← Book details Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 28

Sashe 23

Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A *ZUCIYAR* shi yace my Ammi daga gidan su *my JEEDAH* nake Babanta yarasu Baba mutumin Kirki inason mutumin nan bantaba ganin me halin kwarai irin shiba, saidai bansan taya zanfada miki cewa daga gidan su *my JEEDAH* nafito ba tunda kince KO" sunanta kar nasake kira, my Ammi Ina SON *JEEDAH* ke kuma kince kar nasake kiran sunan ta shin my Ammi yazanyida zallar *KAUNARTA A ZUCIYATA* yazanyi! yazanyi!! yazanyi my Amm?..

wani irin tausayin kanshi ne yarufe shi kawai sai yafashe dakuka tareda fadawa jikinta,dasauri ta rungume shi tareda cewa subhanallahi wai yau meya faru dakaine haka? dakyar ta iya kamashi suka zauna sai kuka yakeyi, mekunshe da Abu biyu nafarko dai kukan rashin baba Na biyu kuma besan yazaiyi Ammi ta amince da maganar *JEEDAH* ba, sai lallashin shi takeyi tareda yafamasa Kai saida yayi kuka sosai sannan yayi shuru.

tace ya'isa haka fada mani meyasa meka sannan inakaje tunda dazu kasan yadda hankalina yatashi narashin sanin halin daka keciki kuwa?..tunda nakira wayarka baka daukaba, daga bayama danakira sai ace akashe har zamkira *SAGEER* tambaye shi don ina tunani kotare kuke da saigashi yazo nemanka, tsoro yakamani sosai da yace yakiraka liyinka besameka ba kuma yace shi besan inda kajeba, shin daga Ina kake haka gashi saifaman kuka kakeyi duk kadaga mani hankali gashi duk kayi wani zuru-zuru gajikinka ma dazafi "alamar zazzabi yana damunka KO?..

Cikin sayin murya yace' daga gidansu abokina nake (yadai fadi haka ne kawai) BABASU yarasu kuma mutumin yanada kirki,bakiga yadda suke kuka ba duk saisuka bani tausayi har Ina tunani idan narasaku keda abba yazanyi?.. pls my Ammi kar kutafi kumarni yakara shi fadi kamar za yasaki wani kukan.

Jitayi jikinta yayi sanyi har taji hankalin ta yatashi saidai kuma tadanne "abunda taji gudun karta sake tayar masa da hankali, Murmushi tayi tace baban Jordan kenan dadina dakai wani lokacin wauta kamar first born sheshi tafadi tana dan' dungure masa kai cikin wasa,

"Ai hanyar kenan guda Wanda dukkan mairai sai yadandani DACINTA kuma dazaran kwanan mutun yakare tofa sai yatafi, wanda ba'abunda yake bukata ga abunda yabari tareda al'ummar annabi bayaga Addu'a,

Don haka koyanzu kaga mun mutu kwanan mune yakare kuma babu wani abunda zakayi bayan HAKURI, saikuma kabimu da Addu'a domin kuwa itakadai ce Soyayyar dazaka nuna mana, Saboda haka yanzu abunda zakaringa yiwa baban abokinka kenan Addu'a domin naga mutuwarshi yatabaka sosai, sannan shima abokin naka kafada masa yarigayi baban sa Addu'a sosai kajiko?..cikin sanyi murya yace' toh" my Ammi, tace yauwa toh" yanzu kaci abinci?..

Tab aran shi harya manta abunda ake kira abinci, yace a ah banci ba tace tace toh" kajiko kanata faman zama dayinwa ga zazzabi yanzu katashi kaje kai wanka, barinaje nahado maka Coffee kasha sannan kaci abinci kasha magani kajiki?..yace toh"tareda tashi yanufi part dinshi ita kuma tanufi kicin tana kiran kulu, me aiki kasan cewar *ZUBEE* batanan tajegidansu can zatayi week shi kuma Abba yayi tafiya don haka gidan daga ita saimasu aiki.

Bayan yayi wanka saiyasha coffee tareda Dan tsakuran abinci kadan Saboda bayajin dadi bakinshi, zaya sha magani kema saiyaji wayar sata nakara koda yaduba saiyaga S A Nasko, haka nan yaji yanasan daga wayar don rabonda su hadu atun rananda 'aka kwantar dababa asibiti, daga can *SAGEER* yace kana Ina?.. Cikin sanyi murya *SEERAJ* yace' Ina gida yace OK gani nan zuwa yace ok sai kazoya kashe wayar tareda watsa magani abaki yakora da ruwa sannan yakoma yazauna jiran *SAGEER.*

