← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 41

Sashe 33

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Tuni General ishaq ya iso gidan ya cika tab da mutane tare da jami'an sojoji da suka rakosa, su Aunty babba sai faman rawar kai akeyi miji ya iso gari, a lokacin hafsat har ta shirya kanta itama tsaf ta kimtsa cikin haɗaɗɗen cord lace Ash colour mai adon duwatsu,rigar mai dogon hannu sai skirt ba ƙaramin kyau kayan su kayi mata ba, gashi dama takware wurin iya kashe kallabi, tare da Mommyn nata da wasu daga cikin abokanan aunty babba da suka zo dana hafsat suke taimakawa wurin tarbar baƙi da abunsha dana ci,
   "Jahad ya Omar shiru kodai ya manta damu ne"? Hussana ta faɗi fuska tamkar zatayi kuka tana kallon jahad suna zaune dab da juna daga gefen gadon hafsat,
   "Hussana bana tunanin hakan, Ya Omar yana son mu sosai ni ina da tabbacin yana sane damu,kuma zaizo ne insha Allah," acewar jahad
Hussana tace "Ni inajin tsoron a rabamu da ya Omar, wlh banso banso....'
  Kamar daga sama suka ji Muryar Aunty babba tace "Saboda ƙanin ubanki ne ko? ta faɗi ayayin da take shigowa, arazane suka miƙe tsaye su duka suna kallonta, su biyu suka shigo cikin ɗakin ita da wata hajiya, amma ita ta tsaya daga baya
   Kusa dasu taje sannan tasoma magana "Ko da gigin wasa bana so wata daga cikin ta leƙo da kanta daga cikin ɗakin nan ! Saboda Mijina ya dawo kuma banaso ya gan ku, ina fata kun gane?
  Cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa "Insha Allah aunty bazamu fito ba,"
   ta6e baki tayi sannan ta juya bayanta ta kalli matar da suka shigo tare tace "Hajjaju gafa yaran nan da nake faɗa baki, Omar yakawo min cikin gidana,"
   ƙarasa shigo wa ciki matar tayi jikinta na sanye da shadda gezna green colour tasha uban aiki a wuyan rigar, tayi ɗaurin ɗan kwalin ture kaga tsiya sannan ta yarfa gyalenta a kafaɗarta,
   Alokacin da matar ta ƙaraso Jahad taganta nan take gabanta yayi wani irin bugu zaro ido tayi tana kallonta saboda son tuna inda tasan fuskarta,
  Hajjaju kuwa tana ganin su hussana da jahad farat ɗaya ta gane su, a ɗan razane ta dafe ƙirji tare da cewa "Kaiii !!!" taja maganar da ƙarfin tana kallonsu cikin mamaki da al'ajabin wannan Ikon Allahn,
  tuni aunty babba tagama ruɗewa ganin yadda hajjaju ta razana da ganinsu, da kuma yarda jahad ta firgita itama wannan alama ce dake nuni da sun san juna kenan ko yaya,
  Cike da mamaki Aunty babba tace "Wai meke faruwa ne hajiya rabi? kinsan su ne?
  Cikin sauri hajjaju tace "A'a bansan su ba, Kamar dae nata6a ganin mai kama dasu ne,"
   tayi maganar tare da ruƙe hannun Aunty babba taja ta, suka fuce daga ɗakin,
   Kallon jahad hussana tayi tare da cewa "Jahad wacece wannan matar? Naga kin razana da ganinta,"
   "Nima so nake na tuna inda nasanta," Jahad ta faɗi tana faman cizon akaifar hannunta da takai abakinta,
  Hajjaju kuwa da taja Aunty babba suka fuce can suka nufa wurin kitchen suka tsaya, ga mutane sai faman shige da fuce suke,.
  "Dan Allah ki faɗamun gaskiya hajjaju raina na bani cewa kinsan yaran can ko? Aunty babba ta tambaya tana kallonta cike da son jin ƙarin bayani daga wurinta,
  Jinjina kai Hajjaju tayi tare da cewa "Yau naga ikon Allah, Lallai ne duk zakaran da Allah ya nufa da cara,to fa sai yayi ta, haƙiƙa nayi matuƙar mamakin yarda akai har Allah ya haɗa Omar da waɗannan yaran , kai kaga wani ikon Allah nan ! mai matuƙar ban mamaki da Al'ajabi?
