← Book details Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 28

Sashe 18

Zuciyatace Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dasauri *SEERAJ* yace yauwa nagode pls kazo yanzu kabudeni,Amma kar ka biyo ta babban falo,ka biyo ta kofar baya pls kayi sauri kaji?.. *SAGEER* yace "Ok gani nan zuwa,Cikin abunda baifi minti talatin ba ya'iso ya kuma yi kamar yadda *SEERAJ* din yace.

Koda yashiga sai bai ganshiba don haka sai yanufi falo, wani irin matsanancin tsoro da Mamaki ne yakama *SAGEER* saka makon gani *SAJEEDAH* da sauri yace?...

Muje zuwa

A

💘Zuciyata ce💘

Tareda Alkalamin

💘Lufhat ce💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

💘ZUCIYATA CE💘

_Based on true life Story_
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘🛫💘
💘🛫💘
💘

(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)

2⃣4⃣

WRITTEN BY

💘©AMEENA UMAR FARUQ💘
OR
💘MEENAT💘

________________________

*_®PEN:WRITERS ASSOCIATION_*

*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
________________________

*_only the exquisite and Whizkid writers are opportune to be pen writers_*

✍🏽

"Kul! kasake marinta lafiya me tayi maka haka?.. Cikin takaici hanashi sake marin ta da Ammi tayi yasauke hannun shi, Sannan ya watsamata harara tareda mika mata hannu yace bani key dakina.

Dagudu tanufi gurin Ammi tana kuka yayinda ta rungume tana cewa, yi shuru muje naji dalilin dayasa ya mareki" suka nufo gurinshi, shikam *SEERAJ* tuni yabaje "akan kushin yajingina bayan shi tareda daukan hannu wanshi duk biyu, yamayar baya ma'ana yayi filodasu idanun shi rufe yadauki kafa daya yadora akan dayaz yayinda yake kada fafafun "ahankali babu abunda yada meshi tamkar bashi yayi Marin ba.

Zama Ammi tayi kusada shi tareda zaunar da *ZUBEE* kusada ita, kallo daya Ammi tayi masa tafahimci RANSHI "abace yake, domin tunbai Kai haka ba take gane idan RANSHI yabaci,

Sai yarufe idanu yayi shuru duk lokacin data ganshi haka takanji badadi don haka, KO" yanzuma data ganshi haka sai taji ba dadi .

"Ahankali tace Ina daga kichin naji saukar Mari har biyu yanzu Kuma nafito, zaka Kara mata wani marin me tayi maka haka?...Cikin bacin rai yabude idanu tareda cewa my Ammi nafasa "auran *ZUBEE*.

Ba Ammi ba hatta da *ZUBEE* saida gabanta yafadi yayinda taji tsoro ya kamata, har batasan lokacin datadago Kai ta kalleshi ba yayinda shikuma ya watsa mata harara, Da saurin Ammi tace Kai! kasan "abunda kafada kuwa?... batare da ya kalleta ba yace "eh my Ammi nafasa aurenta domin itadin batada ce da rayuwata ba.

Cikin bacin rai tace "eh haka ne toh" saidai kuma idan kamanta da abunda kafada "anan gurin toh" niban manta ba domin kuwa cewa kayi tsakanin mu babu "alfarma saidai umarni KO?...batajira yabata "amsaba tacigaba dacewa, sai nikuma nabaka Umarni yayinda Kai Kuma ka tabbatar manida cewa zaka cikamani shi ko?..

Cikin sanyi murya yace "eh domin yaga "alamar ranta yafara baci, tace toh" yanzu Kuma sai "akaga bankai matsayin daza'acika Mani Umarnin bako?.. da sauri yace my Ammi nifa ba nufina kenan bada?.. tace toh" meye nufin ka nacewa kafasa auren *ZUBEE?..*

yace shin "amatsayin ta Na wacece zata zama mata agareni shin ba itace mace ta farko dazata fara kare Mani mutunci naba?...Ammi tace tabbas itace, yace toh" yaza'ayi Kuma "ace itace mace ta farkoda zata fara zubar manida mutunci a idon mutane saboda me toh?..Ammi tace kamar yayafa?

