← Book details Zarrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 33

Sashe 8

Zarrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai hawaye kibin kuncinta tana qara saita injin idonta akan Aseem kallo takeyi masa da yake bayyana tsantsar tsana dajin haushi da kuma tausayin kai tasan duk duniya ba kowane yaja mata wannan wulaqancin ba face Mal, numfashi ta sauke kawai ganin wankin hula na neman kaita dare ta juya ta canza hanya ta tafi tabarsa tsaye yana bin bayanta da kallo yana murmushin mugunta shikadai tasan abinda yake saqawa a zuciyarsa yarinyar ta gama lalacewa idan ta zama mallakinsa zai nuna mata iyakarta zai nuna mata duniya da bambamci.
Komawa yayi yatada motarsa ya tafi sai lkcn Jiddarh ta lura da cewa ashe Asmah ta jima dayi mata nisa tabita da sauri tana qwala mata kira bata tsaya ta saurareta ba sai a cikin makaranta suka hadu bayan an gama assembly suka tafi ajinsu Jiddarh ta dubi asmah tace “wato Allah idan yana sonka da arziqi sai ka zagi sarki a gaban fadawa yace gaisheshi kayi wlh Asmah a rayuwata na dade banga kyakkyawan namiji irin Aseem Ba kayy gsky kin dace, amma fah da alamun dan izzar masifa ne zakisha fama...."

Wani naushi da Asmah ta kaiwa Jiddarh a baki yasata gocewa tare da cewa “daga fadar gsky kuma Allah mijinki dan kyakkyawa dashi" malaminsu ne ya shigo hakan ya tilastawa Jiddah yin shiru ita dama Asmah bakinta ya kulle kalaman Aseem ne kawai sukeyi mata yawo a kwanya iyayenta matsiyata idan ta tuna wannan kalmar sai taji hawaye ya zubo mata to amma komai ya samu shamuwa watan bakwai yaja mata da mahaifinta baibi son zuciya ba da yanzu tana tare da masoyinta, da taji haka a ranta saita tuna yace da quarter million ya siye Sadiqunta.
Gabadaya duniya tayi mata zafi ji takeyi kamar tayita rusa kuka hakadai a dafe aka tashi suka tafi gda daqyar takai gidan saboda azabar masifar zazzabi da yake dirar mata tana zuwa ko uniform bata cire ba ta fara kwara amai bayan ta gama ta shige dakin innah ta kwanta tana mayar da numfashi

A kwance take amma duniyar juya mata takeyi itadai bata qara sanin komai da yake faruwa ba sai farkawa tayi ta ganta daure da robar ruwa a hannunta ta rinqa bin dakin da kallo daya da daya tanason tunano ko a ina take a hakan taji an turo qofar an shigo ta juyo da kanta idanunsa na kanta yana wani lumshesu kamar me jin bacci.
Guri ya samu ya zauna ya bude takardar hannunsa yayi rubuce rubucensa ya rufe ya sake dagowa yanzun kanta yana saman silling fasali yaja ya miqe daidai lkcn da Inna Azeezah qanwar Innah take shigowa suka gaisa har yana wani rusunawa tace “ya me jikin?" Kallon Asmah yayi yace “gatanan da sauqi yanzu ta farka da alamun jikin dakyau insha Allahu gobe ma zamu koma gida yasu Innah?"

“Alhmdllh" ta furta koma ta zauna tana hade kaya shikuma ya fice bai jima ba ya dawo da tarkacen ciye ciye ya ajiye Innah Azeeza nata godiya yayi murmushi yace “babu komai Innah yiwa kaine fatanmu dai ta samu lfy ai taji jiki sati biyu a kwance ga hidimar biki sai matsowa takeyi yanzu fah saura sati biyar" jinjina kai tayi tace “Allah yasadai ayi lfy a gama lfy"

Amsawa yayi da amin sannan yasa kai ya fice zuciyarsa najin haske yanajin nishadi yasan yagama saita saarsa Asmah zata gane kurenta tabbas zatasan ta shigo gonarsa da wannan tunanin ya tashi mota ya nufi gdansa yajima a mota kafin yayi qarfin halin fitowa yana ayyana ta yanda zai tunkari Mime da mgnr auren nasa bayan shi da kansa yayi mata alqawarin bazai taba hada matsayinta da wata ba balle aje ga batun aure.
Shahada yayi daya haura ya tunkari saman a kwance a parlourn saman ya isheta tana duba jarida ya nemi guri ya zauna ta ajiye jaridar tare da dagowa ta dubeshi sukayiwa juna murmushi ya shafa kansa yace “ya gda?" Miqewa tayi zaune tana yatsina tace “gashinan babu dadi kadaici ya dameni kaikuma ka daina samun lkc na na rasa meye yake daukenka hankali gareni" kawar dakai yayi ya shafa sumarsa yace “abubuwa ne sukayimin yawa 2 days dinnan inason samun zama dakema nakasa samun lkc” shiru tadan ratsa na dogon lkc can ya dago yace “Maryam Aure zanyi....." Wata zabura tayi ta miqe da sauri tace “me....me kace Aseem".......

