← Book details Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 22

Sashe 4

Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dubeta cikin sanyin murya "me ya farune izzatu",?
"So nake ka tashi ka sallame Ni don na gaji gaskiya ba Zan Kare a auren da Babu tsiyar da zai tsinana min ba........
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 7*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

......... Ya share ruwan dake yarari akan fuskar shi Yana murmushi Yana kallonta

"Izzatu Allah ya sani Ina Jin tausayin ki Zan Kuma Kara hadaki da Allah da manzon sa ki bar maganar Nan haka......

"Kar ka Kuma Jin tausayi na Kai ne abin tausayi ba Ni ba don Ni na hango mafitata a mafarki don haka sallame Ni kawai in Kama gabana.
Yayi murmushi "Abinda Kika gani a mafarki ba lallai ya zamo gaske ba sai dai nuni ko izna don Allah kiyi hakuri ki barni nayi barci na kaina ciwo yake,

Ya kwanta ya barta tana jijjigar jiki idonta fal masifa ta fito tana sababi inda ta iske tsohuwa talai zaune tana Gyan gyadi sai kawai ta shara Mata Mari
Abin tausayi tsohuwar ta farka afirgice
"Wane irin dabban cine ki share wuri ki zauna kina min bacci da tsakar Rana?
Ke Bari fa kiji in fada Miki idan kinji kin gaji da aikin Nan babu lallai Babu tilas na gaji da gayyar hakora in kin gaji sai na sallame ki
Ta shiga zubar da ruwan tijara inda tsohuwa talai hawaye ya tararo Mata tana ta ahi da neman afuwa

Jin Marin da izzatu tayi wa talai yasa ak fitowa ya na kallon yadda take Mata tijara ranshi ya baci matuka gaya don Allah yasaka mishi son tsohuwa talai don asali talai wurin hajiya Mama take aiki shine ya matsa da sai tsohuwa talai ta dawo gidan shi don ya Saba da abincin ta tun da sauran karfinta tayi aiki a gidan su shine mafarin tsanar da izzatu tayi Mata saboda tana ganin an turo tsohuwar ne don ta saka Mata ido ko da take wulakanta masu aiki tafi wulakanta Talai

Ya karaso wurin ya kamo hannunta ya tada ita inda yaga hawaye na bin idonta
"Kiyi hakuri talai Ni naji Miki Amma ban San haka kike muskanta ba .
Ya dubi izzatu cikin wani irin fushi da Bata taba gani afuskar shi ba

"Baki ji kunyar cire hannu ki Mari tsohuwa irin haka kamar talai ba? To ya zamo na karshe da Zaki Kuma yiwa wani ma aikaci a gidan Nan bare talai. Talai kamar Uwata ce daga yau kar ki Kuma sakata ko shara bare wani aiki na soke Mata duk wani aiki sai dai agirka abata......

"Wannan ne Kuma baka Isa ba wallahi muddin Ina gidan Nan to Dole ne tayi aiki ba tsufa ba ko mu kwana lafiya ce . Dama na Dade da ganota tsohuwar muna fukace wadda aka turo don tazo ta saka min ido to aiki ya Zama Dole tayi shi ko Kuma jikinta ya Bata Labari wallahi salon kasa ta kalli kanta a wata tsiya kace sai dai agirka abata ita a way?

Bai San lokacin da ya faska Mata Marin ba karon farko a tarihin Rayuwar auren su da ya taba Kai hannu jikinta da sunan duka abinda bai taba yi ba.

"Ba Zan taba Bari ki wulakanta tsohuwar da Ni ne na kawo ta gida na ba
Akan talai ba sai kin roki saki ba Zan Baki shi jahilar banza wadda Bata San kimar tsoho ba. Idan har ka girmama tsohon wani to naka ka martaba don hak sai ki kiyaye ba Zan lamunci wulakanta mutanen dake kasanki ba......

Ta cakumo kwalar rigar shi ta tattare ahannun ta "Tunda har ka mareni akan wannan tsohuwar banzar ai kasan ta ballowa kanka aikin da ba zaka iya dashi in yaso sai ka auri talai ko hajiya mama.......