Cikin bacin rai yace my Ammi "Wata yarinya ce tazo gurina nataimaka naje nakai babanta "asibiti bayada lafiya, to" wai Kuma bayan ta nuna mata inda nake kawai saita rufemu 'adaki don iskanci Kuma shine tawuce da key din
toh" akan wani dalili zatayi Mani haka, mene ne nufinta Na rufemu "adaki "eh? jifa yadda tasa naji ciwo gurin bude kofar yanuna mata hannushi rai bace.

Da sauri Ammi takama hannushi tareda cewa subhanallahi "aini ba kulaba, ah lallai *ZUBEE* baki kyauta ba Sam wannan aiba dabi'ar kwarai bace, gashikinsa dan'uwanki yaji ciwo sannan kuma baki gudun mutumin yasamu matsala saboda rashin kai shi asibiti dawuri?..tace Ammi toh" ai yar...harara *SEERAJ* ya watsa mata me kunshe DA gargadin cewa muddun kika kuskura kikace' *JEEDAH ce* saina karyaki harda yimata misalin da hannu.

"Aikam dasauri tayi shuru yayinda Ammi tacigaba dacewa karki sake irin haka kinji ko?.. kai tadaga alamar toh" tace toh" bashi hakuri tace Sorry yah S P batareda ya "amsa ba yace dallah bani key na nidai, Ammi tace Ina key din?.. tace yana daki toh jeki dauko masa abun shi tace toh tareda mikewa tanufi daki.

tace sannu yace yauwa my Ammi sannan tace kai kuma Baban Jordan "aiba haka "akeyi ba, idan tayi maka laifi fada mun zakayi saina yimata fada bawai kace kafasa aurenta ba shin bakasa auren ku yanada yadaga cikin barina ba ummh?..aranshi yace my Ammi Zan cika maki burinki ba dan *ZUCIYATA* nasabo saidon farin cikin ki'.

"Afili kuma sai yayi murmushi yace ki kwantar da hankalin ki my Ammi burin ki zaya cika insha'Allahu, dama dai raina ne yabaci Da abunda tayi mani shiyasa nafadi haka. karki damu my Ammi badai aurena da *ZUBEE* shine farin cikin ki Da cikar burinkiba?..tace "eh Babana yace toh" ki kwantar Da hankalin ki za'ayishi Da izinin Allah.

tace Allah yasa Babana yace ameen tace toh" ya Baban yarinyar ka kaishi asibitin?.. yace "eh nakai shi harma anyi duk abunda yakamata sun ma bashi gado, tace Allah sarki toh" Allah yabashi lafiya yace Ameen. Sannan tace Don Allah kuma "a cigaba da taimakon mabukata yace insha'Allahu my Ammi,

"Anacikin haka saiga Abba yafito(kasan cewar yana gari) dasauri *SEERAJ* yasauka kasa tareda gaida Abba ya'amsa, dai-dai lokacin da yazauna kusada Ammi, murmushi tayi tareda cewa kafito?..yace hayaniyar kuce tafito dani meke faru wane?.. nan Ammi tafada masa "abunda yafaru, Abba yace "ah *ZUBEE* bata kyata ba.

saigata tadawo hannun ta dauke da key, gaida Abba tayi sannan tamika mashi key yakarba tareda hararar ta, Murmushi Abba yayi tareda yiwa *ZUBEE* fada, yamike yana cewa Abba my Ammi zanje nayi wanka, sukace toh" sai kafito yanufi sha shinsa, yayida ita kuma tamike tace Alh barina duba masu shirya breakfast yace toh" miko mani jarida can tabashi, sannan suka nufi kichin tana sakeyiwa *ZUBEE* fada kam abunda tayi baidace ba karta sake yin haka.

_*Yan'uwana biyayya ga iyaye abune mai mahimmanci "arayuwar mu, muyi musu biyayya koda ZUCIYAR MU bataso hakan zaya sa ZUCIYAR SU tayi FARI,har suji DADI susa mana ALBARKA wanda ALBARKAR takine shi "arayuwarmu ALLAH kabamu ikonyiwa iyayanmu biyayya Ameen.*_

Bayan yafito wanka saita shirya cikin wani yadi sky blue me Kyan gaske, wanda kallo daya zakai mashi kagane tsadadde ne yafesa turaruka masu sanyin kamshi Sannan yadauki key mota tareda wayoyinsa sannan yafito.

Direct kinchi yanufa gurin Ammi tana ganin shi tace' har kafito?... yace "eh my Ammi Zan fita, tace "ah bazaka tsana kayi breakfast ba?...gashi "an kusa gamawa yauma dai su kulu sun makara guri shirya breakfast din, yace "aiba dadewa zanyi ba zandawo tace toh" sai kadawo yace toh"tareda fita.