Kafayi wuyar gani abokina toh" Ya'akai ne?.. inji cewar *SAGEER,* yayinda *SEERAJ* yace dan dai-dai yace meya faru?..cikin tausayi yace BABAN *JEEDAH* ne yarasu, yace ayya Allah yaji kanshi amma mutuwar nashi neyasa duk kafada haka?..yace hmm bakasan kowaye baba bashiyasa, baki ya tabe tareda cewa toh" kowaye aibaikai Abba ba dazaka wani tada hankalinka abanza,

cikin bacin rai yature' shi da hannun kasan cewa yana kusada shi zaune yace BABAN ne banza?.. "eh lallai balaifin kabane laufinane dana kiraka, So tashi katafi nagode atunanina zaka tayani bakinci abunda yasameni ashe bansaniba wani bakin cikin zakake kunsamani, tashi katafi yafadi da karfi! yace au korata kakeyi?.. yace nakoreka domin baba wani bangare ne narayuwata wandanayi rashinsa barina fadamaka,

baba mutun neda abun duniya beda meshiba mutun ne da idanka batamasa shi kokarin yake yafaranta maka, baba yasani hanyata kwarai zamana dashi nakaruda abubuwa masuyawa kuma masu amfani arayuwa, shine har kake tunani bazan iyashiga wannan haliba harsai idan Abbana ne yarasu?.. sai yafashe dakuka Wanda yasa jikin *SAGEER* yai sanyi.

Yace toh kayi hakuri ba kuka zakayi masaba Addu'a zakayi masa nandai ya lallasheshi, San yake dan jan shida fira wanda rabi firar *SAGEER* yakeyinta,daga ba yadai yaimasa sallama yatafi.

💘💘💘💘
Yau Addu'ar bakwai kuma saiyaune iyalan gidan Alh Siddi suka shiga gidansu *SAJEEDAH* dinsu yi masu gaisuwa, koshi masaida Haj Mama tamasa sannan yabar su suka shiga dukkan suharda yaransu, *SAJEEDAH* ce tace Sadiya su "besty na basuyi Hutu bane?..bakita tabe(kasan cewar itadin ba baya bace gurin rashin kunya) tace anyimusu ammata tafibididi,idanu *SAJEEDAH* tazaro tareda cewa bididi kuma Sadiya?..tace "eh tana can tabi wata "kawarta bauchi wai a can zatayi Hutu, Murmushi tayi tace ayya dayake hutunma bayawa sati uku ne kawai, kwanan nan zakiga ankoma school din tace "Oho itadai ta sani da shegen yawo, Murmushi kawai *SAJEEDAH* daganan sukai musu sallama.

💘💘***💘💘
Akwana atashi bawuya agurin Allah yaugashi satin baba uku darasuwa, wanda yayi dai-daida kwanan *SEERAJ* talatin da uku da dawowa Wanda kuma haryanzu besa ranan komawa Jordan ba, duk da kiran shida sukeyi awaya. a wannan lokacin kuma babu abunda be wa data su *SAJEEDAH* dashiba,

daga fannin abinci harfannin sutura basuda matsalar komai saita rashin baba kuma kullun *SEERAJ,* agidan yake wuyi yana debemusu kewar rashin baba, saidai kuma rashin zamansa agida yafara damun Ammi kasan cewar yanzuko abincin gidan ba yaci sosai.

"A tunanin ta gidansu abokin mashi yake zuwa sai daga baya tafahimci ba can yake zuwa ba,sannan kuma baya zuwa gurin *SAGEER* tunda wani lokaci yanafita shikuma *SAGEER* din zayazo nemansa, don hakane yauta kudiri aniyar saita gane inda yake zuwa.

*SAGEER* takira awaya tace masa tana son yazo yabi baya *"SEERAJ* yaga inda yake zuwa,yace toh" *ZUCIYAR* shi cikeda farinciki yau Ammi zata gane inda *SEERAJ* yakezuwa domin shi tuniya gane cewa gurin wannan yarinyar da batadace dashiba yakezuwa dama baya sanshi da'ita.

yace toh"Ammi idan zaya fita kikirani saina fito na bishi,tace kafito yanzu dan ya kusan fitowa yace OK " gani nan zuwa tace toh " tareda kashe wayar, Sanye yafito cikin rigar T-shet baka da wando blue Abu ga farin mutun sai kayan sukayi masa kyau, yace my Ammi zan fita yacetoh"sai kadawo yana fita takira *SAGEER* tafada masa.

