← Book details Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 28

Sashe 22

Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace saboda kwanan shi yakare sannan kuma Ubangijunmu yafika SONSHI, sabada hakane mayadauke kayansa, yanzu soyayyar data rage tsakanin ka dashi Addu'a.

kai *SEERAJ* yagirgiza tareda cewa haka ALLAH yajikan kababa, dai-dai lokacin dasukaji wani irin Kara ta bakin kofar dakin dasauri suka nufi waje,dai-dai lokacin da *SAJEEDAH* tazube kasa Sumammiya.

(ashe tun lokacin da *SEERAJ* yakira Dr suka biyosu yayinda *SAJEEDAH* ta tsaya bakin kofa, itakuma inna ta tsaya tagurin wundo, so duk "abunda yafaru akan kunnan su.)

Dasauri *SEERAJ* yakasar gurinta Cikin matsananci tashin hankali yadago ta tareda fadi "a ah *my JEEDAH* karkiyi Mani haka, girgiza tayake ya nakiran sunanta da'iya kaci karfinsa pls *my JEEDAH* wake up saidai KO" motsi batayi, hankalin shi yayi matukar tashi dai-dai lokacin da Inna ta'isa gurinsu tana sharan hawaye.

ganin *SAJEEDAH* kwance magashiya yasa tace shikenan itama ta mutu ko *SEERAJO?* dasauri yace "a ah inn bata mutu ba, yace Dr do something mana cikin tashin hankali Dr yace "OK daukota cak *SEERAJ* ya dauke ta tareda bin bayan Dr wani daki suka shiga akan gado ya kwantar da'ita yayida Dr yadukufa gani cewar numfashi ta yadawo saidai abun yaci tura, wani irin zufa Dr yashare natashin hankali yace "Oh go help me Cikin tsoro
*SEERAJ* yace Dr me?..yace nayi iya bakin kokari na amma abun yafikarfin tunanina.

Dasauri yace No Dr don Allah kayi wani abu itadin *ZUCIYATA CE* rasata yana nufin rasa rayuwata, dasauri Dr yafara danna kirjinta Wanda hakan yasa *SEERAJ* kaudakai gefe saboda wani abuda yadarsu *ZUCIYAR* shi,

tsawon lokaci Dr yanafama amma bata farfado ba, saidai kuma juyowan gada *SEERAJ* zayayi sai kawai yaga Dr yana kokarin hada bakin shi dana *SAJEEDAH*

wani mahaukaci tsawa *SEERAJ* yada kamashi wanda yasa shidago dakai dasauri ya kalle shi, yayinda shikuma ya watsa masa wani fitinan nan harara Cikin matsananci bacin rai yace?...

_*Nasan wannan din yayi kadan friend amma'aida babu garaba dadi, ko?.. inji malam ba haushe*._

~to'ammadai~

Muje zuwa

A

💘Zuciyata ce💘

Tareda Alkalamin

✍🏽

💘Lufhat ce💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

💘ZUCIYATA CE💘

_Based on true life Story_
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

3⃣0⃣

WRITTEN BY

💘©AMEENA UMAR FARUQ💘
OR
💘MEENAT💘

________________________

*_®PEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*

✍🏽

"Meye haka kake kokarin aikata wa?. Murmushi Dr yayi saka makon gani wani masifaffen kishi, akwayar idanun *SEERAJ.* yace Sorry Oga *SEERAJ* dama akwai wani taimakon dazan batane shiyasa,
Cikin matsananci mamaki yace taimako for how?.. Dr yace anakama hancin Mutum atoshe yanda iska bazaya shiga ba sai kuma aringa huramasa iskata bakinshi toh" in Allah yasa akadace sai yafarfado,
Cikin bacin rai yace toh" shine zaka hada bakin ka Dana matar dazan aura?..

_*A ah kai su Captain SEERAJ kishi yamotsa*_

Dr yace toh" kayi hakuri yisauri kayi mata da kanka Idan Allah yasa akai sa'a zata farfado yanzu, da sauri *SEERAJ* yaduka yayi kamar yadda Dr yace Cikin sa'a saigashi tafara tari, saida tadan tayi sosai sannan tabude idanu ahankali tafara tunani abunda kunnanta suka yajiyo mata, ciki matsananci firgici tareda bugawar *ZUCIYA* tamike zaune yayinda take baza idanu wanda kallo daya zakai mata kafahimci bata Cikin nutsuwar ta.

sai kuma tayi zumbur tamike tsaye saidai kuma wani irin jiri ne ya kwasheta ta tafi luuuuuu zata fadi, Cikin zafin nama *SEERAJ* yariketa tareda cewa pls *My JEEDAH* ki zauna kinji?..dasauri ta damke hannun shi wanda da'alama batasan tayi hakan ba, cikin matsananci tashin hankali tace *yah SEERAJ* da gaske ne abunda kunne na yaji?...