💘💘💘💘💘💘
Da Sallama yashiga gidan *SAJEEDAH* ta amsa tareda mikewa daga zaunen datake kasan cewar tashin shi takeji ta, sanyetakedadayadagacikin abayar dayasaimata tun wancan lokacin, saidai wannan jace sabani waccan baka dama mayafin babban don haka shiga yafa, kallon tayake fuskarta fayau ba kwalliya Amma dai saiyaga tayi mashi kyau.

Murmushi tayi tareda dukar dakai kasa wani irin kunya taji yakamata saka makon kallon dayake yimata, Cikin sanyi murya tace sannu da dawowa *yah SEERAJ* yace yauwa *my JEEDAH* kinyi kyau sosai barina yi maki hoto, dasauri tarufe fuska tana dariya tace kai *yah SEERAJ* ahaka?..

yace yesss let me snaps u my dear pls remove u hands, dariya tayi har beauty point dinta yalotsa "ahankali tacire hannun saidai baduka ba hakan sai yabada style, dasauri ya dauketa tareda cewa *my JEEDAH* "aikam tayi kyau sosai nan da nanya'ajiye hoton "agaban wayar, sannan yace kin shirya kenan mutafi?.. tace "eh OK muje tace toh"
tareda dukawa zata dauki buhun baggo datasa kayan da zasu bukata, sai yayi saurin dauka dasauri tace Lah *yah SEERAJ* kaida hannun ka yake ciwo kawo na dauka, yace lah *my JEEDAH* barina dauka dawannan hannun yafadi yana kwaikwayon maganar ta me sanyi.

Dariya tayi tareda rufe fuska tace kai *yah SEERAJ* shima dariyar yayi tareda fara tafiya yac' Oya muje tace toh" tareda bin bayan shi, yace *my JEEDAH* naga book da school uniform dasu Zaki asibiti?.. tace "eh gobe zamu fara exam, shine zanyi karatu kuma ni gaskiya tsoro nakeji bazan iyakwana gida nikadai ba dariya yi dai-dai lokacin da yabude mata mota. "ahankali yake yin tuki da hannu daya kasan cewar daya hannun daya yanke yanayi masa ciwo sosai KO" kwana zayayi saiyayi dabara.

Shuru tsakanin su bawanda yacekomai can sai yace' *my JEEDAH* wai tun yaushe ne baba bayada lafiya?.. tace hmm yanzu fa yakai wata uku, yace Kai! *my JEEDAH* har _three month_ baba bayada lafiya amma ban saniba, gaskiya nidai baki kyauta mani ba. Cikin sanyi murya tace kayi hakuri *yah SEERAJ* kasan duk abunda Allah ya shirya zaya faru toh" faba babu maka wa sai yafaru.

Yace hakane toh"Allah yabawa baba lafiya tace ameen dai-dai lokacin dayake shiga ciki asibitin,yauwa *yah SEERAJ* me "doctor yace yanada mun "baba? yana kokarin yi parking yace mata befadaba tukun saisunyi test din jininsa da fitsari, Ahankali tace toh' ni "abun tsoro yake bani,

yace tsoro kuma? ke daza kiringa yin Addu'a toh" amma meyasa kike jin tsoro?... tace saboda gani nakeyi kamar ciwon koda kedamun shi Kuma kaga shi idan tayi tsananisa kaji "ance sai anyima Mutum dashen, shiyasa nakejintsoro shikam *SEERAJ* gaban shine yafadi yayinda yasaki baki yanakallon *SAJEEDAH* Cikin mamaki.

Dasauri yace ke waya fada maki?..tace a school "a fada mana alamonin masu ciwon koda Kuma kaga duk alamomin ciwon Baba, irin na masu ciwon koda ne kaga yawan fitsari Kuma Da jini sannan yawan barci, sunada yawafa alamomin Kuma duk ciwon baba yanuna su shiyasa nakeji tsoro *yah SEERAJ*.

Dasauri yace kidai najin tsoro Addu'azaki ringayi kinjiko?.tace inayi,yace toh" muci gabada yi masa insha allahu zayaji sauki tace toh" Sannan su kafito daga motar, suka nufi dakin da'aka kwantarda baba.
Chapter 18 · 0% Book details