← Book details Zarrah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 33

Sashe 28

Zarrah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ya gama ta shige daki ta shiga wanka ta fito tasha magungunanta tasa kayan bacci ta kwanta koda ya gama ya dade a zaune yana tunanin ko zata fito yajita shiru miqewa yayi ya murda handle din yajishi a rufe ya girgiza kai kawai ya shiga nasa dakin ya kwanta. Hakanan sukaci gaba da rayuwa shikam yanashan wahalar rayuwar duk wani nauyi dake kanta na kula da duk abinda ya shafesa zata sauke masa hatta dakinsa bata fasa shiga ta gyara masa ba amma taqi bashi damar ya kusanceta duk shisshige matan da yake da rara gefen da yakeyi tana kallonsa amma taqi bashi hadin kai.
A cikin kwanakin ya gama musu komai na tafiyarsu Mimee tanacan shanye da baki tana jiran yaje ya bata hqr wai ita matar so ya dauke matarsa suka daga sukabar qasar, aikuwa ranar da taji lbrn tafiyar tasu bata iya bacci ba kira kam takira wayarsa yafi sau dari bata shiga dole ta hqr a washegari kuwa Naja'at qanwarta tayi mata jagora gurin bokanta sukaje ta baje masa komai kamar gaske yayi surkullensa fuskar Aseem din ta fara fitowa cikin Madubin nasa sannan Asmah kwance a cinyarsa daure da drip wani baqin kishi ya tasowa mimee ganin yanda yake wani shafa cikin Asmah tace “nifa mal cikin nan nakeso ya fara lalacewa inyaso bayan ya zube itama sai a kadata ta kama gabanta shikuma a dasa masa qinta yanda ko uwarta zata yanka ta bashi bazata burgeshi ba"

Dariya bokan yayi ya mayar da hankalinsa ga surkullensa ya dago ya dubesu yace “abu daya zai yuwu biyu bazai yuwu ba" da sauri suka dubesa ya sake kecewa da dariya yace “zasu dawo gida a warware bazasu dawo tare ba zaa rabasu amma bazamu iya cire masa sonta ba saboda ba son faraddaya yayi mata ba a hankali sonta ya zaga jininsa da bargonsa idan kinga ya rabu da qaunarta to ya rabu da rayuwarsa ne abu na biyu bazamu iya taba wannan ciki ba domin kuwa ya rubutowa kansa manyan qaddarori da idan mutum ya matsa ganin bayansa to shi zai fece ya sanqama lahira babu shiri"
Gumine ya karyo mata ta miqe da sauri tace “aa nifa indai ukunnan bazai yuwu ba to duka abarshi saboda rabasu ba shine muhimmim abuba rabasu da qaunar juna sannan ni nasan indai shegiyar yarinyar nan ta haihu a gdannan to kashina ya bushe yanda Aseem keson haihuwa ruwa ma saida umarnin danta zanshashi a wannan gidan Boka ka sake dubawa dai idan akwai wata mafitar ayi amfani da ita" tana fadin haka ta fice ya dubeta ya kece da dariya yace “shegiya tsinanna mara albarka wacce ta kwashe kayanta daga gaban ma'aiki bazan rabasu dinba hakanan kawai saina rabasu bayan da bakinki kikace yarinyar tasha wahala a baya" sudai basu tsaya ba suka dunguma suka shiga motarsu driver yaja kowanne zuciyarsa babu sanyi wata uwar ashar Mimee ta saki tace “wlh ko zanyi yawo babu pant saina tarwatsa rayuwar Asma'u a gdan Aseem koda nima zan rasa nawa farin cikin"..............