Kai yake girgiza mata Wanda ban gane nufin shiba "eh KO a ah, tace yauwa nasan ba gaskiya bane baba baza yatafi ya barmu ba KO?..wani irin Zafi yakeji acikin *ZUCIYAR* shi domin kwata kwata bayasan ganin bacin ranta, Cikin karfin hali yace Uhmm! kinga kizauna tukun na kinji?..tace a ah gurin baba zayi, yace "aiyanzu baba yana barci, tace toh" zanjirashi yatashi, dasauri tafara tafiya yayinda suka bibayanta shida Dr tana tafiya tana hada hanya domin jirin be sake taba.

Inna da Sajeed suna tsaye suna kuka basu kulada itaba itadin ma bata kulada suba,
Dakin da baba yake kawai tanufa koda tashiga har anrufeshi da sauri takarasa gurin shi, tana cewa Babana waya rufeka?.. barina bude ka kana barci neko?.. toh" Bari najiraka katashi zama tayi akujera tsura masa idanu. dai-dai lokacin su *SEERAJ* suka shiga shida Dr jiki bakwari, da sauri tace *yah SEERAJ* zomu zauna mujira baba yatashi kaji?..

Daga jin yadda take magana Kai kasan bata ciki hayyacin ta, "Ahankali yakarasa gurinta yatsuramata idanu wani irin SONTA keratsa *ZUCIYAR* shi tareda matsananci tausayin ta, tabbas sunyi rashari rashi me girma rashin da bazasu taba maida kamarshi ba, Cikin sanyi murya yace *my JEEDAH* baba bayanzu zaya tashi ba, dasauri tace *yah SEERAJ* toh" yaushe?.. cemata yayi kawai sai "anjima, tareda mikewa zaifita dasauri tace *yah SEERAJ* katafine bazakajira baba yatashiba?...yace ai zanjira shi inazuwa. yayi waje domin wani irin kuka ne yazo masa.

Dr ne yakarasa gurinta cikin sanyin murya yace' kiyi hakuri kisa cewa wannan barci da baba yakeyi bazaya taba tashiga sai DARUSSALAM, zumbur tamike tanayiwa Dr wani irin kallo dai-dai lokacin da su Inna suka shiga itada *SEERAJ,* dasauri takarasa gurin inna cikin matsananci tashin hankali tace,

Inna kinji Dr wai baba bazaya tashiba sai darussalam?.. cikin karfin hali Inna tace haka ne idanun ta zaro Cikin tsoro tace Inna MUTUWA kenan fa?... tace "eh *SAJEEDAH* babanku Allah yaimasa cikawa tafadi tana mesakin kuka, da sauri takarasa gurinshi tace wayyo baba meyasa zaka tafi kabarmu bakasan bamu da kowa ba, sai Allah saikai bakasan cewa Kaine bango majinginar mu ba?..

Sai girgirashi take tana fadin "a ah babana katashi don Allah kaji Babana?.. Saidai Ina baba kam yatafi wani irin kuka tasa ki mai ban tausayi, dasauri inna tazo tadaga ta, "aikam dasauri ta rungume Inna tana kuka yayinda jikinta sairawa yake, itama Inna kuka take haka shima Sajeed yazo ya rungume su hakan suka hadu saikuka sukeyi babu me bawani hakuri, yayinda Inna take fadin tabbas munyi rashi me girma bani da Uwa bani da Uba mijidana dogara dashi yaushima yatafi yabarni, ALLAH kazama gatana kadumeni nida marayun nan haka nantake tafaman fadi "abundai gwanin ban tausayi.

*SEERAJ* shima yana can gefe yana nashi kukan mecikeda tausayinsu dakuma tausayin kanshin, jiyake kamar yaje ya rungumesu ya lallashesu toh" saidai yasan bazaya iyayin hakan ba domin shima yana bukatar alallashe sa.

Dr ne yaketa lallai shin su" har sukayi shuru, saidai *SAJEEDAH* kam hawaye yaki tsayawa afuskarta, Cikin lokaci kankani suka dauki gawar Baba suka tafi gida don a shirya shi zuwa gidan sana gaskiya.

