← Book details Zarrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 33

Sashe 12

Zarrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi taja tace “nifa banson gulmarki nan ina ruwanki tunda kedai anyi miki abinda kikeso" sanin hali yasa Dijah cewa “kekam kin fiya masifa daga na kiraki mu jajantawa juna zaki kama yimin fada to ai shikenan sai kiyita yi nidai nazama cikakkiyar mace yarinya ko iyanan alamu sun nuna nafiki" murmushi tayi tace “to meye na gorin abinnan da ba dambe ba kowacce mace ma tana zuwa gurin lkc dai igiya uku ke gareki nima itace dani saboda haka banga bambamcin ba".........
Kashe wayarta tayi ta gyara kwanciyarta tasha bacci sosai har wajen daya sannan ta tashi tayi sallah ta gyara gadonta ta nufi part din Mimee har yanzu tana kwance inda ta barta mamaki ya cika Asmah tayi mata sannu da gda ta dago ta kalleta saida gabanta ya fadi ganin irin kwalliyar da Asmah ta caba cikin wani tsadadden less dake cikin lefenta, sarai take kallon Asmah tun daga sama har qasa ta zubawa hips dinta ido tuni Asmah ta fahimci kallon qurillar da takeyi mata tayi qaramin murmushi a ranta tace “jira dai madam ba damuwata mijinki ba amma dole ne kisan nafi qarfin matsayin da kuka ajeni"
Dagowa tayi tace “me kike buqata?" Iska Mimee ta furzar ta qanqance ido tace “kewai bakisan matsayinki bane a gdannan? Waye ya baki damar kwalliya?" Dagowa tayi ta dubi mimee tace “wai dake naji sunanmu daya a duniya Matan Dr Aseem Shaheed shiyasa nabawa kaina yancin kwalliya a gdan mijina....."

Wata muguwar tsawa mimee ta daka mata tace “Ubanwa yace miki matsayinmu daya dake yar matsiyata? Ke mece a mata da har zaki hada kanki dani??" Abinda Asmah takeso kenan ta juya cikin salonta na iskanci tana kada mata mazaunai tace “In kinga dama ma ki kirani da tafi haka nidai inajin kaina matsayin matar Mijinki bawai isar ki ce tasa na qudurta yi miki wannan aikin da kuka bani ba not sister tausayinki ne a matsayinki na patient kuma naji mijina yace cikine dake zaki haifa mana sanyin idaniya" tsayawa tayi ta juyo tace.
“Bari kiji wani abu ko Maryam naso ko bataso Asma'uh ta Aseem Shaheed ce zabinsa ce sannan inayi ne don farin cikinsa tabbas zanyi komai indai zaisa mijina abin alfaharina Happy domin nasan zamusha mango harda gwanda ke har water milon zan yanka nabashi a baki....."
Dafe kuncinta tayi da sauri ta dago sukayi ido hudu da Aseem dake tsaye, ya hade rai sai huci yakeyi maimakon tayi qoqarin yin wani abu sai kawai ta shammaceshi ta fada jikinsa ta qanqameshi ta rushe da kuka, raunin Aseem kenan A duniya baya qaunar kuka a cikin kukanma ya rasa masifar da tasa indai Asmah zatayi kuka sai yafi dagansa hankali fiye da yanda kukan kowa yake dagansa.
Sake qanqameshi tayi tana tura masa nononta a qirjinsa tuni baisan sanda ya dagata ba cak ya nufi saman da ita Mimee na tsaye sake da baki tana kallon ikon Allah suna shiga ya ajiyeta saman resting chair ya fada bathroom ya sakarwa kansa ruwa a ransa yanajin zafin kukan da ta zauna tanata rerawa har wani qara sauti takeyi, badan ya gaji da wankan ba ya dauro towel ya fito yace “oh gud ki daina wannan kukan haka na fada miki banso ko?" Ajiyar zuciya ta rinqa jerawa ya tsugunna gabanta ya kamo hannunta yace “ki daina yi mata rashin kunya duk abinda zakiyi ya tsaya iyakar ni dana daukoki" miqewa tayi zata fice ya fincikota da qarfi ya hadata da bango ta saki qarawa hawayenta qarfi tanajin sanda yasa hannu ya shafa shatin inda ya maretan yace “kinga gurin har ya tashi" tureshi tayi ya sake ruqota ya hadata da qirjinsa ya murdawa qofar key ya matseta sosai a sanyaye yace “me kika bawa Mimee taci da safe?...." Bai gama rufe bakinsa ba yaji an turo qofar an shigo, ya saketa d sauri Idanun mimee akansu wani murmushi Asmah tayi tace “Insha Allahu bazan qaraba kayi hqr kaji mijina" tana fadin haka ta juya ta fice tana yiwa Mimee Murmushin qeta, kitchen ta wucce zuciyarta tas ta fara hada abinda zata girka lkcn uku har da rabi tayi tuwon shinkafa ta dora ta rage gas din ta fice ta nufi part dinta tayi sallah da gayyah ta sake wanka ta canza kaya ta fito ta koma taci gaba da aikinta miyar zogale tayi musu ta sake yi musu jallop din taliya ta jere musu a dinning ta zuba a nata a collar ta bude qofar baya tayi ficewarta tanajinsu sunata bala'i itadai ko a jikinta an qudurta tayi ko zai rinqa zagin iyayenta bazata sake Mimee ta fahimta ba gara idan sun kebe sucinye iyayensu ma.....