  Hajjaju tayi maganar cikin nuna mamakinta,
Aunty babba kuwa cewa take yi "Hajjaju kin barni acikin duhu, wlh har kinsa hantar cikina ta kaÉ—a dan Allah kisanar dani me kika sani agame dasu?
  dariya hajjaJu tayi tare da tafa hannayenta tace "Ana bura'uba a lagos! yo ke laila da kike cewa zaki sa a zubar maki da waɗannan yaran don ki nisanta su da Omar, idan Kin toshe wannan hanyar to ita waccen ɗayar hanyar da ta ruga isa inda bakya so ya zakiyi da ita?
   gaba ɗaya fa Aunty babba ta gama rikicewa da bayanin hajjaju, cikin tashin hankali tace "wai me kike nufi ne hajjau, kiyimun bayani mana yadda zan fahimta !!!
   ta faɗi tare da ɗan jan guntun tsoki, Murmushi hajjaju tasaki sannan tace "Ni baza kiji mutuwar sarki abakina ba!kawai abunda nakeso ki sani shine babu wanda ya isa ya hana ruwa gudu sai Allah! Bakin alƙalami dai ya ruga daya bushe, Amma fa waɗannan yaran da kike gani wlh ikon Allah ne su, tunda har Allah ya haɗasu da Omar aikuwa magana ta ƙare, Yakamata kisan abunyi,'
  Hajjaju tayi maganar tare da wuce wa ciki tabar Aunty babba tsaye abakin kitchen baki asake, lokaci guda taji ta ƙara tsanarsu hussana da jahad tabbas suna tattare da wani abu yaran, duk da bata fahimci inda maganar hajjaju ta dosa ba,
  ranta ya gama 6aci tsoki ta buga tare da cewa "ta tsaya tayimun bayani amma ta tsaya yimun wasu sambatun banza dana wofi,ni duk tasa hankalina ya ƙara tashi, kuma wlh goben nan zansa a Kwashe mun su aje can azubar dasu tsakar daji, sai dae abunda bangane ba acikin maganar hajjaju wacece ɗayar hanyar da take nufi wadda ta isa inda banaso!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!? ta tambayi kanta sai dae kash babu amsa hakanan ta koma ciki tana faman sambatu aranta,
    Zumbur !! Jahad tayi tare da kallon husana tace "Wlh nasanta!! Nagane ta !! Itace matar da ta taimaka mana a asibiti har ta biya kuɗin gadon Ki husana, wlh itace matar da tasama ma SEHRISH aiki, hakan na nufin ta son inda sehrish take.....!!
  Cikin tsananin farin ciki jahad tayi maganar, hussana ma aɗan raxane tace "dagaske jahad itace tasama ma sehrish aiki? Ke nan itace kawai zata iya faɗa mana inda ƴar uwarmu take kenan,. 
   jahad tace "eh itace, nagane ta yanzu ya za'ayi muyi magana da ita, gashi aunty ta hanamu fita, amma ni dae inason magana da ita kodan saboda ta faɗa mana inda sehrish take,' jahad tayi maganar fuskarta tamkar zatayi kuka,
   Cikin sanyin murya hussana tace "Jahad kada ma musa rai don nasan bazata faɗa mana ba, ita fa ƙawar Aunty ce, kuma kinsan muguwace idan halinsu ɗaya fa? Bazata ta6a faɗa mana ba, Ni tsorona ma kada ta faɗa ma wannan muguwar auntyn inda sehrish take, suna iya zuwa su cutar da ita, Allah yasa sehrish tana lafiya banaso wani abu yasame ta.........'" tayi maganar cikin shessheƙar kuka,
   "Da gaskiyar hosana,Nima ina tunanin hakan Allah yasa karta faɗama auntyncan inda ƴar uwarmu take, amma dai ni inason naga matar na roƙeta akan ta faɗa mana inda sehrish take,yakamata musan inda take, wane hali take ciki, gashi yanzu sai mutuwa akeyi Ya Allah kasa sehrish tana araye har mu haɗu," tayi maganar idonta cike tab da hawaye,
  daga bisani ta kalli hosana tace "ki zauna hosana kada ki fito bari ni naje nayi magana da matar na roƙe ta, ta faɗamun inda rishi take,"
  Hosana tace "toh," sannan tasamu wuri ta zauna gefen gadon tana faman sauke ajiyar zuciya,
  Cikin sanɗa jahad ta futo daga kopar ɗakin ta tsaya tana ɗan leƙa kanta, mutane tagani gasu nan sai faman zarya sukeyi acikin babban falon,
   A hankali ta miƙi hanya ta soma tafiya tana faman waige-waigen neman hajjaju, ta ɗanyi nisa a tafiyar ta ta, tajiyo magana daga bayanta ana cewa "Nasan cewa ni kike nema ko"?
Cikin sauri jahad ta juyo bayanta, hajjaju ce tsaye tana kallonta fuska É—auke da murmushi,
Ajiyar zuciya jahad ta saki sannan itama ta mayar mata martanin murmushin tare da gaishe ta, hajjaju ta amsa mata da cewa "Nayi mamakin ganin ku, anan gidan ko ba'a faÉ—amun ba nasan cewa kunsha wahalar rayuwa don nasan Laila sarai muguwace bata da Imani,kuma tana sanar dani game daku a waya sai dai bansan cewa ku bane,"
Jinjina kai Jahad tayi tare da cewa "Munsha Wahala sosai tamkar ba zamu rayuwa ba,dan Allah ki faɗa mana ina Sehrish take? Munyi kewarta sosai, rabon mu da ita, tun da ta tafi aikin nan da kika sama mata,bayan wasu kwanaki hosana ta 6atar mana da wayar da muke amfani da ita wurin kiranta, shikenan rabuwarmu da ita......' jahad ta ƙarasa maganar idonta cike tab da kwalla,
   ɗan shuru hajjaju tayi tana kallonta gwanin ban tausayi kafin tace "Kiyi haƙuri, amma bazan iya shaida a ina sehrish take ba nikaina,saboda nasaba hulɗa da yara ina sama musu aiki, bazan iya tuna a wane gari nakai sehrish ba, bazan iya tunawa ba......'
