← Book details Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 41

Sashe 18

Abban Sojoji Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Around 8 Ta farka kai tsaye kitchen ta wuce har time É—in rigar jiya ce ajikinta da rolling É—inta, a kitchen ta samu Azmee harta kusan kammala breakfast din gaba É—aya, bayan tayi sallama ta shiga suka gaisa da junan su, Daga bisa ni azmee tace "Ina fata jiya kin kai ma SGR dinner É—insa ko? don na shigo na taras da kayan abinci a warmers ko ta6a su ba ayi ba,'
   Sehrish tace "Na babban yaya ne, Jiya bai samu yaci ba dana kai masa, Tea kawai yasha daga baya yace mun yana buƙatar fruits, shine kafin naje na kawo masa har bacci ya ɗauke sa,'
  Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Allah sarki da alama jiya sun sha aiki ne that's why harya gaza cin abinci, Yanzu bari na shirya miki breakfast ɗinsa ki kai masa da sauri saboda nasan dole ya tashi da yunwa,'
   Sehrish ta amsa mata da Toh, ta tsaya tana jiran ta shirya mata kayan breakfast ɗin nasa,
Shiru tayi tana tunano maganar da HAROON ya faÉ—a mata jiya, akwai abunda ya tsaya mata arai take son fitar dashi
"Aunty azmee dan Allah me ake nufi da ZAREN BA KALAR YADIN bane? ta tambaya tana kallom azmee dake shirya abinci cikin warmers asaman kitchen drawers din dake jere,
  Ba tare da ta juyo ta kalle ta ba tace "idan aka ce Zaren ba kalar yadin bane, a tunani na ana nufin kamar abunda bai dace da wani ba, a misali kamar ace kina son wani wanda yafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, bari na baki wani misali ma kamar yanzu ace mace tana Son Namiji wanda ya kasance hamshaƙin mai kuɗi ne ko mai mulki ga ilmi ga kyau gashi prominent dae, ke kuma ace kin kasance ƴar talakawa ce koma kina aiki a ƙasan shi baki da duk wani abu daya mallaka da zaku zo ɗaya dashi kin ga kuwa ba sa'an yin ki bane,wannan shi ake nufi da Zaren ba kalar yadin bane......'
   Jinjina kai sehrish tayi aranta tana cewa "Wato abunda haroon yake nufi kenan hmmm,"
Sannan a fili tace "To Aunty azmee me ake nufi da cewa ISKA NA WAHALAR DA MAI KAYAN KARA,!"?
  Har sai da azmee ta ɗanyi dariya jin wannan, ɗan gyaran murya tayi kafin tace "Kamar mutun ya yi ta wahalar da kansa akan abunda bazai ta6a samu ba, yanzu in mutun ya sanya kayan kara ana iska shin kayan zasu zauna ne batare da sun tarwatse ba?
  Sehrish tace "Eh hakane kuwa,"
  "Yawwa ma'anar kenan, mutun yasanya wa ransa abunda bazai ta6a samu ba, kin ga zai tashan wahala ne,"
  ta ƙarasa maganar tare da cewa "Zo ki ɗauki breakfast ɗin ki kai masa na kammala,"
ƙarasawa sehrish tayi ta ɗauki tray ɗin duk jikinta yayi sanyi ga me da abunda Azmee ta fassara mata yanzu, amma taci alwashin duk runtsi duk wuya zata jaraba Soyayyarta Agare shi ba fashi 💔

    Fuce wa tayi ta miƙi hanya kamar daga sama taji muryar haroon a kunnanta yana cewa "ƴar Shila barka da safiya fatan kin kwana cikin ƙoshin lpy,
   Shiru tayi bata bashi amsa ba, yana tsaye ruƙe da ƙugu daga shi sai gajeran wando ajikinsa,
Ci gaba da magana yayi "Dole kisha ƙamshi baby, an fa samu Freedom dole a hura hanci, hallau dae bari na ƙara tunasar miki, shisshigi da kutsi ba zai kai ki ga cin nasara ba akan wancan Babban kayan da ki ke hari, ke bama shi ba ko junaid dana ga kina shisshige mawa wlh yafi ƙarfin ajin ki, kwara ma ni zan iya yin maneji na lalla6a ki mu rufa wa juna asiri, ke ƴar aiki ni kuma ɗan masu gida Fantsararre,,,
  takaici ya hana ta cewa komai wuce wa kawai tayi upstairs,
   Tun da ta nufi part ɗinsa take jin tashin ƙamshi ya gauraye ko'ina Har cikin hancin ta direct masu daɗin ƙamshi,

   Bayan tayi sallama tashi ga, babu kowa a palor ɗinsa ƙarasawa tayi ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗinsa, tsayawa ta ɗanyi don ta jira fitowarsa,

  Tana cikin tsayuwar nan wayarsa da ya bari asaman hannun Sofa ta soma ringing da ƙarfi har sai da sehrish ta ɗan yi firgit da ido, kai idonta tayi a inda wayar take hada sa hannu tana dafe kirjinta, matsawa tayi a ƙoƙarinta na ta ɗauki wayar takai masa,
  Adai-dai time ɗin yafito cikin sauri Don ya ɗauki wayar saboda Kira ne mai mahimmanci agare Sa yasan dashi
   Jin motsin mutun yasa sehrish ɗagowa takai ido a kansa, aikuwa a tsananin firgice ta ɗanyi wani sauti tare da yin Hanzarin juyawa cikin tsananin farga ba,
   Sam baisan da mutun ba, fitowa yayi daga shi sai ɗan pant a jikinsa gaba ɗaya halittar jikinsa ta bayyana,
   bin bayan ta yayi da kallo mamakin sa ganin yarda ta razana kamar taga wani dodo, wuce wa yayi yasa hannu ya ɗauki wayarsa sannan ya shige ciki yana amsa kiran a kunnansa,
  Juyo wa sehrish Tayi jin alamar ya koma ciki sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, gaba ɗaya duk ta firgice ta gigice ta tsorata da yanayin da tagansa,*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*

_🔥The Father Of Soldiers🔥_

Story & Written
By
*BOSS BATURE*

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·*Episode 13-14*•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________
Chapter 18 · 0% Book details