Sashe 26
Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
rufe surar jikinta daga jan hankalin mutane akanta saboda tsaro,' girgiza kai sgr yayi tare da cewa "ban yarda da wannan shigar ba, shin Omar taya mutun zai iya motsi acikin wannan abun"? Ya tambaya yana nuna hijabin jikin sehrish,😂 Fashewa da dariya Omar yayi kamar kamar me, ganin yarda Sgr ya haƙiƙance akan hijabin dake ajikin yarinyar, shi a ganinsa takurace kuma mutun bazai iya motsi acikinta ba, daƙer ya dakatar da dariyar tasa ya kalli sehrish tare da cewa "Ki faɗa masa yarda kike motsi acikinta may be ya fahimta," ɗan murmushi sehrish ta saki ita kanta abun ya gama ɗaure mata kai, ɗagowa da hannayenta tayi tare da cewa "Ga hannun hijabin nan, tun da na fiddo da hannun acikinsa lafiya lau nake motsi acikinta," ta ƙarasa bayanin tana kallonsa Jingina bayansa yayi ajikin sofa ɗin tare da cewa "Its Okey, u can go,' har ta juya zata tafi Omar yace "Ya Sunan ki ne? Juyo wa tayi ta kallesa da murmushi a fuskarta tace"SEHRISH" Omar yace "masha Allah suna mai daɗi, amma menene ma'anarsa? ya tambaya yana kallonta, *kyawawan halayyu na mutun," ta bashi amsa, *ina fata zaki nuna mana waɗannan kyawawan ɗabi'un acikin gidan nan, har ma ki zama alkhairi agare mu," omar ya faɗi da ɗan murmushi a fuskarsa, duk Sgr na sauraronsu duk da ya ci gaba da dannar wayarsa, Sehrish ta amsa masa da cewa "Insha Allah," sannan ta wuce Sai lokacin Sgr yace "Ashe kana surutu har haka Omar? Kallonsa Omar yayi tare da cewa"Yarinyar ce tana tattare da wani abun al'ajabi a fuskarta shiya sanya Na sake mata," "Ba kowace baƙuwar fuska yakamata ace kana sakemawa ba irin haka ba, Mata Basu da tabbas they're trouble makers," acewar Babban yaya, ƴar dariya Omar yayi batare da cewa komai ba, Sehrish kuwa kitchen ta wuce ta zubo musu coffee tare da snacks a plate Cikin tray sannan tadawo inda suke tare da ajiye masu saman Table, Omar yace "thank u miss Sehrish," Murmushi tayi masa sannan ta juya ta nufi ɗakin azmee tunkan ta ƙarasa ɗakin nata sai ga Azmee ta fito itama ta kammala shiryawa cikin atampha ja, ta aza babban mayafi milk colour launin takalminta ƙafarta, atare suka fuce suna jiran isowar junaid, Ba da jimawa ba sai ga junaid ya fito daga upstairs yana saukowa down sai faman zabga murmushi yake yi, jikinsa na sanye da haɗaɗɗiyar shadda gezner blue colour mai maiƙo sai faman ɗaukar ido yakeyi kai kace wani sabon ango ne, shaddar tasha aiki a wuyanta tsantsararre, hannunsa na ruƙe da wayarsa haɗe da key ɗin motarsa, Lokacin daya ƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin, gaba ɗaya Marshal Omar da Sgr suka bishi da kallo, Zagayawa yayi inda babban yayan nasu yake yana isa ya manna mashi kiss agefen fuskarsa sannan yace "Zan fita, saina dawo," ko amsa bai jira ba cikin sauri ya lalla6a ya fuce yana cewa "yaya Omar kayi masa bayani, mu mun wuce ," Girgixa kai kawai SGR yayi sam ya kasa magana, wato junaid yasan cewa zai iya dakatar dashi daga fita shine yayi dabarar tserewa, Murmushi Omar yasaki tare da cewa "Junaid kenan ! komai nasa na burgewa, ya cika ƙiriniya ga shegen wayon tsiya, saboda kada ka hana shi fita shiyasa ya gudu bai jira amsarka ba," yayi maganar yana kur6ar coffee ɗin da sehrish ta kawo masu a cup, "Ina zasu je ne"? Sgr ya tambaya yana kallonsa, Omar yace "Gidan Uncle Abusufyan na aikesu, inaso zanyi amfani da gidan ne akwai wasu marayune da zan zuba acikinsa kwanan nan," Sgr yace "Omar kenan, meyasa baka sanarmun ba? ko ni ba'a buƙatar gudummuwata ne? ya faɗi yana kallonsa, Murmushi Omar yasaki dama sun saba indai irin haka ne, muddin akace aikin lada yasamu, to har rububi suke yi wurin bada taimakonsu, kowa burinsa ace da dukiyarsa za'ayi amfani wurin bada tallafi sam basa gajiya da irin wannan (Kaji masuyi don Allah) Shiyasa dukiyar tasu kullum hau hawa takeyi kamar kamar me, a ƙalla su kansu basu son adadin gidajen marayun da suka buɗe ba a kasashe daban daban kuma suke ɗaukar ɗawainiyarsu da komai, Manyan asibitoci kuwa da suka buɗe ba iyaka, wanda suma duk kyauta ne ake duba marasa lafiya acikinsu, ga makarantu na marayu da marasa hali da suke dasu ba adadi, wannan ba komai bane ba, kaɗan ne daga cikin abubuwan da suke yi na taimako, Ya Allah ka bamu arziƙi mai albarka wanda zamu amfana dashi kuma ƴan uwanmu musulmai suma su amfana dashi, ba irin arziƙin da mutun zai mallaƙe ba, ka ga ko cikin gidansa fama ake dashi basa ciyuwa balle na waje su samu😧