Sashe 38
Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
bindiga ae ba arziƙi naja motata na koma," Fashewa da dariya aunty babba tayi tace"Ae mijina ne yadawo jiya shiyasa kaga sojoji nan," Baba Alamu yace "Oh to ashe angon ne yadawo, yanzu dae ya za'ayi wurin fitar da yaran kinsan fa wlh shegen tsoran Soja nake, don kwanaki sun ta6a tarar mu a hanya suka sanya mu tsallen kwaɗi a tsakiyar titi da rana tsaka," Aunty babba tace "Ae basu da Imani, musamman in suka ji su acikin kakin nan sai su dunga ɗaukar kansu tamkar wasu dodonni, yanzu abunda za'ayi kana ina ne? Baba alamu yace "yanzu haka na fito da mota ta ina kan hanyar zuwa unguwarku amma fa bazan shigo ciki ba sai dai ki san yarda zakiyi a fito da yaran, Aunty babba tace "Shikenan ka jira ni, zaka ga kirana yanzun nan bada jimawa ba,". bayan ta kammala maganar ta kashe wayar sannan ta fito daga cikin toilet ɗin cikin sanɗa ta lalla6a ta fuce daga ɗakin, Kai tsaye ta nufi ɗakin hafsat ta shiga, tsayawa tayi tana kallonsu hussana da jahad dake ta faman sharar bacci baje saman gadon hafsat, yayin da ita kuma hafsat ɗin ke kwance saman doguwar kujerar ɗakin tana bacci, da alama dukansu daga tashin asuba suka koma bacci, jinjina kanta tayi sannan ta ƙarasa dab da hafsat ta ɗansa hannu ta bubbuga ƙafarta, a dan firgice hafsat tafarka tana cewa "wanene," Murya ƙasa ƙasa aunty babba tace "ke ki taso inason magana dake," Bin ta da kallo hafsat tayi tana yamutsa fuska Alamar bacci bai ishe ta ba, daker tasa hannunta ta janye bargon data lullu6e rabin jikinta da tashi sannan ta miƙe tsaye tabi bayan aunty babba, suka fito daga ƙopar ɗakin suna fuskarta junansu hafsat tace "Meya faru mommy naga kin tashe ni ina tsaka da bacci na? Aunty babba tace "Mutumin fa wanda zai kai su hussana da jahad gidan marayu ya ƙaraso....," jin hakan yasa hafsat canza fuska tuni tace "Mommy yanzu dole sai kin raba ni da yaran nan? Wai me suka tsare maki ne? Dan Allah mommy kibarsu suyi rayuwarsu cikin salama, sun sha wahala fa baki tausayin su? tsoki Aunty babba ta buga tuni ta tamke fuska tace "Tausayin Uban me? menene alaƙata dasu? ke bana son zancen banza mun riga da mun gama magana dake don haka ! Ke nake so ki fidda yaran nan daga cikin gidan nan!! In yaso zan baki numbarsa in kin fitar dasu acikin motarki sai ki kira shi ki bashi su ya tafi dasu can Orphanage home ɗin," Murya asanyaye hafsat tace"shikenan mommy amma ina so ki sani haƙƙinsu ba zai ta6a barin mu ba! Sai Allah ya saka musu duk wani cin zalinsu da mu kayi,!!!!!!!!!!!!!!!! tana faɗin hakan ta juya tare da shigewa cikin ɗakin, wani irin matashin murmushi aunty babba tasa ki tare da cewa "Komai zaki ce ki ce, nidae in dae burina zai cika ba abunda bazan iya aikatawa ba ehen," acan ciki kuwa bayan hafsat ta shiga wuri tasamu gefen gadon ta zauna maimakon ta tashe su sai kawai tafashe da kuka mai cin rai Sautin kukanta ne ya farkar da jahad a firgice ta tashi zaune hankali atashe take cewa "Subhanallahi Aunty hafsat meya faru naga kina kuka? Meya same ki? jahad ta tambaya fuskarta cike da nuna alamun damuwa, Ci gaba da kukan hafsat tayi sam ta gaza cewa komai jikinta har wani jijjiga yake yi, jahad ta kuma cewa "dan Allah sister hafsat ki daina kuka, ban ta6a tunanin zanga wannan ranar ba, idan wani abu ke damunki, zan taya ki addu'a Allah ya yaye maki jin wannan maganar ta jahad yasa hafsat ƙara sautin kukan nata, ɗagowa tayi ta kalli jahad idanunta jawur suna fitar da zafafan hawaye tace"Jahad ba saboda kaina nake wannan kukan ba, face saboda ku ! Ina tausayinku, Nasaba daku zan iya cewa akanku nafara jin tausayin wani ɗan adam aduniyar nan !! tun da jahad taji hakan gabanta ya faɗi Rasssss !! Duk da hafsat bata fito fili ta faɗa mata kai tsaye abunda yasa ta kuka ba, miƙewa hafsat tayi tana faman sharar hawaye tace "Ki tashi hussana ku shirya inaso zan fita daku," Jiki a mace jahad tace "Toh," cikin sauri hafsat ta fuce daga ɗakin, Jahad kuwa jikinta har kerma yakeyi saboda tsoran inda hafsat zata kaisu, daker tasamu hussana ta farka daga bacci sannan ta sanar da ita cewa ta tashi su shirya Sister hafsat zata fita dasu, Batare da sunyi wanka ba, tsaka tsami kawai su kayi acikin toilet sannan suka fito suka shirya, jahad ta zumbula doguwar riga Orange colour ta yafa mayafi launin fari akanta, ita kuma Hussana riga ce Square neck green colour, sai Skirt Ethnic maxi ta sanya ajikinta yana da dan faɗi ya bude da ƴar bazarsa, ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, Mayafi tasamu launin skirt ɗin black colour mai ɗigon fari² ajikinsa, tayi rolling ɗinsa tamkar yadda Jahad tayi, Kallon hussana kawai jahad keyi kallon tausayi don ita ranta yana bata cewa lokacin barinsu gidan ne yayi, yanzu kuma zasu fuskanci wata ƙaddarar !!! lokacin da suka fito daga ɗakin hannunsu ruƙe dana juna, Aunty babba na'a falon sai faman zagaye zagaye take yi, tana ganinsu ta nufo su cikin sauri gudun kada ishaq ya farka daga bacci ya fito yagansu, Tana ƙaraso wa inda suke tace "Ku biyo ni," sannan ta juya ta miƙi hanyar fita daga falon, bin bayanta su jahad su kayi gabansu na faɗuwa, suna fitowa daga falon a harabar gidan tuni hafsat ta fito da motarta, buɗe musu motar aunty babba tayi tana cewa "Maza ku shiga ciki, ku jira hafsat yanzu zata zo, Allah ya kiyaye hanya," ta faɗi tana faman tiƙar dariya sannan ta rufe musu motar, Kusan minti goma sha biyar suna zaune jigum cikin motar gaba ɗayansu babu mai magana duk jikinsu yayi mugun sanyi ganin yarda Aunty babba ke faman yi musu dariya, tun daga haka suka gane cewa ba lafiya," 😳😳😳