← Book details Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 22

Sashe 17

Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yamma ya fito da zummar siyo kayan shayi ya wuce ta kuki cafee inda ya hango ta tafito daga kukin rungume da takardu ta bude motar ta SHIGA ta ja ta nufi gida
Atake ya Gane kuki ta fito zuwa dazun me yuwa computer take karanta
Ya wuce abin shi itama ta wuce batare da tasan yanayi ba

Satin da gambo mafiyas ya dawo daga Lagos ya Kuma samo abin duniya Wanda suke karewa ga Matan banza da kayan maye don basa tsinana abin arziki don haka ya Isa gidan izzatu Yana zukar tabar iblis wiwi

Da sauri ta toshe hanci tana tofar da yawu
"Haba gambo meye haka zaka shigo min da wannan shegiyar tabar me warin Kashin jaki? Don Allah koma waje ka zuke abinka ko dadin me kukeji acikin zukar hayaki hayakinma irin wannan da ko dadin Shaka Babu?..........."yi hakuri hajiya kan ne in Babu hayaki fanko ne Rayuwa ta in Babu mandular Nan akwai damuwa har Rashin lafiya nake kwantawa idan ban busa ta ba

Ya murtsuke sauran ya saka aljihunshi
"Yauwa to haka dai yafi don har kaina ya soma juyawa Nima ka sakani kwalewar Dole

"Yauwa hajiya Ashe akasi aka samu wurin aiki?
"Ai shiyasa nafi yarda da aikin ka yanzu Yaya za ayi kenan?

Ki bar komai a hannu na hajjya Ina me tabbatar Miki Nan da Rana irin ta yau wancan mutumin ya SHIGA UKU ke dai ku tanadi kudi don kin San Ni bana tare da tsautsayi ko kuskure bare wani Abu Wai shi sabani.......

"Karka damu gambo idan aiki yayi kyau ma za a biyaka kudi lunki uku Kai dai baje basirar ka kayi aiki me shegen zafi don ka samu sallama me kyau....

"Angama hajiya bani sati guda Daya kacal zakiji mugun albishir da haka sukayi sallama ya fito ya Kama gabanshi inda izzatu ta Kira Kabir take sanar dashi yadda sukayi da gambo mafiyas yace yayi daidai Kuma zai biya gambon lunki hudu ma ko biyar matukar dai aikin shi yayi sanadin fakuwar eng AK

Cikar satin da gambo mafiyas ya diba yayi daidai da kammaluwar aikin shi inda ya Kira Kabir yace yaje wurin hukuma ya sanar da akwai wani da yake kisan yaran mutane yau ya kashe wata yarinya ya sako a motar shi don haka su tashi Jami ansu da binciken motocin mutane ta haka ne tarkon zai Kama eng AK.

Aikuwa atake Kabir mashi kashe arna ya Kira wayar D P O ya sanar dashi abinda gambo mafiyas ya sanar dashi inda Kuma suka tashi Jami ansu aka soma checking point Wanda duk motar da zataje ko tazo sai me ita ya fito ya bude but sun caje komai kafin su bashi izinin tafiya

Bawan Allah eng abdukarim ya taho batare da sanin mugun qullin da aka hada mishi ba ya taho inda ya iske dogon layin na checking point Wanda ake ta bincike motoci shima ya bi layi batare da sanin shi ake son ganin baya ba ba Kuma Wai idan yajuya zaiyi tafiya ba. A a ganin baya na har abada inda ake son kasa ta rufe idanun shi................

Ubangiji kayi Mana sutura kar ka Bari makiya suga bayanmu 🤔
[5/22, 7:24 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 33*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

........Sannu ahankali akazo Kan eng AK Wanda ke kallon yadda ake binciken motocin mutane har akazo gareshi

"Ranka ya Dade muna son duba cikin motarka idan Babu damuwa.......

"A a Babu komai yallabai Bismillah ya fito Yana daga musu cikin motar suka bincike ba su samu komai ba sukace ya bude musu but

Ya kewayo ya soma kokarin bude but din Amma wani abun mamaki tamkar an sakawa but din kwado yayi yayi ya bude Amma yaki buduwa yayi iyakar kokarin shi Amma but ya ki buduwa ya dubi Dan sandan Yana sharce zufa
"Ranka ya Dade wallahi yaki buduwa karfen nasara kenan ban fa Dade da budeshi ba Amma yanzu da yake so ake ya bude yaki da zaku yarda sai ince muku babu komai aciki.............

