← Book details Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 22

Sashe 9

Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mero da ta gabatar da cek din da zata fitar su kansu sun girgiza Anna da suka duba asusun izzatu sai Basuyi mamaki ba atake suka Bata takardar da zata cike ta cike aka fitar Mata da kudin duka sai ta raba su ta saka milyon biyar cikin asusun ta ta fito da milyon biyar don taje ta biya bashi sau Kuma ta aje don bukatu

Ta SHIGA motar ta ta nufi gida don ta Kira me mota yazo gida ya amshi kudin shi saboda zai fi sirri
Sai dai wani Al amari dake Shirin faruwa ya gigita sister mero inda wata mota ta Sha gabanta cikin azama ta taka burki don kadan ya rage ta banki motar da ta Sha gabanta

Atake gambo mafiyas ya fito ya na bude motar mero Yana kanga Mata bindiga agoshi Yana tambayar ta kudi
Bataja ba ta jawo buhun kudin ta Miko mishi ya amsa ya koma motar sukaja motar aguje suka bacewa ganinta inda mero take sauke ajiyar zuciya ta iso gida tana tunanin waye ya San zataje banki? Babu ko shakka izzatu na da hannu akan wannan abin da akayi Mata koma ita ta turo Mata bakaken mabiya sai Kuma ta tuna da yadda izzatun taso yi Mata dungu akan kudinta sai kawai ta gano mugun kulli ne izzatu ta kullo Mata inda Kuma wata zuciya ke Bata shawarar tashi kije kuyi ta ta Kare Babu Wanda yasan zakije banki sai ita to komai zai iya faruwa

Aikuwa ta fice zuwa gidan izzatu inda ta badda sawu da saka nikabi ta tari napep ya kawota kofar gidan izzatu inda Kuma cikin sa a ta ga motar da tayi Mata fashi ta faka har katon basamuden da ya yi Mata atakin da bindiga ya fito Yana rike da buhun kudinta inda ta tabbatar dai izzatu ce me alhakin yi Mata hakan, to yanzu meye abin yi? Anya kuwa idan tace SHIGA zatayi gidan izzatu ba zata saka katon ya illatata ba????............
[5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*page 18*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

.........Wata zuciyar tace Mata shiga kawai ki karbo hakkin ki tunda ma gashi kin gani ya kawowa wadda ta sakashi
Har ta cire kafa zata tunkari kofar shiga gidan sai Kuma wata zuciyar ta kwabeta
Akul Kika SHIGA gidan can yadda Dan ta addar can ya nuna Miki bindiga komai zai iya faruwa gara dai ki koma gida ki sako sabon lale Amma SHIGA gidan can ayanzu akwai matsala
Sai Kuma ta karbi wannan shawarar da fuskar fahimta ta juya gida

Gambo mafiyas ya direwa izzatu kudin a gabanta inda inda ta Gane kudin ba duka bane Amma dai an rage ta Zaria rafar dubu dari ta bashi ya karba Yana godiya inda yace da wani aikin ya samu ta kirashi
Da haka ya fice Yana zukar tabar iblis din shi

Abinda izzatu bats sani ba shine shima gambo mafiyas sai da ya wari wasu kudin ya boye don harkar duka Babu Amana Amma izzatu Bata Gane ba ta dauki kudin ta mayar daki

Komawar sister mero gida ta doko wa izzatu waya inda tana ganin Kiran meron gabanta ya Sara dass ! Amma sai ta maze ta daga da salon bagararwa

"Sister mero ya kike ya aikine?
"Lafiya Amma abinda Zan fada Miki izzatu karki yarda kice irin wannan wasan zamuyi dake don na rantse Miki da Allah sai na kaiki kasa warwas..........

"Me akayi Kuma mero?....... .
"Karki yaudare Ni don Ni ba yarinyar goye bace idan kudin ki kike so ai ba sai kin turo min babbakun mabiya ba sai in maido Miki in karbi Yar mutane.........

"Nifa bangane Abinda kike nufi ba mero wani Abu ya faru ne?
"Kin fini sanin abinda ya faru saboda Babu Wanda ya San zanje banki karbar kudi sai ke to Akan me Zaki turo min Dan fashi bayan Ni da ke taimakon juna mukayi? Kuma magana Kare nazo dazu na tarar da shi Wanda Kika sa yayi min fashin ya Zo gidan ki da buhun kudina to saurareni da kyau na rantse Miki da sarkin da ya huran numfashi da tassarufin lamurana sai kin biyani kudina Baki Nan da awa ashirin da hudu ki turo min kudina ga lambar asusuna Nan Zan turo Miki idan Kuma kina bukatar sauran kudinki Zan maido Miki in karbi Yar mutane duk shawarar da Kika yanke Ina jiran kiranki.........
Dit ta yanke wayar tabar izzatu da kyalkyala dariya

"Uhum mero kenan na kula in ba kwanji na na motsa ba Zaki zame min kadangaren bakin tulu to duk Zan hada in kashe da tulun da kadangaren don Banga amfanin su ba

Akarshe dai ta yanke shawarar turawa sister mero kudinta don suna game wayar sakon lambar account din ta shigo wayar izzatu a take kuma tayi Mata transfer ta wsyar kudinta suka SHIGA inda sister mero tayi murmushi

