Sashe 2
Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari ta nufi gidan Asma u inda ta tabbatar ba zasu kwashe da marar arzikk ba musamman dangin shi dake da burin yada Mata bakar magana to yau Suma zata nuna musu uwar su ma dai dai take da ita bare su kanan shegu
Da haka ta fice ta iso gidan sunan Wanda ya ciki ya batse da Yan uwa da abokan arziki ta fito mota tana shakar iska dai dai inda ta hade fuska don kar su Raina ta.......
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*
*NA*
*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*
_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_
*Page 3*
*___________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*__________________________________*
...Sanye take da leshi me kalar ruwan kasa me cizawa wato coffee brown kafarta sanye da takalmi me tudu Wanda ya Kara Mata tsayi hannunta cike da warwaraye da zabban zinariya yayinda kwalliya ta taimakamata afuskar ta don in baccin kwalliyar to da ba zata kallu ba ahalayya Kam taci sunan ta izzatu don izgili da dagawa ba a magana hakama Bata Faye shiga mutane ba saboda tana ganin ta zarce hada kafada da mutane musamman idan Basu da kumbar Susa don kuwa mijin da take aure eng abdukarim fitaccen Dan kwangilar dake samu kwangila daga gwamnatin tarayya Wanda sunan shi ya tumbatsa aduniya shine barazanar ta da homar ta sai dai inda matsalar ta take shine tsayin shekaru Bata haihu ba inda har dangin shi ke yada Mata magana da habaici da arashi karshe ma said ga hajiyar shi da kanta ta wanko kafarta ta wanke ta soso da sabulu inda itama ta daura damarar yakar duk Wanda yace Mata kulle zata ce mishi Cass
Ta shigo gidan sunan inda ta iske ana ta sabga ta dauke kanta tana hura hanci
Da yawan Matan dake gidan suka bita da kallo suna kallonta awatse itama tana musu kallon sai dai aganni abarni ko Kuma bakin ciki ya kashe mutum.
Kai tsaye ta shiga dakin me jegon Wanda yake cike da Yan uwa da dangi
Tamkar wadda ta shigo cikin wata najasa haka take ta shakar hanci tana dauke Kai inda asmau take kallon ta tana mamakin daukar kanta
Bata gaishe da kowa ba ta jawo kudin ta mikowa asmau
"Gashi inji AK yace akawo Miki Yana Miki barka ta Mika mata tana dauke Kai.
"Madallah na gode inji asmau ta fada tana Miko Mata jariri
Shafa tace "Kai Yaya ak ya soma rage kyauta ba kamar da ba.......
Samira ta karbe da fadin
"Yaya eng ba zai rage kyauta ba wata Kil dai sauran kudin ne sukayi dimuwa Yar gidan ikon tashi ta na baza irin wannan ikon Allah yaushe zaiyi abin kuzo ku gani? Samira tace Ni wallahi Ina tausayin shi bawan Allah kowa da danshi Amma shi Babu Kuma an rufe mishi idon ganin gaskiya.....
Ke dai Bari Yar uwa sai dai aci akima katon Kashi a hau mota ashiga gari ana hura hanci Ni wallahi har gobe mamaki nake yayun mu sunyi Rashin dacen Mata mu Kuma mazan mu sunyi dacen Mata....
"To ko kina da Sha awa ne akan yayan naki shafa? Cewar izzatu da tagaji da Jin shaguben su
"Me kike nufi da ko Ina da Sha awa? Inji shafar,
Izzatu tace
"Wai ko ki aure shi nake nufi tunda Ni na tsare muku gaba na tsare muku baya tunda kina haihuwa kawai sai ki kaso auren ki kizo kuyi Maja Kinga sai kema ki biyo layin masu sa ar mijin harma ki yi abinda nakeyi.
Sai suka harzuko Mata su duka tamkar zasu cinyeta.
"Me kike nufi da wannan maganar? Dama kinzo don kici Mana fuska ? To aikuwa Wallahi jikin ki zai gaya Miki zakuma ki Gane karyar iskanci kike...
Izzatu ta Mike tana aje jaririn
"To Bari agano Yan iska tsakanin Ni da ku ai a yanzu dai dai nake da uwar mutum ma da uban shi bara ku gayyar na gayyaro
"Eh kice dama da abinda ya kawo ki yau har hajiya ta samu tukwaicin zagi gareki ? Sai saka soma musayar yawu har an daura damarar dambacewa inda shafa ta rarumi izzatu suka soma dambe har suna yagawa juna sutura inda a karshe sukayi Mata taron dangi har suka fasa Mata goshi . Inda gidan suna ya hautsine wasu suka shiga tsakani izzatu ta taho da Alwashi kala kala Alwashin karshe shine rabuwa da ak
Kwana biyu da yin hakan me gidan ya dawo daga tafiyar da yayi ayadda taso ba zata Kuma kwana gidan ak ba Amma wani Abu da ta kasa ganewa shine ak kwarjini ne gareshi Koko son shi ne takeyi da har in tayi arba da shi take mantawa da kanta? Ganin ak yasa taji ko za a dawo da bara bana ba zata Rabu da ak ba
Ta tarbeshi cikin salon kissa da kisisina Wanda take siyeshi har ma ta mantar dashi tunanin wata ya mace.