_*Oum Hairan*_
[29/06 4:41 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

_*Fauziyya Tasiu Umar*_

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

_*57-58*_

Tunda su Asmah suka daga zuwa Germany ranar da sukaje ta kwanta rashin lfy kwananta uku a kwance yana kula da ita yana harkar data kaisa suna rayuwar ne a yanda suka farota tun a 9ja duk da cewar yana cutuwa matuqa amma yayiwa kansa alqawarin iyakar lkcn da zata sauko don kanta bazai taba takura mata ba shi kansa yasani ya cutar da ita a baya shekara daya suna kallon juna babu uwar da yake tsinana mata lkcn da ya kamata ta samu kulawar tasa kuma ya bullo mata ta wata sigar to shi meye zaisa ya takurata sai ta tausaya masa bayan shima baiji tausayinta ba a lkcn da ya dace yaji tausayin nata?
Kwanakin nasu sunayi mata dadi kulawar da yake bata tana tsumata sosai baya gajiya da tarairayarta  da nuna kulawarsa akan cikin jikinta, kwanakin sunata tafiya tausayinsa na nunkuwa a ranta sosai musamman yanda taga da dare baya iya bacci ya tashi yakai sau goma a dare kafin asuba idan ta farka kuma yace mata karta damu yana nazarin wasu Abubuwa ne, ta ayyana hqr yafi sau nawa amma kunya ta hanata nuna masa mubaya'arta gani takeyi kamar zaiga rashin kunyarta ko zaqewarta,
Ranar wata Asabar tana kwance a daki tana duba littafin Hisnul muslum wayarta ta shiga ruri ta kifa littafin a kan cikinta ta dauko  wayar number Jiddarh tagani ta kara a kunnenta tare dayi mata sallama suka gaisa ta tambayeta gda ta jikin Innarta.

Shiru ce ta dan ratsa kana Jiddarh tace “meye yake damunki ne Asmah? Ina hankalinki da iliminki ya tafi da kika yarda kike daukarwa kanki wannan nauyin me girma da baki da gurin ajiyeshi?" A mamakance tace “me kuma nayi Jiddarh?" Numfashi Jiddarh ta sauke tace “dazun Inna ta kirani take fada mani cewa mijinki ya kirata yace ta tayashi baki hqr kina fushi dashine akan wani dalili da yaqi fada mata, nasan bazai wucce akan abubuwan da suka farune kika dauki abin kikasa a ranki har ya bawa shaidan gurbi a zuciyarki kike ganin ba komai bane don kinyi watsi da haqqoqin mijinki ko?" Shiru tayi cikin sanyin jiki tama rasa meye ya kamata tace murmushi Jiddarh tayi tace “idan ya kasance mijinki ya cutar dake a cikin rayuwar aure kada kice zaki rama ta hanyar qauracewa shimfidarsa wannan laifine kuma kuskure ne mai girma da mu mata mukeyi Asmah idan wani ya jure wani bazai iya jurewa ba shin kinsan irin azabtuwar da yakeyi da har ya kasa jurewa ya iya tunkarar Inna da mgnr nan?"
Hakana taji zuciyarta ta karye hawaye suka tsiyayo mata jiddarh ta katse shassheqarta da cewa “a matsayinki na wacce take dauke da sabon mutum a jikinta ya kamata kiyi qoqarin zamowa uwa ta kwarai abar koyi da alfahari a rayuwar al'ummar da zasu wanzu ta dalilinki shin ya zaayi hakan ta kasance bayan kin kasance mara yafiya da jin qai ga mahaifinsu a lkcn da yafi kowanne lkcn buqatar jin qanki? Ita mace ta qwarai kullum cikin gaggawa take akan abinda zai faranta zuciyar mijin da ubangiji ya hadata dashi koda kuwa shidin ya kasance cutarta yakeyi Asmah ina baki shawara don Allah kiji tausayin mijinki kada ku zame masa uku bala'i saboda ke uwarsa na neman yi masa baki saboda matarsa sannan kedin kuma ki kasa basa farin ciki don Allah da wanne zaiji?"

