← Book details Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 22

Sashe 13

Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dungo baiwar Allah ciwo yaki Jin magani duk Yan dabarunta na Shan magani Amma ciwo yaki inda ta siyar da Yan awakinta ta hada kudin da Basu Kai ko Rabin abinda ake nema ba ta nufi likitan ta Yi mishi bayani ya tausaya Mata matuka inda tace ya ajiye kudin hannunshi idan ta Nemo cikon zata zo ayi Mata aikin

Ya karbi kudin sukayi rubutu ya Kuma nemi address dinta ta kawo shi har gidanta inda yake ganin kokarin ta na son ta taimaki kanta da kaucewa roko da tumasanci sai yake Jin ko da cikon ne ma zaiyi Mata in ta kama don haka sai ya saurareta

Zaman gidan yayiwa ummita yawa inda ta nemi shiga makarantar koyon computer Kuma eng ya Goya Mata baya ta shiga inda take Jin ta rage kadaici

Sai ya zamo ta fannin shaharar aikin kwangila ya zarta Kabir mashi kashe arna don gudar da akace za a rokar mishi ma ba a bashi ba eng AK aka bawa ita , idan har baiyi kuskure ba kusan wata goma Sha daya kenan Rabon da ace mishi ga aikin kwangila don haka yake ganin eng ne yayi mishi shigar sauri abinda kuwa ba zai yarda dashi kenan ba

Izzatu da take ta durawa ak din ashar tace ya zamo Dole yaje ya samu ak ya yayi gargadin shi Akan ya Daina karbar kwangila sai dai ya Bari idan anyi a Yan mishi wani Abu
Ai kuwa ya sallamawa eng Wanda ya fito ya tarbeshi suka gaisa inda ya fito mishi ta hanyar siyasa

"Eng nazo ne inji adadin kwangilar da akace za a bani Amma shiru har yanzu sai ji nayi Wai an baka kayi ta harma ka Dora da wasu shine abin ya bani mamaki.

"Kwarai kuwa me gida nayi ta har ma na dora da wasu guda biyu Wanda nakeyi yanzu. Amma banji Dadin tada maka alkawari da akayi ba. Sai dai Zan baka shawara ka nemi dalili idan na kuskure ne sai agyara shi don gaba don yanzu haka akarshen shekara za a gabatar da wasu manyan kwangilolin har biyar kaga idan ka nuna bakaji dadin alkawarin da aka tada maka ba to Ina me tabbatar maka da acikin wadan can biyar din za a baka wasu inaga hakan ya dace kayi.

"Kwarai kuwa eng ka kawo shawara na Kuma gode da haka sukayi sallama ya dawo gida Yana fadawa izzatu yadda sukayi........

"Rainin hankali ne kawai yake son shigo maka dashi ta Yaya zakaja kunnen gwamnati indai ba salon Dan sauran girmanka ya zubeba?

Idan har irin wannan ta Kuma faruwa nagane shi ke son talauta ka to Zan sako gambo mafiyas atafiyar don in ba koya mishi hankali akayi ba to munaji muna gani sai ruwa ma ya gagare mu

Kabir yayi na am da hakan inda suka ci gaba da zaman jiran saurare Amma shiru tamkar bawa ya leka garin su..............
[5/19, 7:15 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*page 25*
*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

.........."Kai Nan har Dan iska ne Kai da zaka saka shimfideden hannunka ka marar min yariya? Dama ina jiranka akan wulakancin da kayi Mata har sau uku saboda Kai Dan iska ne? Waye ubanka a duk fadin Nigeria? To zaka Gane karyar iskanci kake don sai ka Kare Rayuwar ka agidan maza. Kasan ko wacece ita da irin gatan dake gareta ? To bude kunnen ka kaji da ranta ya baci gara gara amaimsita yakin badar da tabuka ita kadai ce gayya zakuma ka Gane gatanta ya zarce ayi Mata ko harara bare kallon banza

Izzatu tayi ta sababi da masifa tana wanke shi soso da sabulu Amma ko daga Kai baiyi ba bare ya tanka inda izzatu ta fiddo wayar ta ta Kira D P O na yankin ta sanar dashi tana son aturo Mata motar Yan sanda biyu suzo su wuce Mata da wani Dan iska da take son abatar dashi gaba daya

Ta gama wayar tana mishi kallon banza inda ta dubi motar shi ta dora da sababi

"Dan iska da Kai ka aro mota ka shigo gari shine zaka nemi shiga hurumin yarinyata shege da ganinka ma kayi Kama da masu wankin mota wata Kil wanki aka kawo maka shine ka shigo gari don kayi bagu da barazana da motar mutane don da ganinka matsiyacine Kai zaka Gane ka tabo abinda yafi karfin ka har iyayen ka sai an kulle min su tunda Basu iya tarbiya ba......

Baice Mata komai ba har tagama cinye fuskar shi tas inda Kuma motocin na Yan sanda suka faka har mota uku cike da Yan sanda tamkar zasu Kama Yan fashi

"Kunga shegen Nan ku Kama min shi cewar izzatu inda taga kaf din Yan sandan sun wuce wurin Wanda take cewa su Kama Amma me? Sai gani tayi suna kamewa da sarawa abinda ya bawa izzatu haushi.........