Duk wani masoyin baba saida mutuwar shita taba mashi *ZUCIYA* musamman mlm barau kuka yake wiwi domin yayi rashin makoci na kwarai, su shikam dai Alh Siddi bamusan inda yadosaba yaji mutuwar makocin nasa ko?.. beji ba "Oho saidai wani daga kai yakeyi,

_*Nikam nace "a aha Alh Siddi indai mutu wace tasan dakinkowa*._

duk abunda "akeyiwa mamaci anyi wa baba shiryashi tsaf cikin likafani yayinda *SAJEEDAH* da *SEERAJ* suketayi masa karatun Qur'an maigirma, sunayi suna kuka saida akai sallar la'asar sanna akakai baba gidan sa na gaskiya.

_*Allah sarki baba mutumin kirki Allah yajikanka da Rahama halin kana Alkhairi yabi ka ameen*_

Hakanan dai akakai Baba gidan sa nagaskiya akadawo aka cigaba da karban gaisuwa,sai bayan sallah isha'i sannan yai shirin tafiya gida Cikin gida yashiga don ya sallamo Inna,
yana tsugunne gaban inna yana sallamar ta amma kuma idanunshi yana kan *SAJEEDAH* datake kwance kan kafar inna hannun ta rikeda chasbi ta naja, saidai kuma tanayin kuka kadan kadan domin haryanzu hawaye yaki tsayawa,

Inna tace toh" *SEERAJO* saida safe mungode kwarai da dawainiya ALLAH yayi maka Albarka, yasaka maka da Alkhairi ka gaida mutanan gida yace toh" ahankali ta tashi daga kwancen datake cikin sheshshekar kuka tace *yah SEERAJ* saida safe yamike tareda cewa zomana *JEEDAH* tace tace toh" saidai kuma bata tashi ba, Inna tace bayace kije ba?.. kai tadaga alamar "eh tace toh tashi kije mana,tace toh"tareda tashi tabin bayan shi, tsaye ta iskeshi jikin motar shi yajingina cikin muryar kuka tace *yah SEERAJ* gani.

idanu ya tsuramata wani irin matsanancin SONTA yakeji acikin *ZUCIYAR* shi ga tausayinta dayake ratsa ilahirin jikinsa jiyake kamar ya rungume ta "akirjinshi ya lallasheta, Cikin sanyi murya yace' *my JEEDAH* kiyi shuru kibar kukan hakanan kinji kinga "ance babu kyau anayi mamaci kuka haka neko?.. tace "eh yace toh" ki daina muyi tayiwa baba Addu'a Allah yakai rahama agareshi kinji?.. tace toh" yace toh"kishiga gida ki kwanta saida safe kinji? tace toh" tareda wucewa yana tsaye yana kallonta har tashige gida sannan yaja jiki yatafi.

"Aban garen Ammi kuwa hankalin ta yatashi tunda 12 :00pm da *SEERAJ* yafita bai dawoba, kasan cewar baitabayin hakaba gashi takira wayar bai dauka ba daga baya ma data kira sai akace akashe take,shiyasa hankali ta yatashi musamman data tuna cewar *SAGEER* yazo nema shi sannan yace shima yakirashi awaya besa meshiba.

Sai faman safa damarwa takeyi a tsakiyar falo, Cikin sanyin jiki yashiga falon bakinsa dauke da Sallama,dasauri tajuyo takalleshi gabanta ne yafadi saka makon ganinshi datayi wujigawujiga, gashi duk yafada idanun shi duk sunzurma fuskarshi tayi fayau sai dogo hanci kawai kake gani, cikin tashin hankali takarasa gurin tareda rikeshi cikin matsananci tsoro tace?...

Muje zuwa

A

💘Zuciyata ce💘

Tareda Alkalamin

✍🏽

💘Lufhat ce💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

💘ZUCIYATA CE💘

_Based on true life Story_
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

3⃣1⃣

WRITTEN BY

💘©AMEENA UMAR FARUQ💘
OR
💘MEENAT💘

_*WANNAN page NAKUNE MASOYA ZUCIYATA CE NA (BAYAN WUYA FANS) INA SONKU INAYIDAKU FIYEDA YADDA KUKEYI DANI, INAJIN DADI YADDA KUKE NUNA KAUNARKU AKAN LITTAFIN NAN, ALLAH YABAR KAUNA AMEEN NAGODE SOSAI,*._

________________________

*_®PEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*

✍🏽

"Subhanallahi lafiya meyasa meka daga ina kake haka?.. sai tambayar shi take tareda tattaba jikinshi,ahankali yadago kai yazuba mata lumsassun idanun shi ba tareda yace komai ba,
cikin tashin hankali tace nace meyasa meka daga inaka ke kayi shuru?..
Chapter 22 · 0% Book details