"Uhum izzatu kenan tunda wannan turbar kike son mubi to Zan nuna Miki Ni har gobe takadarci Yana min Rana Baki sanni bane Amma Zan nuna Miki kece karamar Yar iskace Nasha gabanki har abada ke gaba da abada ma na wuce da iyawar ki Zan Kuma waiwaye ki don wasan mu Bai ma fara ba karamar marar kunya dake bileja

Itama izzatu anata bangaren Tasha mugun Alwashin akan mero saboda ta kula itace zata zamo Mata matsala to su zuba shege NE zai fasa Bata santa bane nata iskancin kawai ta sani Bata San nata ba Allah yasa tsautsayi ko azal ya sa mero Kiran wayarta ko ma zuwa gidanta taga yadda ake kera Rashin mutunci

Tom Bari muga yadda Za ayi haduwa ta gaba da sister mero da izzatu waye zai FASA KWAI.............
[5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 19*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

.........Wata irin Rashin lafiya ta Kama dungo uwar Kabir mashi ciwo irin Wanda Bata taba yin irin taba Amma da yake ta iya jarumta da hakuri haka take ta jaganiya da Yan yaran rainon ta yaran Babu Wanda ya shekara biyu ga Yar banzar rigima wancan yayi kuka ta rurruga wancan yayi fitsari ta wanke wancan yayi Kashi ta wanke ba zata taba samun sauki ba sai sunyi bacci ko iyayen su sun karbesu Amma Duk da haka ciwon da takeji Bai sa ta kwanta ba duk da kallo Daya zakayi Mata ka Gane Bata da lafiya matukar dai kana Gane lamarin Rayuwa sai dai Rashin kudi ya Hana Mata zuwa Asibiti inda ta Bari sai ta karbi kudin rainon ta idan anyi albashi sun karbi kudin su

Sai dai kafin albashin ciwo yaci karfin ta har ta Fadi kwance ciwo riris inda har rainon ma ya gagara
Wata daga cikin masu kawo yaranta me suna Jamila ta shigo gidan inda ta iske dungon kwance abin tausayi

"Subhallah ladidi Baki da lafiya ne? Wallahi kuwa Jamila Ina Dan gidana fahat? Yaron da take raino ya SHIGA dago Mata hannu Yana son ta dauke shi saboda sunyi sabo me karfi da yaran
Ta Mika hannu ya taho ta rungume shi inda Jamila ke kallon ta cikin tausayawa

"Amma ladidi kinje Asibiti kuwa? A a Jamila banje ba saboda Babu kudi hannu na..........
"Karki damu taso muje in kaiki ai lafiya tafi komai

Jamila ta kaita Asibiti aka dubata aka Bata magun guna suka juyo gida inda jamilar ta kashe kudi masu dama sama da dubu goma Sha biyar duka dawo gida gungo nata zuba godiya don gaskiya Jamila na mutunta ta ko abinci me Dadi tayi sai ta Aiko Mata bare ta dafa nama

"Karki damu ladidi ai mun Zama Daya Babu komai ke dai Allah ya Baki lafiya
Ta amsa da ameen ya Allah
Haka Tasha magani har sauki ya samu
Inda wata ya cika Jamila ta dauki albashinta ta kawowa dungo hakkinta Amma dungo tace Allah ya sauwake wallahi ba zata karba ba Amma Jamila tace wallahi sai ta karba.....

"Haba Jamila don dai nice uwar marasa mutunci sai na karbi kudinki ?......
"A a sai kin amshe su wallahi banyi don komai ba sai don Allah da zaman tare Allah ya Kara Miki lafiya ta aje Mata kudin ta dauko danta ta fito inda ta bar dungo da zubar hawaye Wai yau Dan da ta haifa ta wahaltawa shi ke gudunta yayin da can wasu da Basu hada komai ba sai musulunci da mutunci suke wahala Mata har suyi Mata abinda danta Bai yi Mata ba

Babu abinda yafi Kona ranta irin yadda ta taka har gida ta sanar dashi zubar bangon ta Amma har yau Bai tada Mata ba asalima an kusa shekara Amma har yau zuwan shi guda Kuma yaga yadda aka saka zana amma bai Kuma zuwa ba Kuma yanzu da mutuwa tayi ba lallai ya sani ba to in ta mutu ma Yana da asara ne?

Amma dayake tana mishi uzuri sai ta bar abin ya wuce ko aranta Bata aje shi ba taci gaba da rainon yaranta Wanda ke debe Mata kewa fiye da zato inda makocinta malam Ali ya shigo ya duba jikinta inda yake tambayar ta Kabir ya Zo kuwa? Tayi murmushi "Bai zo ba malam Ali , to Allah ya Kara lafiya da haka ya fice Yana mamakin wannan yaro da duniya ke rudu duk shaharar shi Amma abin haushi ya yasar da uwar shi sai tayi raino ta ke ciyar da kanta Amma shi Yana can cikin katon gida daga shi sai matar shi suke hutawa Anya kuwa Bai dauko hanyar lalacewa ba?

Uwafa? Uwar ma irin dungo wadda yasan yadda ta wahalta mishi har ya tako matsayin da ya tako? Babu wata riba ko nasara da ake samu ba ta silar uwaye ba koma an sameta to zata sulale saboda Babu albarkar iyayen sai yayi mishi adduar Allah ya shirye shi ya kuma shiryi Al ummar musulmi Baki Daya..........
[5/16, 11:57 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*
Chapter 9 · 0% Book details