"Ku Kama min shege ku aje sai Naga ko uban waye yake daure mishi kugu..........

D P O ya dako Mata tsawa wadda Bata San ko ta wacece ba inda suke ta bawa Anwar hakuri suna sarawa abinda ya daurewa izzatu Kai Bata Sha mamaki ba sai da taji Anwar din na bada umarnin Kama ta ita da fulani kawai sai gani tayi suyo musu zummuwa

Aka garkama musu ankwa ana iza keyar su SHIGA motar Yan sandar........

"Kafin ku wuce dasu kusa yarinyar tazo ta janye motar can Kuma kar abada belin su sai in Ni Naga damar hakan Kuma don yanzu kar a kirani sai Nan da bayan wata uku don inaso uwar da Yar su koyi darasi. Ita Yar Ina so ta koyi tarbiya ita Kuma uwar don idan ta sake haifar wani dan Nan gaba ta San irin tarbiyar da zata bashi

Aka dakowa fulani tsawa ta fito jiki na rawa ta janye motar ta koma cikin motar Yan sanda akaja su aka wuce dasu inda izzatu ke kallon lamarin kamar wani mafarki ko Shirin film Wai ka dauko Dan sanda ya kama maka mutum Amma sai lamarin ya juye akanka waye wannan yaron da taga Yan sandan ma kamar tsoron shi sukeji? Da sauri ta jawo wayar ta ta Kira Kabir take fada mishi abinda ya faru inda isar su station din ko minti Sha biyar ba ayi ba Kabir mashi kashe arna ya iso don yayi belin iyalan nashi

Azaton shi ficen da yayi da sharar da kowa ya sanshi yasa yayi zaton da yazo ne za a bashi belin su izzatu Amma sai ya iske sabon Labari Wai babu batun beli sai Nan da wata uku

Yayi mamakin wannan yaro da izzatu ta fada mishi to waye? Da ya nemi sanin yaron da yayi wannan aikin D P O ya sanar dashi Anwar ne,

Mamaki ya Kama Kabir Jin Wai Anwar ne to Ina suka hadun da fulanin har sukayi wannan wautar? Da haka yayi sallama da caji ofis din ya nufi me bawa shugaban kasa shawara don ya zamo tsanin shi na ganin Mr President don ya San shi kadai ne zai saka Baki Anwar din ya fito mishi da iyalin shi don haka ya tunkari Alh uba Dan yaro Wanda ya sanar dashi abinda ya faru tsakanin yarshi da Anwar Wanda ya bada umarnin kulle su har sai bayan watannin uku shine yake son Isa wurin Mr President don asaka Baki Anwar ya hakura

Ai kuwa alh uba Dan yaro yayi mishi jagora har sukayi nasarar gani Mr President Kabir ya zayyane mishi komai inda yayi murmushi Yana cewa

"Yara ne su duka Kuma suna takama da zafin Kai kayi hakuri Kabir don Allah bansani ba Amma yanzu Nan zai zo Nan inji abinda yasa yayi hakan ya fada Yana dauko wayar shi ya latso lambar Anwar Kara biyu ya dauka inda uban yace yazo yanzu Yana son magana dashi ya amsa da gashi Nan zuwa ya aje wayar

Ya dubi Kabir "Kabir fatan ba zanyi maka shisshigi ba idan na tambaye ka bakayiwa Yar tamu miji ba? Ya amsa da baiyi Mata miji ba inda Mr President yace zaiso su hada Anwar da ita fulanin aure don wata Kil wannan tsamar tasu salon tasu soyayyar ne.

Wani Dadi da ya rufe Kabir tamkar ya shide don Yana ganin auren fulani zai zamo mishi auren jari da yadda zai dawo da kwangilolin shi da ake son yi mishi fin karfi don haka jiki na rawa ya amsa da Babu matsala duk yadda Mr President ke so hakan za ayi daga karshe ma yace ya bawa Anwar din auren fulanin idan an shirya azo ayi magana

Mr President yaji Dadi sosai dama Yana neman Yar da zai hada da Anwar tunda shi har yanzu cewa yake Wai baiga wadda tayi mishi ba don haka ya zabi yi mishi haka don baya son yaron nashi ya bude Tasha shiyasa yake son yi mishi aure

Mr President ya kawo kyautar girma ya bada yace akaiwa fulani ta siyi kayan kwalliya abind ya gigita Kabir mashi shi Kam zai iya cewa gara da akayi da haka Anwar yayi sallama ya shigo ya zube Yana gaishe da Kabir mashi don ya sanshi sosai Yana ganinshi agidan nasu sai dai har ga Allah Bai zaci shine uban yarinyar da tayi mishi gatsali ba. Mr President ya tambayeshi
"Su waye kasa aka kulle a station? Ya fada mishi duk yadda abin ya faro har zuwan izzatu da irin tozarcin da tayi mishi duk ya fada musu inda Mr President yayi murmushi

"To kanwar ka da uwarka kasa aka kulle don iyalan Kabir ne sai kaje maza kasa asake su............

Yazube gaban Kabir Yana bashi hakuri
"Kayi hakuri Abba ban sani ba ne ka gafarce Ni yanzu ne zansa akansu har gida.............
[5/19, 4:36 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 27*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*
Chapter 13 · 0% Book details