Yanatafe *SAGEER* yanabin shi abaya harsaida yaga shigarsa gidan sannan yajuya, zaune yake adan'ma dai-daicin falon gidan dambun shinkafa sukeci shida Sajeed wanda *SAJEEDAH* ce tayi shi, yajikayan lambu kamshi duk ya cika falon, *SEERAJ* kam sai faman sanyi yake yayinda Sajeed ke tayi masa dariya Inna ma dake zaune agurin murmushi takeyi, itama *SAJEEDAH* dake zaune a can gefe dariyar takeyi hannun rikeda abun yankan kunba tana yankewa, jikinta sanye da riga da siket namateriya yayi mata kyau sosai.

*SEERAJ* bayan ya cika bakinshi da dambun sai yace ummh! Jeed kaidai fada mani gaskiya Inna ce tayiwan dambuko?..dariya Sajeed yayi yace Kai *yah SEERAJ,* my friend nafada maka Aunty *JEEDAH* ce tayi, yace ah gaskiya Aunty *JEEDAH* ta'iya dambu pls Aunty *JEEDAH* kinkoya mani nimana'iya?.. yafadi yana kallonta tareda sakarmata lallausan Murmushi itama tamayar masa.

Sallama akayi aka shigo Inna ya'amsa tareda cewa maraba sannan dazuwa, shikam *SEERAJ* jiyayi gaban shi yafadi harsaida dambun bakinsa Ya kusan zubowa kasa saboda tsabar firgici dajin muryar dabeyi zatoba, cikin karfin hali yajuya Ya kalleta *ZUCIYAR* shice taharba sakamakon kallon da Ammi ta watsa mashi, kai yadukar kasa yayinda yaji kirjin shi yana dukan tara-tara.

Inna tace bissimillah kizauna, fuskar Ammi ba annuri tace "a ah bazama nazoyiba hararata watsa *SEERAJ* cikin bacin rai tace?..

Muje zuwa

A

💘Zuciyata ce💘

Tareda Alkalamin

✍🏽

💘Lufhat ce💘
[10:01AM, 3/29/2018] ‪+234 902 288 0912‬: 💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

💘ZUCIYATA CE💘

_Based on true life Story_
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

3⃣2⃣

WRITTEN BY

💘©AMEENA UMAR FARUQ💘
OR
💘MEENAT💘

________________________

*_®PEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*

✍🏽

"Toh aisai katashi mutafi ko?.. jiki asanyaye yamike cikin karfin hali ya kalli Inna yace Inna wannan itace Ammi na, Murmushi Inna tayi tareda cewa ALLAH sarki nifanaga Kama Sannun Hajiya gashi baki zaunaba?.. cikin daure fuska Ammi tace ainace miki bazama nazoyi bako?..cikin sanyin jiki Inna tace haka ne toh" mungode sosai da kokarinku "agaremu Allah yasakada Alkhairi idanun ta yanakan *SEERAJ* tace Ameen,

*SAJEEDAH* kam kirjintane yake bugawa gawani tsoron Ammi data jiya darsu a *ZUCIYARTA* cikin lokaci guda, cikin sanyin jiki tareda bugawa *ZUCIYA* tazo gaban Ammi ta tsugunna tareda dukarda kai kasa tace Ammi inayini?.. ta kalleta sama dakasa sannan tamaida kai gefe sannan tace Lafiya, tareda maida dubantaga *SEERAJ* Wanda yake tsaye kamar gunki duk da bugawar da kirjinshi yakeyi hakan bai hanashi jin bacin ran abunda Ammi tayi ba.

tace aisaka wuce mutafi ko?... "ahankali yace toh" my Ammi kiyimasu gaisuwa "anyimasu rasuwa, fuska daure tace ayya toh" Allah yaji kan musulmai cikin mutuwar jiki Inna tace Ameen mungode, cikin sanyin murya yace' Inna sai anjima tace toh" *SEERAJO* sai anjima mungode Allah yayi Albarka idanu yazubawa *SAJEEDAH* wacce haryanzu tananan tsugunne, Kai ya girgiza tareda wucewa, Ammi tabi bayan shi yayinda Inna tace sai anjima bata amsa ba.

"Ahankali kuma jiki ba kwari *SAJEEDAH* tamike daga tsugun'nan datake, karaf suka hada idanu da inna
Kai *SAJEEDAH* tadukar kasa tana wasa da hannun kuma har a lokacin kirjinta yana bugawa, Inna kam tausayin yartane yakamata har tana fadi a *ZUCIYARTA* ayya za'a shirya da mahaifiyar *SEERAJO* kuwa?..
Itama *SAJEEDAH* abunda take fadi kenan a *ZUCIYARTA,* "Ahankali takoma ta zauna inda aranta tacigaba da fadi Ammi Inason danki da dukkan *ZUCIYATA* saidai Allah yasa karki zama matsala tsakanin mu ameen.

_*nima nace to ameen SAJEEDAH*._
Chapter 23 · 0% Book details