← Book details Zarrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 33

Sashe 2

Zarrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shi gani yake dole shi wata tsiyane qwafa tayi yakai Mata naushi ta goce yace “wlh Inna badan keba da tuni na dade da barar da yarinyar nan batada aiki sai jan maganar masifa shegiya kullum baqi take qarawa Wai kwananki nawa ma bakiyi wanka ba ne?" Turo baki tayi tana qunquni ya miqe yayi kanta Inna tayi saurin riqeshi tace “Kaga Mudansir ka kiyayi tabamin auta qaniyarka zanci uwarme tayi maka da zaka wani zage kwanji kace zaka bugeta bakaganin ba qwari gareta ba" qwafa yayi yace “yawwa Inna wlh na qara ganinta da Sadiqu sai na kakkaryata nan Naziru abokina yazo yanasonta tayi masa rashin albarka har tana cewa nima din dana turoshi menene bare shi.
Murmushi tayi tace “to Banda abinka Mudan inakai ina shiga tsakanin Ma'u da Sadiqu Kuma ma meye laifin Sadiqu yarannan sunason junansu tun suna qananu bakace su rabu ba sai yanzu da aski yazo gaban goshi to ban yarda karna qaraji matuqar Ina raye saina dauki Ma'u nakaiwa Sadiqu dakinsa matsayin Mata insha Allahu na lura dagakai har babanku ba son zaman lfy kukeyi ba shikenan kowanne rashin albarkarku ya tashi akan Asma'u na zai qare yar tawa tilo bata damu kowa ba Amma kowa ya dameta"

Jinjina Kai yayi ya fice yana cewa “ai dama Mal yace kece kike daure Mata gindi a gdannan to Allah yasa na qara ganinta da Sadiqun a unguwarnan Kai nama daina zuwa ko Ina a qofar gidannan zan rinqa zama naga qarshen rashin kunyarki shegiya me idon aljanu" matsawa tayi ta kwanta jikin Inna tace “nifa Inna bansan me Sadiquna ya tarewa su Mal da Yaya ba dazuma da Mal yaganmu inaji Sadiqu yana gaisheshi yaqi amsawa nikuwa nace da Sadiqu dama ya daina wahalar da kansa aure ne dai dole a dauramin da wanda nakeso kamar yanda aka daurawa kowacce ya a gidannan ehe...."
Buge Mata haba Inna tayi tace “kinci malafar ubanki don qaniyarki bakisan cewa Allah uba yabawa damar zabawa yarsa budurwa miji ba to shine har kike wata taqama kul na kumaji yar jaka da qusa kawai tashi ki debi kayan makarantarki ki goge jiya Jiddah ma tazo bakyanan kinje debo ruwa tace ki taho muku ta tast book dinnan na biology zakuyi tast ranar laraba miqewa tayi ta fita ta aro dutsen guga ta dawo tana gugar suna Hira da Innanta rabin hirar akan Aseem Shaheed ne da irin alwashin da taci na yimasa rashin mutunci duk ranar da Allah ya sake hadasu, Jinjina Kai Inna tayi tace “amma da kin hqr da yafi Miki kinga shi namiji ne ke kuwa mace ce ko marinki ya sakeyi ya cuceki a sadakinki sai an rage wani abu balle ma ni banga laifin da yayi miki ba badan dai sakarcinki ba mutum nawa kika nemi taimakonsu sukaqi taimaka Miki baki qullacesu ba saishi wasu ma mutuncinki suka rinqa farauta Amma duk kin manta saishi da yayi fada dake da fatar baki Kuma tabakin nasa ai ba kunyar gareki ba qila abinda kikayi Masa ma yafi Wanda kika fadamin"

Shiru tayi don tasan idan ta cika magana yanzu Inna zata gindaya Mata sharadi ita Kuma tariga ta qudurta a ranta saidai idan Allah bai sake hadasu da Dr Aseem Shaheed ba Amma saitayi Masa abinda zai tsaya Masa arai kamar yanda yayi mata ita ba lusarar ƴa bace dazai zageta yaci mutuncin Innanta kuma ta ƙyaleshi dama iya ita kaɗai yayiwa da da sauƙi kamar yanda na bayan sukayi amma shi Innanta fa yacewa tsumma tab ai wlh ya taro march kwararo kwararo zatake bi don ta ganshi tashin farko rotse zatayiwa motarsa idan yayi yunƙurin yin wani abu ta kwankwatse masa yatsan ƙafarsa da dutse.
Dariya takeyi ciki ciki Inna tace “dariyar me kikeyi?" Saurin saita kanta tayi tace “tunawa nayi da wata tsokana da mukayi nida Jiddah a hanyar school ranar mun dawo dukkanmu bamuda kuɗin mota mukaga Mata da miji suna tafiya a qafa matar da tsohon ciki shine Jiddah tacemin lahh Asmah Kinga wata Mata ta haɗiyi wake ya kumbura Mata ciki nikuwa na matsa kusa dasu nace sannu Mata buhun garin kwaki kikaci ne yayi miki saqeqe a ciki shine mijin ya Kama zaginmu muka mayar dashi mahaukaci mukayita dariya kawai saiya biyomu da gudu na turansa dutse ya tungule ya faɗi....."