Kukanta ne yayi qarfi yanda har Jiddarh take jiyo shassheqarta taja fasali tace “ya zanyi Jiddarh Allah tsoronsa nakeji inason na nuna masa komai ya hucce amma tsoron jizginsa yana hanani kaiwa ga hakan Jiddarh Aseem wani irin mutum ne da bazaki gane ya yake ba indai baki zauna tare dashi ba......" Katseta tayi da cewa “haba don Allah saikace ba mace ba asmah duk yanda zakiyi ki saita mijinki bazai gagareki ba saidai idan haka kikaso dama ki zauna kuna kallon kallo namijin daya fishi taurin kai ma ana juyashi bareshi da rauninsa ya riga ya gama bayyana akanki kiyi qoqari ki zame masa matar da idan ya kalleki zai rinqajin farin ciki a ransa kema Allah zai faranta taki rayuwar kada ki yarda ki zamo mahadin dayar ku taru kuyi baqi a gurin mijinku plz don Allah idan ya shigo kije ki durqusa a gsbansa ki basa hqr nasan zai tambayeki dalili idan ya tambayeki kice, yakai mijina mafi alkhairi sama da duk mazajen dake duniya nasan na sosa zuciyarka da qaurace maka ds nayi tsayin kwanaki inajin tsoron kada wannan dslilin ya zamo silar fushin ubangiji a gareni shiyasa nakeso kace ka yafemin kuma ka tabbatarmin da hakan yanda zuciyata zatayi sanyi na samu nutsuwar cewa mijina ba fushi yskeyi dani ba"
Sosai Jiddarh ta rinqa bata shawari har saida taji a ranta komai ya wucce sannan take fada mata itama ankawo kudinta Dr Mus'ab na Asibitin Aseem shine wanda Allah ya zaba mata, sosai Asmah tayi farin ciki tare dayi musu fatan Alkhairi sukayi sallama ta ajiye wayar tanata tuntun tunin kalaman tabbas gsky Jiddarh ta fada mata dolene ta zamo salihar mata me rangwame yafiya da afuwa ga mijinta kafin ta zamo managarciyar uwa abar alfaharin yaya.
Miqewa tayi ta gyara dakinta ta fito parloun dakin hotel din da suka sauka shima ta gyara ta nufi kitchen abin mamaki babu abinda bai aje musu na amfani ba dangin kwadayi tayi murmushi tanajin wani yanayi game dashi iyakar abinsa bai yarda da wasa da haqqin ciyarwa da tufatarwa da abinda ya shafi lfy ba, ji tayi tanason burgeshi hakanan ta dauki flower ta kwaba ta gasa ta gashin gurasa ta koma gefe taja da baya tayi masa miyar ganye da taji naman rago sai zuba qamshi takeyi ta zuba a mazubi me kyau ta dawo ta hadansa lemon kankana shima da yaji sugar da madara tasa qanqara ta mayar dashi freedge ta ja da baya tayi farfesun hantar ta kasancewar ita kadai takeci ta zauna a cikinta.

Wanka tayi ta dauki wasu fitinannnun riga da wando tasa sunyi matuqar karbarta ta gyara gashinta ta daure ta dauki wata hula tasa ta saki jelarsa baya tasa yar qaramar barimar kunne tayi kyau iyakar kyau abin sai wanda ya gani ta shafe jikinta da turare ta dawo parloun ta zauna tana chat da qawayenta tanajin dadin yanayin duk da cewa a taorace take da haduwar tasu ta yau amma haka ta rinqa tausar kanta.
Bataji shigowarsa ba saijin dumin hannunsa tayi a saman  cikinta ta saki wayar a kasalce tare da dago kanta suka kalli juna idanunsa na cikin nata ta lumshe nata tare da dora bakinta a wuyansa ta sakar masa wani kiss me kashe jiki tace “barka da dawowa mijin....." Sai kuma tayi shiru kunya ta kamata yayi murmushi ya hade bakinsu ya limshe idonsa yana sakar wata ajiyar zuciya.
Chapter 28 · 0% Book details