in yarinyar ta mutu, jahad kuwa tana abakin ɗakin da aka kwantar da hosana ta kwantar da kanta jikin door ɗin idonta na tsiyayar da hawaye masu ɗumi,😭
Gaba É—ayansu babu wanda ya samu bacci adaren nan saboda da tashin hankali,
   (Na zubda hawaye saboda halin da su Hosana da jahad suke ciki Ya Allah ka kawo masu ɗauki) 😭
______________________________________
Chapter 7 · 0% Book details