← Book details Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 22

Sashe 6

Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mutumin da ta tsayar me abin hannun shi ne irin Yan bokon Nan Wanda duniya ke fadawa karya Wanda suke dadewa Basuyi aure ba saboda tsara Rayuwa da suke ai kuwa aka daura auren ta tare agidan shi

Babu abinda ya sauya daga halinta sai ma abinda yayi gaba na wulakanta ma aikata da son dagawa da fangima . daular dake gidan Kabir mashi ta zarce ta gidan ak don shima Dan kwangila ne me zaman kanshi don shima Yana da communication da fadar shugaban kasa wurin karbar kwangila

Hakan yasa ta ga ya Zama dole ta dakushe kaifin irin wancan garnakakin irin na gidan ak don ba zata yarda tarihi ya maimaita kanshi ba Dole ne ta samawa kanta mafita akan samun magaji agidan Kabir don haka ta lalubo lambar sister mero wata malamar Asibiti dake taimakon ta a lokacin da ta nemi maganin Hana daukar ciki

Kara biyu sister mero ta daga wayar bayan sun gaisa take tambayar tana Asibiti? Ta amsa Bata Asibiti yanzu sai dai ko zuwa gobe su hadu a asibitin kawai don azaton sister mero maganin da ta Saba karba ne zata karba da haka sukayi sallama ta aje wayar inda take tunanin idan Bata yi kokarin samun Wanda zai gaji dukiyar Kabir ba idan ya kauce ai ta tabbata me asara to ba ma zata yarda tarihi ya maimaita kanshi ba daga gidan Kabir ta gama matsawa wani wurin don ta hadu da matsalar dangin miji ba Kuma zata yarda Rashin haihuwa ya Kara kawo Mata wani tarnaki ba don haka ta Matsu garin ya waye ta iske mero don taji yadda zasu faro da yadda zasu Kare

Washe gari kuwa ta gillawa Kabir karyar cewa Bata da lafiya zata je Asibiti inda ya cika Mata Jakarta da kudi ta ja motar da Kabir ya siya Mata ta wuce Asibitin national hospital dake garin Abuja don ganawa da sister mero.....

Bari muji yadda wannan ganawa zata Kaya tsakanin izzatu da sister mero
[5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 13*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

...........Sister mero ta zakuda tamkar wadda kunama ta sakarwa harbi jin izzatu na ambato Mata milyon goma

"Banji me kikace ba izzatu
"Yadda kikaji hakan nake nufi milyon goma na ce Zan Baki idan har aikinki ya tafi daidai.....

"Wane irin aikine zanyi Miki ki bani wannan kudin? Don Allah karki yaudare Ni izzatu ko cikin mafarki ban taba ganin milyon goma ba ......
"Zaki gansu ido biyu harma su zamo naki idan kinyi nasarar kammala aikin ki Babu kuskure ko sabani........
"To naji wane irin aikine kike ta fada haka? Fada min don Allah tun zuciya ta Bata buga ba.

Izzatu ta dubeta tayi shiru kafin tace
"So nake mu hada wata kwangila dake kwangilar da zata danka Miki milyon goma ahannu.....

"Wace irin kwangila Ni ki fito amutum kiyi min magana ba alaye da kwane kwane ba.

"Da ko Diya nake so ki samo min acikin karbar haihuwar da kike Ni Kuma Zan sanar inada ciki Wanda Dan da Zaki kawo min shine Zan batar da hankalin mutane Kan cewa nice na haifa.........

"Dakata Allah idan na fahimce ki wata ta dauki cikin ta haife sai in dauko in kawo Miki?
"Hakan nake nufi.
"To tashi ki Kai kudin ki gaban da Kika San fin dubu zasu yi Miki Ni dai Kam albarka ban siyar ba.
"Haba wannan ma ai Rainin hankali ne da son ki wulakanta min aiki kija akore Ni
Haka kawai wata zatayi wahalar daukar ciki da rainon shi ta Kuma ketare hadarin na kuda ta haifa saboda son zuciya sai in sato in kawo Miki don Allah meye sunana idan nayi Miki hakan? Yaya zakiji idan ke akayiwa hakan? To mu rufe wannan maganar muyi wata

Izzatu ta dubeta asheke
"Dama fa ALHERI bai Faye karbar bakin mutum ba Amma ki sani kudin da kike kokarin yiwa arziki kullin da zai tarwatse har ki mutu ba Zaki taba mallakar su ba tunda Kuma ba Zaki iya ba zanje birnin gaba inda za ayi min
Tana gama fadin haka ta Suri Jakarta ta fice tamkar kububuwa inda sister mero ta bita da kallo inda Kuma take Jin wani lissafin me kama da na dokin Rano ya sauko Mata akan bukatunta na son ta mallaki mota da son ta siyi gida Amma ta Yaya zata mallaki gidan da motar alhalin albashin ta ma kafin ta karbe shi bukatu sun targada shi? Amma Kuma ta Yaya zata iya wannan aiki me matukar hadari akanta da aikinta? Sannan Kuma Yaya zatayi da hakki da alhakin wadda zata sibarewa Dan?

Ance mugun tunani shi ke abotakar shaidan sai sister mero ta ture wancen kalubalen ta hango bukatar ta inda tayi na am da aikin da zai mallaka Mata milyon goma wannan ai shine yiwa arziki kulli yaushe ne? Yaushe ne zata hada Kan wadan can kudin a wannan Nigeriar me jiya tafi yau gobe tafi jibi.