[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*

*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*

Littafin _*_ZARRAH* na kudine idan kinason zaki biya 200 ta _account dina_
__0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTBank_ _ko kati MTN ta whattsAp a wannan number 09013718241 ko VTU ta wannan number 09031307566._

_Gareku yan'uwanmu na Niger kuma fah kuna da damar samun wannan littafan guda biyu idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_

*_17-18_*

Miqewa yayi yana shirin shiga daki ta riqoshi ta baya tace “wai da gaske kunne na yakeyi kaine kake fadawa Mimee zakayi aure Aseem da gaske hakane? Please tabbatar min domin nasan tudun dafawa" kama hannunta yayi ya zaunar da ita yana binta da kallo yace “ba kamar yanda kowanne aure yakw nawa yake ba Mimee idan kika tashi hankalinki ke kikaga dama da kanki zan Aure ne domin ramuwa da daukar fansa, idan baki manta ba nataba baki lbrn wata yarinya data mareni ta fasamin yatsa kwanakin baya, to itane zan aura, a zahirinta ba ajina bace kuma ba tsarata bace ni kaina inajin kunyar hadaka ta da ita ina qyaqqyaminta wlh don an daina cinikin bayi ne da siyo miki ita zanyi matsayin baiwa ki rinqa morarta

Dakatar dashi tayi da sauri tace “shut up Aseem banason yaudara da zalimci ni zaka wulaqanta ashe dsma abinda ake fadamin gsky ne Wayyoh Aseem meye nayi maka da zakayimin wannan sakayyar...." Rufenta baki yayi yana girgiza mata kai yace “kada ki kawo komai a ranki ba haka nake nufi ba har abada kece zabina kece burina kuma kece zuciyata wlh da gaske yarinyar nan don ke na aurota nasan zata taimaka miki

Sake dagansa hannu tayi ta miqe da gudu ta nufi dakinta ya bita da sauri daqyar ya samu ya shawo kanta bayan yayi mata manyan alqawura masu wuyar cikawa yana qara rantse mata baso bane zaisa ya auri Asmah kawai gayya ce to ganin yanda ya zage yana rarrashinta yasata sakin jiki amma duk da haka kishin mijinta yana cinta a ranta duk da tayi ammannar bai isa ya wulaqantata ba kodon soyayyar da mahaifiyarsa takeyi mata dole yabi umarnin uwarsa saboda haka ta yanke shawarar binsa ta qasa zata hadashi da hajiyansa tasanta sarai bata hada hanya da takala balle kuma ta bari a kawo mata yar matsiyatan qarshen zamani matsayin suruka da wannan tunanin suka fita ko a hanya aikin rarrashin mimee yakeyi suna shiga harabar gidan yaji gabansa yana faduwa so yayi ya juya amma INA ya makara yana daga Kansa ya hango hajiyansa saman bene ta zubawa motarsa ido dole tasashi fita yabi bayan Mimee data shige gdan a qofar falon sukayi karo da Hajja ta daukeshi da mari ya dafe gurin da tafukan hannunsa yanajin zugin marin saman jar fatarsa yana dagowa ta sake daukeshi da mari tana kumfar bakin cewa yanzu Aseem har kayi qwarin da zaka nemi aure batare da ka sanar dani ba saidai naji a wajen qannenka....."
Hawaye Mimee ta goge tace “ai dole bazai fada miki ba Hajja wai ya rasa dawa zai hadani kishi saida yar talakawa...." Dafe qirji Hajja tayi tace “na shiga uku ni Saratu yar talakawa Aseem ina ka samota me suka Baka suka sauya maka tunani ni zaka wulaqanta yanzu yaushe ma akayi aurenka da Maryam da har zaka tattagowa kanka aure kuma auren ma memakon kaci gaba sai kawai kaci baya to wallahi baka isaba dole ka hqr da wannan dan iskan auren naka ka zauna da matarka dana zaba maka"

Shidai tunda yayi qasa da Kansa bai dagoba sai yanzun yace “wlh Hajja ba haka bane kawai...." Buge masa baki tayi tace kawai Ubanka ka kiyayeni Aseem zanci ubanka wlh dama na lura shine yake daure maka gindi shi ko ubanme ya hanashi auren mace sama da dayan sai kai da quruciyarka zaka dorawa kanka wahala to indai na isa dole ka janye ban amince ba bakuma zan amince ba"
Juyawa tayi ta shige parlournta ta barshi tsaye itama Mimee tabi bayanta a sanyaye ya juya ya fice daga gdan yanajin zafin abinda Hajja tayi masa yanzu meye laifinsa don anyi masa ba daidai ba yayi shirin daukar fansa zaayi masa wata fassara ta dabam bandama abinsu shi meye zaici da wannan banzar yarinyar da bata isheshi kallo ba"

Da wannan tunanin ya nufi gdan Jabir yake fada masa abinda ke faruwa sosai shima Jabir ya jinjina abin ya dubesa yace “to kai tunda abin baiyi nisa ba ka hqr mana kasan dai halin Hajja shi kansa Dad hqr yakeyi da ita" girgiza kai yayi yayi murmushi yace “nifa babu abinda zaisa na janye akan qudurina saidai kowa yayi hqr kamar yanda nake haqurqurtar da zuciyata ta karbi auren idan na janye dama haka Asma'uh da nahaifiyarta sukeso farin ciki zasuyi nikuma ba burina suyi farin cikin ba saboda haka kawai aci gaba da tafiya a haka tunda Dad ya karba mgnr kowa ma kada ya karba" da wannan tunanin ya miqe ya nufi gdan Yayarsa Aseemah itace kadai me sauqin yanayi a wajenta yake tunanin samun mafita game da auren nasa yana zuwa ta tareshi da fara'a tana tsokanarsa nan yake zube mata abinda yake ransa sosai tayi murna ta tayashi fatan alkhairi yayi shiru kamar bazaice komai ba sannan ya dago yace.
“Banasonta Sister na rasa meye yasa na dage wajen Neman auren ta yar talakawa ce Allah ina qyaqqyamin kaina inajin kunyar nunata matsayin mata talauci yayi musu kanta nifa badon quduruna a kanta ba da tuni na hqr ko na samu nutsuwa"
Chapter 8 · 0% Book details