Vote
Comments
Share

*_Oum Hairan_*
[20/06 4:27 pm] Oum Hairan: *ZARRAH*

_Tare da Alƙalamin_

*_Oum Hairan_*

_Bismillahir Rahamanur Rahim_

_Page 5-6_

*_Wattpad-realfauzahtasiu_*

*_Telegram Link_*
            👇🏻
https://t.me/joinchat/Gdtmu0TgTHu66CF7

____________________________
____________________________

Daquwa Inna ta watsa Mata tace “wato dana hanaki tsokanar bakiji ba kenan aikuwa tabbas zan hadaki da yayanki yacimin qaniyarki ni banason sakarcin banza Shiru tayi saboda tsoran kada Inna ta fusata ta hadata da Mudan tasan kashinta tsaf zai bushe ta miqe sumsum ta nade kayan gugarta ta sanya a jakar kayanta ta fice ta dauki bokati ta tafi debo ruwa sawu uku tayi ta qyale kasancewar dare ya riga ya fara tana shigowa sallar Isha kawai tayi ta shimfida taburmarta ta kwanta tana addu'a bacci ya dauketa.
Da safe ta riga Inna tashi saboda zumudin kudin makarantar da zaa biya Mata tayi wanka aka dauki kwalliya aka dau jaka ta fito cikin shirinta tsaf Ma'un Inna idan taga dama yar gayuce ta gaske komanta qwas-qwas Amma idan taso iskanci tafi kowa iyashi dumamen taliyar data boye jiya ta dauka taci ta kora da ruwan koko ta miqe tace “inna zan tafi"
Fito da kudin Inna tayi ta miqa Mata ta qirga zari sha hudu ta miqawa Inna uku da biyar tace "saura uku da biyar idan na dawo saimu siyo abinda zamuke ci kafin Allah ya kawo wata hanyar" Jinjina Kai Inna tayi tayi Mata fatan alkhairi ta fice ta nufi gdansu Jidda dake yafi nasu kan hanya nan suka dunguma suka tafi sunata hirarsu Asma'u na bata labarin irin wulaqancin da akeyi musu idan sukaje neman taimako sosai jiddah ke tausayawa qawar tata.

Da wannan hirar suka qarasa suka shiga aji suka fara daukar darasi Saida aka fito break sannan Asma'u ta nufi Office din Principal tayi sallama ta shiga principal din tanason Asma sosai saboda yanda malaman bangaren kimiyyar suke yabawa da qwazonta da ace makarantar tatace ma da tuni ta yafewa Asma kudin makaranta saidai kash batada iko.
Rusunawa tayi ta gaisheta ta amsa sannan ta fito da kudin makarantar ta miqa Mata tayi rubuce rubucenta ta miqanta receipt ta miqe har takai bakin qofa taji a bayanta ance “Asma'u Hussain" tsayawa tayi adan tsorace tace “yes mAh" murmushi tayi tace “meye yasa duk biyan kudin makaranta kece qarshe ne meyesa iyayenki sukewa karatunki ruqon sakainar Kashi bayan Kuma Ubangiji ya Basu dama domin yabasu ke me qwazo da son karatu?" Idanunta ne ya kawo ruwa tayi saurin daukewa tace “na gode mAh kawai ta juya ta fice daga office din principal din ta nufi inda sukecin abinci yau batada ko sisi sai kudin motarta don haka ta nemi guri nesa ta zauna tana kallon daluban wani na siyan wainar fulawa wani na siyan cake kowa dai da abinda yakeso. Jiddah ta hango ta nufota ta zauna kusa da ita tace “yadai naganki anan" dubanta tayi tace “to da Ina kikeson ganina?" Share zancen jiddah tayi da cewa akwai wani guy dana tama a bayan makarantar nan yau indai mun ganshi saina goge Masa hadda"

Zaro idanu Asma tayi tace “kayy Kinga ki rufa Mana asiri Principal tace mu daina kula mazan bayan makarantar nan yawancinsu duk yan shaye² ne" harararta Jiddah tayi tace “kefa wani lkcn farar kura ce me suka Isa suyi Mana basai mu gudu ba mu jasu har area mu hadasu dasu Sadiqu suci ubansu" Shiru tayi tana nazarin kalamanta kafin ta dago tace “nidai Babu ruwana bazanje garin goge musu hadda su su gogemin tawa ba" dariya Jidda tayi tace “bansan yaushe kika zama matsoraciya ba wlh Ma'u Allah ya shiryeki" bata Kuma cewa komai ba har suka koma aji Basu suka tashi a makaranta ba sai uku Wanda a qa'ida biyu suke tashi wani mugun malaminsu ne yabasu assignment me wahala shine suka bata lkc haka gashi yace a lkcn yakeso dukkan fuskokin daluban daka gansu kasan sun jigata da yunwa musamma Ma'u da batayi karyawar kirki ba gashi babu kudin break sun riga kowa something suka fito duk ta galabaita suka nufi get megadi ya Kuma taresu akan cewa principal tace kada su fita da daidai su bari su tashi gabadaya,

Neman guri sukayi suka zauna kawai Jidda taga qawar tata na kuka Asma'u babu juriyar yunwa ko kadan tasan dalilin kukan don haka ta miqe da sauri ta nufi shagon me gadi ta siyo musu biscuits pure blues dan saba'in ta siyo musu lemo jarka daya sukaci Saida sukaji dama dama asmai ta dubeta tace “dama kinada kudi shine kikaqi ki siya Mana break?" Harararta Jiddah tayi tace “wanne kudi ke gareni kudin motarmu ne naga zaki mushe na taimaka na siyo Mana muka taba Kinga malama an gama fitowa kawai miqe mu yanki burtali"
Chapter 2 · 0% Book details