Don haka tana tashi aiki sai ta Kira wayar izzatu ta nemi kwatancen gidanta......

"Me ye na neman kwatancen gidana Kuma? In ma shawara Kika sauya kin makara don Ni magana guda nake bana maimaici.....
"Yi hakuri fada min inzo muyi magana
Izzatu taja tsaki kafin ta Bata kwatancen
Mero ta iso gidan Wanda ita da kanta ta San lallai Dole izzatu ke rudewa da son samun mafita

Ta dubeta awatse
"Meye Kuma na biyoni gida?
"Kiyi hakuri shawara nayi Naga Bai kamata ace kizo da bukatar ki wurina ba in watsa Miki kasa a ido haka na yarda sai mu tsara yadda abun zai kasance.

"Me yasa shi matsiyaci ko ya shiga tandun Mai yake fitowa kandas?
Yaushe ne mero Zaki Tara milyon goma?
Meye abin wuya acikin aikina?
Wannan magana tayiwa mero zafi Amma ta hadiye

"Ni dai yanzu muyi magana Yaya abin zai kasance?
"Zan sanar da Kabir nazo Asibiti ance inada ciki Zan dauki acting din masu ciki ke Kuma ba ki Nan da wata bakwai ko takwas kiyi kokarin kawo min abinda yasamu namiji ko mace duk Wanda ya samu Ina so

"To shikenan zanyi kokarin hakan in Sha Allah sai dai maganar kudin Zaki fara bani wani Abu ne kafin cikar aikin ?

"Kare ya cijeni ne mero da zan Baki kudi Baki gama aiki ba?
Ranar da duk Kika gama aikin ki Ina me tabbatar Miki da ko minti ba za a Kara ba Zan biya ki kudin ki cash

Da haka sukayi sallama da mero ta fice daga gidan inda Kuma a wannan Rana lamarin ya soma Wanda ya kunshi wani KWAI da fasuwar shi zai tafi da Ruhin Al umma da yawa.

Kabir ya dawo inda izzatu ke sanar dashi taje Asibiti an sanar da ita cikine da ita inda yayi murna tamkar ya mayar da ita cikin shi inda ita Kuma ta soma fito da salo kala kala inda Kuma izzatu ke baza izza inda Kuma akayi sa a Kabir Bai Faye bawa uwarshi muhimmanci ba inda izzatu ta Kara baza komar wulakanta uwar Kabir din wadda Allah ya zubawa tsananin hakuri da alkunya inda a yau ta nuko gari tundaga birnin Zaria ta iso gidan Dan nata don ta ga shi saboda shi dai yakan iya share shekara Bai lekota ba bare ya agaza Mata duk kudin shi da shaharar shi Bai bada Kai ga lamarin mahaifiyar shi ba inda Ni Kam gidan iko nace anyi asara kuwa indai haka ne...........
[5/16, 5:54 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 12*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

..........Ta faka motar me kololuwar daraja a farfajiyar Asibitin national hospital dake babban birnin tarayya Abuja inda ta fito fuskarta sanye da Derk spes ta soma takawa sannu ahankali tamkar me tausayin kasa hannunta sabe da jakar LV kafar ta sanye da takalmin LV mahadin jakar sai wani matsiyacin leshe Wanda ya lashe kudi ba kadan ba kamshin turaren ta ya bulale wurin ta kara daukar kanta yayin da ta ga wasu manyan Mata suna binta da kallo don gaskiyar magana shigarta Babu karya don ta samu Kabir mashi yadda take so Kuma ya rike Mata Kan macijin inda har take Jin kanta ame jinin arziki
Ta iso ofis din sister mero wadda aiki yayiwa sauki suka gaisa inda meron ke kallon ta cikin Sha awa

"Jiya kin Kira bana Asibiti naje gwarunfa duba wata abokiyar aikina da bataji Dadi ba Ina fatan dai ba kwayar pills din da Kika Saba karba Zaki karba don gaskiya lokaci yayi da ya kamata ace kin haihu ai kin Sha Miya haka Nan,

"Uhum mero ai ba Zan kuma yarda insha wani Abu yanzu da sunan Hana daukar ciki don nayi nadama ba kadan ba......

"Gara dai Kam don abin in ya kazanta Babu kyau. To yanzu me za ayi Miki?
Ta sauke ajiyar zuciya

"Mero na rabu da mijina sanadin Rashin haihuwa inda ayanzu nayi wani auren Wanda bana fatan sake gamuwa da wani tarnakin irin na gidan AK shine nake son samun mafita daga gareki.....
Mero ta tareta
"Kin samu matsala ne halan?
"Na samu matsala kuwa gagaruma wadda silar Shan maganin Hana daukar ciki ya haifar min har na samu bakin sakamakon ba Zan haihu ba shine nake gudun haduwa da irin waccan matsalar ta gidan AK shine nake so ki taimakeni da mafita.

Sister mero ta sauke ajiyar zuciya
"Gaskiya izzatu Babu wani taimakon da Zan iya yi Miki illa ki rungumi kaddara Kuma hakan ya zamo izna da Jan kunne gareki da masu irin abinda kikayi
Shi Allah ba ayi mishi Dole ana yin tsari Amma sai an fara haihuwa anga yadda haihuwar ta faro misali yinta Kai da Kai ko Kuma inke da mijinki zaku iya haifar me cutar sikila idan kunyi tsari ba laifi bane don ku hutar da yaran daga wahala Amma da yawan ku Kuna SHIGA hurumin Ubangiji da son kuci gyaran wahayi........
Chapter 6 · 0% Book details