"A a ranka ya Dade a dai bude don Rana tsaka aka tashe mu aikin Nan ..............
Ya Miko mishi key din motar

"Karbi to ka gwada kagani Ni dai na gaji gaskiya,
Dan sandan ya karbi key din ya soma kokarin gwada tashi sa ar inda ya turza sosai kafin yayi nasarar bude but din cikin sa a Kuma ya hango wani Abu me kama da jini na bin wani tsumma dake kudun dune yajawo shi ya warware inda yaga wani Abu me kama da hannun mutum inda kafar mutum ta fado Kuma wani Abu ya fado me kama da kokon Kan mutum

Eng AK ya zaro idanu Yana mamakin yadda wannan alamarin ke Shirin faruwa ta Yaya akayi wannan abin ya shigo motar shi

Inda Dan sandan yake kallon eng abdukarim da mamakin wannan abinda da ya samu acikin motar inda daga can baya Kuma cikin masu jiran go slow Kabir masi ya fito daga tashi motar ya karaso wurin inda shima yaga abinda ake mamakin gani amotar abdulkarim

"Wai abdulkarim Kaine da part din mutum a mota? Eh lallai da gaske kake har da tsafi kake hadawa shiyasa ka shiga gabana to Allah ya shirye ka ya fada Yana murmushi ya koma motar shi Yana kallo aka fidda motar eng abdukarim aka saka Mata key aka kulle shi Kuma aka wuce dashi sashen da zai bincike shi yayin da Yan sandan suka ci gaba da bincike motocin mutane

Da wata irin dariya Kabir ya SHIGA gida inda izzatu ta tarbeshi tana tambayar dariyar Nan ta lafiya ce?

"Ki tayani dariya don ya akan idona Dan banzan can AK ya shiga hannu shigar da ba zai taba fita a yanzu ba. Kai lallai na yabawa gambo mafiyas akan wannan aikin nashi Dole ne in mishi biya me kyau,

Izzatu ta kyalkyale da dariya tana fadin nasan gambo mafiyas ya fi da haka Amma ya akayi har hakan ta faru?

"Nima ban San yadda gambon ya shirya wannan makircin ba ya dai kirani ya fada min abinda Zan sanar da Jami an tsaro na Kuma fada musu sai gashi akan idona aka damke Dan banza da kafafun mutane har da hannu da kokon Kai
Amma Bari in Kira gambo mafiyas din yazo ya karbi kudin shi kuma inji yadda ya shirya wannan makircin
Ya dauko wayar shi ya Kira gambo ya ce yazo yanzu
Ai kuwa ba a rufe awa guda ba sai ga gambo mafiyas

Kabir ya daga mishi hannu alamar jinjina inda gambon ke murmushi
"Me gida kaga aiki ne Hala?
"Naga aiki gambo don akan idona aka damke Dan banza da kafafun mutane har da hannu da kokon Kai ya akayi ka shirya mishi hakan?

"Ai me gida na Dade ina binshi sannu ahankali har na samu sa ar ya bude but din na fakaici idon shi na saka mishi hannu da kafar shiyasa nace ka sanar da hukuma don ta fara binciken motocin ta yadda Za a kamashi kaga idan aka samu wannan abin a motar shi Dole za a shiga bincike kaga daga Nan sai sunan shi ya baci har ya Kai Babu me kallon shi bare sunan shi ya motsa

Izzatu da Kabir suka tafawa gambo mafiyas akan makircin shi Kabir kuwa ya bashi kudi masu yawa ya Kuma ce zai neme shi matukar wani zai yi mishi shigar sauri irin na ak to yanzu ne zai Kira shi don yayi mishi maganin shi da haka sukayi sallama gambo ya wuce Yana murna izzatu da Kabir ma suka wuni farin ciki sun jefa Rayuwar bawan Allah cikin garari....................
[5/22, 7:24 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 34*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

..........Bincike tamkar za a binciko yadda uwa tayi ciki har ta haife lamarin da yazo mishi da wani irin rudani har yakasa Gane inda mafita take bayan ta Allah

Yasha tambayoyi har na tashin hankali inda lamarin ya koma hannun C I D inda kuma suka rikeshi Wai sai sunyi bincike agidan shi

Wayarshi ma kasheta akayi don kar ya Kira wani ko wani ya kirashi,

Lubabatu da sukayi dashi ba zai wuce shida na maraice ba gashi har takwas da Rabi tayi mamakin abinda ya tsaidashi don ta San baya son yayi sallar magruba a waje
Ta jawo wayar ta ta doka mishi Kira Amma abin haushi matar Nan me zakin muryar tsiya na sanar da ita sai dai ta sake Kira lokaci na gaba yanzu Wai ba za a samu layin ba

Haka tayi ta jaraba Kiran wayar shi Amma ta kasa samun shi Dole ta hakura ba Kuma hakura tayi ba tunanin abinda ya tsaidashi da kuma Rashin samun wayar shi don tasan ba lafiya ba don ta San wayar shi Yana da caji

Ummita ta shigo Mami Ina Abba ya shige yau har yanzu Bai dawo ba?
"To Ni kuwa ina Zan sani ummita? Gaba na dai na faduwa don na fara tunanin ba lafiya ba............

"Mami bara na Kira wayarshi naji inda ya tsaya................
"Wayarshi Bata shiga na Kira na kasa samun shi Ubangiji yasa dai lafiya.

Hankali ya kasa kwanciya inda ummita tace zata Kira haj mama taji ko ta San inda abban ya shiga Amma lubabatu ta ce ta saurara tukuna
Sai dai har Sha dayan dare Babu wani Abu ko da na samun wayar shi ne Dole lubabatu ta Kira wayar haj Mama wadda har ta fara bacci ta jiyo karar waya ta farka tana tambayar lubabatu lafiya kuwa?

"Hajiya AK ne har yanzu Bai dawo ba Kuma duka layikan shi arufe shine ko ya fada Miki zaije wani wuri?
Chapter 17 · 0% Book details