Washe gari ya fice zuwa gaishe da hajiya Mama inda acan ya karbo umarnin hajiyar na ya karo aure ko Kuma ita tayo mishi
Ya dawo inda ta kula da Yana cikin damuwa duk da Bai fada Mata ba Amma ta San kwanan zancen don haka sai kawai ta fada mishi yadda sukayi da Hajiya. Ya dubeta
"Ni kamar Ni ace za ayi min aure ai kamar an sarawa matar da aka aura min aiki.
Ta Sha mur tana hade fuska
"Nifa har yanzu kaki fito Dani duhu akan gwajin da akayi Mana Amma ko baka fada min ba na san an samu matsala ta bangarenka don da akaina aka samu matsalar da tuni ka bi bayan hajiya ka karo aure shine ka rufe min har kana tsallake kasa neman lafiya to kasani Nima hakuri na ya Kare tunda hajiya ma tazo har gida taci min fuska akan hakan bare su shafa dake fasa min goshi
Lokaci yayi da ya kamata ka fito ka fada musu gaskiyar magana akan Kaine me matsalar don su sakar min Mara nayi fitsari idan Kuma na gaji da mugun halin su sai ka sauwake min auren ka kawai.
Yayi murmushi Yana dubanta
"Wa ya fada Miki magani naje nema India? Yo har sai an fada min ga Abu abude? Ai na San halinku ne maza na Rashin adalci da Akaina aka samu matsalar nan da tuni ka samawa kanka mafita to Nima na gaji
Ya Kuma yin murmushi " to haka din ne Allah ya bamu lafiya Amma Ina so ki sani Ni haihuwa da ake ta maganar ta akaina ban wani damu ba saboda na San komai Allah NE ke yin shi idan Ina da rabon haihuwa Zan haihu idan Kuma bani dashi auren ne kawai ake da ikon yi min Amma haihuwa Babu me ikon bani ita in ba Allah ba So ki bar damuwa hajiya Kuma kiyi Mata uzuri Dole ne taji tausayina Amma ko ita ki Bari Zan fahimatar da ita zata Gane sai dai ki sani ba Zan lamunci Raini gareta ba duk abinda zatayi Miki saboda kin rabeni ne idan Kuma kina sona Dole ki girmam min mahaifiyata don su shafa in sukayi Miki zanci mutuncin su Amma akan hajiya komai zai iya faruwa
Ta dubeshi cikin Jin haushi da takaici
"Kana nufin sai don Ina sonka sai in Bari hajiya ta takani akan abinda ba laifina bane?
Shima ya dubeta cikin Jin haushin abinda take kokarin fada akan mahaifiyar shi........

*Page 4*
*_____________________________________*

.........."Me kike son ce min ne"? Ko hajiya Bata haifeni ba nayi Zaton girmanta zaisa ta ci albarkacin sa bare kuma Ni da kaina. To kar ki Fara don Zan iya jure komai akaran kaina Amma ba Zan jure ko kallon banza ga hajiya ba bare ki nuna Mata yatsa.......
"Ohooo sai nice za a iske gida azageni in Kuma shiga sabgarsu su zageni saboda Ni ban San yanci ba ko kuma shago aka bude na fito ko Kuma daga sama na fado? "To na rantse maka Babu shegen da Zan Kuma yarda ya taka Ni in zuba ido in kyale shi don yanzu Kai nakewa Alfarma ba kamar Ni da suke zaton kayi min Alfarmar ba sai Kuma ka shirya sanar dasu Kaine da matsala ba Ni ba.
Ya dubeta "Ina fatan cikin shegun da ba Zaki yarda su taka ki ba Babu hajiya? Kiji ki Kuma kiyaye Babu wani Abu da hajiya zata so ko ta sani Wanda ba zanyi shi ba don bani da wani fata ko buri sai na in rabu da ita lafiya. Ko auren take so nayi zanyi don zanyi biyayya agareta sai ki kiyaye.
Tayi wata kwafa ta shige daki ta barshi da yi Mata rakiya da ido kafin yayi murmushi kishi manya kowace mace da kalar nata abinda ma yake tambaya shine shi kishi dabi a ce ko hali ne?
Tunda sukayi haka sai izzatu ta fito da sabbin salo tamkar wadda ake zugawa Amma dayake Allah yayi mishi hakuri sai yayi Mata uzuri akan cewa maganar hajiya ce ta sa ta daukar Kai
Sati biyu Yana gida Yana kallon idon mikiya a tashar farin wata shafa ta shigo ita da wata budurwa me shegen kyau ya tashi zaune inda izzatu ke kallon su awatse
Suka zauna suna gaishe da shi inda ko kallon izzatu Basuyi ba
Bayan sun gaisa shafa tace
"Dama hajiya ce tace na kawo maka lubabatu gata nan kanwar mijin asiya ce idan Allah ya yi sai ku dai dai ta".
Lubabatu ta sunnar da kanta kasa cikin Jin kunya inda yaji wani Abu marar Dadi in Banda hajiya yaushe zata turo mishi yarinyar har gida Mai makon ma ace yaje ya ganta.
Izzatu da take kallon su cikin kaskanci ta tofa albarka cin bakinta.