_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: https://chat.whatsapp.com/IJkh1cP8h62Avsz2Zrcr2x

_*Zarrah*_

_*Fauziyyah Tasiu Umar*_

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

_*25-26*_

Tana shiga part din nata ta dauki wayarta tana latse latsenta tana murmushi hirar manyan mata na bata nishadi a group din DOMINKI YAR GATA na Oum Hairan wanda Aunty Hajar ta biya mata tasata a ciki tunda ta shiga batace komai ba saidai murmushi da takeyi wata matace a group din tace _“wato Jiya naji dadin lectures din da Malama Ummi tayi mana a gidannan nabawa kafura kuka kwana sukayi suna bala'i inajinsu dake baa dakina yake ba na kulle qofata"_ stikers wata ta turo ta dariya Asmah ta sauke ajiyar zuciya kafin tayi mgn taji wata tace _“ ai koni da nake ni kadai jiya Munji Happy nida Abban Salim har kyautar kudi yayimin unguwar da na dade ina tambayarsa sai gashi ya daukeni ya kaini, Mukam sai gdy Oum Hairan group din dominki yar gata 2 yana taimaka mana wajen samawa kanmu yanci gurin riqaqqun mazajen nan na zamani babu boka babu mallam"_

Suna taka da wannan tattaunawa taga ansawa group din mukulli bayan kamar mintuna biyar alamun rubutu suka bayyana a saman group din sallama ce ta fara shigowa kafin me rubutun ta fara da cewa _"kamar yanda kuka sani yau Oum Hairan ke gabatar da shirin zuciyar masoyi ba Aunty Mamee ce saboda haka zan koma gefe Nima nayi sauraro aunty mamee bismillah dalubanki na sauraronki💃🏻"_
Tasa alamun rawa tayi dif abinta shudewar yan mintuna aka fara gabatar da lecturer me taken *ZUCIYAR MASOYI* matan sunji nayi duk sunyi zukudun suna saurare" jinjina kai kawai Asmah takeyi taji manyan wada wadai tuni ta shiga hankalinta wani abin idan Aunty mamee ta fada har daukewa numfashinta yakeyi saboda kunya, ta jima a zaune ko sallah ta kasa tashi tayi bayan an gama lectures ne kuma aka tafi bangaren gyara Hajjiya mandiya hamshaqiya Oum Hairan ce ta karbi filin da cewa _“Da yawan iyayenmu mata suna damun kansu Idan zasu auradda yayansu da nemo musu maganin mata wanda a zahiri ba abinda ya kamata ba kenan abu mafi muhimmaci shine dauki yarki ki kaita asibiti ayi mata gwajin sanyi ayi mata hoton maranta idan ta tsallake batada sanyi fine idan kuma akwai sanyi to aiki ya sameki ke uwa dole ne kiyi aiki da hikima wajen nemawa yarki lfy domin kuwa indai da sanyi a jikinta ba namiji ba macema yar uwarta bazatayi qima a gurinta ba"_

Numfashi Asmah taja cikin tsoro tace "munshiga uku sanyi kuma? Tab to muda ko ararrabi baa jiqa manaba ya kenan?" Wawurar wayar tagumi
a kashe datar ta kira number Aunty Hajar ta daga tace “Aunty ki hau online oum hairan nayi lecture akan ciwon sanyi a group din DOMINKI YAR GATA nifa kaina ya kulle" kashewa tayi ta sake kunna datar ta rinqa bin bayanan a hankali tana nazarinsu tunawa tayi batayi sallah ba ta miqe ta dauro alwala tayi sallah bata qara hawa ba saida tayi wanka tasa kayan baccinta ta kulle part dinta ta haye gado taja bargo sannan ta kunna tanabin bayanan wanda bata ganeba tana tambayar Aunty Hajar saboda anriga angama lectures din taji bayanai sosai har ta dauki na aikatawa gobe da safe.

Washegari tun asuba data tashi bata koma ba ta gama gyaran part dinta ta sanya wasu yan iskan riga da wando rigar airmles ce wandon three quarter ta bude cikin akwatunanta ta dauki takalmi sawu ciki tasa ta hade gashinta tayi donnut dashi ta sauko daga saman da dan gudu gudunta ta bude qofar ta fice ta nufi gurin training din gdan tana yan guje²nta da tsalle tsallenta Aseem da ya dawo daga masallaci ya zauna a wani bangare na gurin ya zuba mata ido yana kallon yanda take sarrafa jikinta kamar babu qashi abin yayi bala'in burgeshi baisan sanda ya aje jaridar ya zubanta ido yana sauke ajiyar zuciya, dakatawa tayi tana duba agogonta tana share gumi.
Bakwai saura juyawa tayi ta nufi part dinta ta sake wanka ta sake kaya ta dauko wayarta ta nufi bangaren nasu bata tarar da kowa a parlour ba ta tabe baki ta fara hade kayan dake parloun bayan ta gama ta dafansu tea ta zubansu a flast ta soyansu doya da qwai ta jere musu tayi ficewarta tana fita suka fito qamshi ya cika gdan suka sauke ajiyar zuciya Mimee tace “wannan yarinyar ta shigo ne?"
Kallon falon yayi yace “idan haka kikabar parlounki to qila bata shigo ba" tabe baki tayi ta zauna a dinning din ta bude kayan abincin ta fara zubawa yayi murmushi yasakai ya fice a ya nufi inda yake parking motarsa har ya bude zai shiga yaji kamar ana kallonsa ya dagakai sama Asmah ya hango tsaye a corridor din samanta tana cilla teddy sama tana cafewa.
Chapter 12 · 0% Book details