← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 41

Sashe 6

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

a masifance take magana ƙarshe tayi  Wurgi da takardar ƙasa sannan azafafe da wannan hannun nata ƙirar samudawa ta damƙo mayafin dake lullu6e akan Jahad nan take ya sul6e ƙasa hakan ya bata damar damƙar gashin kanta, wani irin zafi ne ya ziyarci jahad saboda ruƙon da aunty babba tayiwa gashin kanta,
    Janyo gashin tayi ta ɗago jahad dashi, jikinta sai kerma yakeyi duk ta rurruƙe hannun aunty babba dake ruƙe da gashin kanta tana faɗin "Aunty dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba....' bata ƙarasa ba aunty babba takai mata naushi a bakinta, nan take jini ya soma zuba daga bakinta le6enta suka faffashe, saboda tsananin azaba da raɗaɗi yasa jahad fashewa da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali,
   Wurgi da ita aunty babba tayi jahad ta tafi jiki a mace ta zube ƙasa, tattakawa aunty babbba tayi izuwa inda take don bata gama dukan nata ba,
   Tashi zaune jahad tayi tana jan jikinta da baya da baya tana faɗin "dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba.....nasan nayi kuskure....
   "Ke ƙaramar ƴar iska ce ! bakisan koni wacece ba ! Har ni zakiyi wa iya shege acikin gidana ! Ni zaki tonawa asiri Wurin Omar? idan na so yanzu saina sa wuƙa na yanka ki, shashasha...
ta ƙarasa maganar tare da sake damƙo gashin jahad tashiga yi mata azaba dashi, ta ja shi da ƙarfi tamkar zata tsige shi daga kanta, tuni idon jahad yayi jawur wasu irin jijiyoyi suka firfito mata a goshin ta, don rashin imani aunty babba sai ta naɗe gashin a wuyan jahad ta shaƙeta dashi gadan gadan zata kashe ta, murya ashaƙe jahad ke fidda sounds tana faɗin "Ahh...ah..ann...bazan..ƙa..ra..ba' sam aunty babba bata da niyar ƙyale ta sai ma ƙara shaƙeta da take yi
   Kamar daga sama Hosana ta faɗo ɗakin saboda tajiyo ihun jahad da farko sai tayi tsammanin kunnanta ne Suke mata gixau,amma rashin kwanciyar hankali da jin bugawar zuciya yasa hosana gaza samun natsuwa ta fito don tazo taga wani hali jahad ke ciki ta rubuta wasiƙar,
  Shine ta taras da wannan tashin hankali, ihu tasaki a haukace ta watsa da gudu inda aunty babba ta shaƙe jahad ajikin wardrobe,
  "Kada ki kuskura ki ƙaraso in ba haka ba zan haɗa dake kema," aunty babba ce tayi ma hosana wannan maganar batare da ta janye hannunta daga wuyan jahad ba, cikin kuka hosana ke faɗin "ki sake ta...! Ki kyale ta....kada ki kashe mun ƴar uwata.....' amma sam aunty babba taƙiya,
   Ganin jahad ta soma kakarin sheƙawa barzahu yasa hosana fita hayyacin ta,
aikuwa ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe tasamu damtsen hannun aunty babba ta Gartsa mata lafiyayyen Cizo da hakoranta 30 cufffff
   A firgice aunty babba ta saki jahad tana yarfa hannun ta sai ga jini na ɗigowa, cikin hanxari tasa ɗayan hannunta ta zame hannun rigar jikinta don taga inda hosana ta cije ta, wurin yayi jawur ga sahun haƙoran hosana nan rerass a farar fatar hannunta dama gashi dumurmur na ƴan hutu,
   Cike da jin raɗaɗi tace "Innalallahi !ni kika ciza har kika fasa mun fatar jiki na !! Ya salammmm !! Kin mutu wlh !! Kin shiga uku !! tayi maganar idonta jawur saboda taji raɗaɗin cizon hosana wurin har wani Zogin azaba yake yi mata,
   Ja da baya hosana tashiga yi a tsorace ganin aunty babba na tunkaro ta Kamar Damusa, gashi jahad tunda aunty babba ta sake ta, ta sulale ta sume a ƙasa balle itama ta taimaki hosana,
   Hanyar fita ta nufa da gudu zata fice, cikin rashin sa'a aunty babba tasanya ƙafarta ta taɗiyo ƙafar hosana, aikuwa ba ƙaramin buguwa hosana tayi ba, gaba ɗaya ta kife ƙasan tiles ɗin ɗakin, fuskarta ta dake sa, nan take hancinta ya fashe jini ya soma kwaranyowa, haka goshinta ma ya fashe da La66anta duk sun farfashe ihun azaba kawai hosana ke saki tana faɗin "wayyo Allah na ....! Nashiga uku...na mutu na lalace !!
   Aunty babba tace "baki mutu ba, don ubanki, yanzu ne zaki mutun.....tayi maganar tare da kai hannunta kan Gashin hosana wanda ya barbaje ƙasa, kwakkwarar damƙa takai masa, ta ruƙo shi dakyau ta janyo hosana dashi har sai da hosana ta miƙe tsaye tana ihu kamar ranta zai fita, daddagewa aunty babba tayi da iya ƙarfinta na ƙarshe ta buga kan Hosana jikin bangon ɗakin wayyo Allah zoka ga yarda jini ya wanke bangon,
Razanan nan Ihu hosana tasaki na azaba tamkar maƙoshinta zai ballo waje nan take ta sulale ƙasa a mace.......
Chapter 6 · 0% Book details