  Jin hakan yasa Jahad fashe wa da kuka mai cin rai, matsawa hajjaju ta ƙara yi gab da jahad tasanya hannunta tare da dafa kafaɗunta tace"kiyi haƙuri Jahad, ina mai matuƙar jin takaicin gaza taimaka maku akan halin da kuke ciki, haƙika kun ga rayuwa, amma ni abunda nakeson sani taya akai kuka haɗu da Omar? bayan naji labarin rasuwar tsohuwa ya gigita ni matuƙa, sannan naji labarin cewa ana zargin cewa kune kuka bata poison amma bansan ya ƙarshen labarin yake ba,'. 
  Cikin shessheƙar kuka jahad tace "bayan tsohuwa ta rasu, mutane suka ce mune muka kashe ta alhalin mu bamu da masaniya akan mutuwarta, shine aka kaimu police station, munsha Wahala sosai saboda bamu da sheda, ana shirye shiryen za'a miƙa case ɗinmu kotu, hussana tayi rashin lafiya shine dalilin dayasa ƴan sanda suka tafi da ita asibiti tare dani, Acan ne Allah ya haɗamu da yaya Omar shine ya kwace mu daga hannun police ɗin kuma ya kashe case ɗin gaba ɗaya......' ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya,
  Murmushi hajjaju tasa ki tare da cewa "Allah sarki Omar mutumin kirki ne sosai, yana da tausayi inama ace tunfarko ba nan ya kawo ku ba, wlh da kun more rayuwarku,amma sai dai kash yayi kuskuren jefa rayuwarku cikin haɗari batare da sanin shi ba, Amma insha Allah Laila bazata ta6a cin nasara akanku ba,'
  Jinjina kai kawai Jahad ke yi, bayan sun ɗanyi shiru hajjaju tace "Muje ɗakin da kuke,ina son ganin ƴar uwarki danaji kin kirata da hussana, bazan manta ba itace a lokacin kwance saman medical bed ansa mata oxygen tana shaƙar numfashi cikin mawuyacin hali, Amma yanzu naganta taji sauƙi sosai jiki yayi kyau,' hajjaju ta faɗi da ɗan murmushi a fuskarta yayin da suke nufar ɗakin hafsat atare,
   Suna shiga suka samu hussana atsaye sai faman zirga-zirga take yi burinta kawai jahad tadawo kusa da ita,
   Tsayawa tayi ganin sun shigo tare da matar, Murmushi hajjaju ta sakar ma hussana tare da ƙarasawa inda take ta rungumo ajikinta, tana ɗan bubbuga bayanta tace "nasan ke baki sanni ba,sabosa lokacin kina kwance rai hannun Allah, amma ni nasan ki saboda naganki a lokacin, naji daɗi sosai dana ganki cikin ƙoshin lafiya,
   Hajjaju ta ƙarasa maganar tare da janye hussana daga jikinta, ita dai hosana kallonta kawai take yi don batasan ta ba, mayar da idonta tayi kan jahad tace "ta faɗa maki inda sehrish take?
  Jahad tace "a'a hosana, tace itama ta manta inda takaita aiki saboda ta saba kai yara aiki bazata iya tuna inda takai su ba,"
   Jin haka yasa Hosana fashewa da kuka tana cewa "..yanzu shikenan bazamu ƙara ganin sehrish ba....
  Hajjaju tace "Ki daina kuka hosana,wayace maki bazaku sake ganin sehrish ba? Ki daina wannan tunanin Insha Allah zaku haɗu da ƴar uwarku, abunda nakeso daku kawai ku cigaba da addu'a insha Allah zaku dace,"
  Jahad tace "kullum muna cikin yin addu'a,Kuma zamu cigaba da yi har illa masha Allah"
    Murmushi hajjaju ta kuma yi sannan tace "Ni zan wuce,Ku kula da kan ku,Allah ya Albarkanci rayuwarku, yaci gaba da tsare ku aduk inda zaku kasance arayuwar nan,"
  Suka amsa mata da "Amin," sannan tasa kai ta fuce tana mai jin rashin daɗin gaza taimaka masu da tayi na ƙin faɗa masu inda ƴar uwarsu take, bayan ta son inda take,
  Komawa sukayi atare suka zauna jikinsu amace, Shin mai zai biyo baya?😥
Chapter 33 · 0% Book details