Ya Kuma Bata kyakkyawan marika guda biyu ajere Wanda yasa taga wata koriyar walkiya
Ya Kira duka ma aikatan gidan inda yace kar akuma saka tsohuwa talai aikin komai Koda dibar ruwa ne wankin kayan ta ma arika hadawa ana kaiwa shago a wanko
Haka Kuma duk Wanda izzatu ta Kuma ciwa fuska ko wulakanci to ya fada mishi tunda ga wannan Rana tsohuwa talai ta samu cikakken yanci inda Kuma izzatu ta fice daga gida ta nufi nasu da sunan tagama auren dama sanadi take nema ta Kuma samu sai dai acan gidan Basu Bata samu goyon baya ba inda aka tuso keyar ta aka dawo da ita aka Kuma bawa ak hakuri inda ita Kuma take Jin ta gama auren shi Koda shi Daya yayi saura aduniya sai sun rabu inda Kuma ta fito da sabon salo na aunawa hajiya Mama da duk wani nashi zagi abinda yake Jin ba zai daukaba

Tsawon sati biyu tana gurza mishi Rashin mutunci Yana dauke Kai inda washe gari sai ga hajiya mama da tarin magunguna ta diro gidan..........
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 8*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*___________________________________*

...........Hajiya Mama ta shigo gidan tana sallama inda izzatu ke zaune tana chatt a wayarta ta dago kanta ta dubi hajiyar ba tare da ta amsa sallamar ta ba ta maida kanta ga wayarta taci gaba da chat dinta
Hajiyar ta karaso ta zauna tana kallon izzatu da ta baiwa banza ajiyar ta.
Tayi murmushi kafin tace
"Ga maganin Nan ki ajewa abdukarim da Zuma ake Sha safe da maraice. Bata karba ba kamar yadda Bata nuna ta San da zaman hajiyar a wurin ba
Talai da taji zuwan hajiyar ta karaso tana gaishe ta

"Yauwa talai ga magani Nan ki ajewa abdukarim kice mishi sau biyu ake Sha safe da maraice Kuma da Zuma ake Sha
Talai ta karba tana fadin insha Allah ba Zan manta ba hajiya

Hajiyar ta Mike da Shirin ficewa inda talai tace
"Hajiya ki tsaya ko ruwa Kisha Mana bare ki huta.....
"Tunda gidan gyatumin tazo sai ki Bata ruwa gwana yar ka iya , cewar izzatu wadda ke wurgo musu harara

"Ni in nagane mutum munafiki ne me zai hada Ni dashi da munafurcin sa? Wallahi a yanzu dai dai nake da anuna min yatsa na karya tunda tafiyar Babu mutunci

Hajiya Mama ta Kada kanta "Allah ya shiryeki ya dawo dake hanya.....
"Ameen in dagaske kike duk da kema kina bukatar shiriyar tsohuwar banza me bibiyar Matan ya'yan ta......

Kalmar tsohuwar banza ta fado akunne AK dake shigowa gidan wani Abu ya naushi kahon zuciyar shi ya dubi hajiya ya Kuma dubi talai da ta soke Kai kasa Yana son ya gano wadda izzatu ke jifa da kalmar tsohuwar banza amma ya kasa ganowa

"Yanzu kike tafe hajiya? Yayi karfin halin tambaya
"Yanzu nazo har Zan wuce dama magani na kawo maka gashi Nan wurin talai tayi maka bayani.
Wannan saurin na hajiya shi ya alam ta mishi zagin tsohuwar banza da izzatu tayi ba da kowa take ba sai hajiya mama.

Ya riko hannun hajiyar Yana fadin "hajiya don Allah me ya faru kike sauri haka?
"Babu abinda ya faru ak Zan koma gida ne kawai ka tabbatar kayi amfani da maganin da na kawo maka....
"Ina fatan hajiya ba ke ko talai take Kira da tsohuwar banza ba?
"To wacece Ni da ba za a zageni ba ......

Kafin ma hajiya ta dire zancen ta ya Cabo izzatu ya soma wanketa da maruka
"Ayau Zan nuna Miki hajiya tafi karfin komai agareni Ina tausaya Miki Amma da yake jaka ce Baki San ana tausayin ki kije na sakek........

"Kar ka fara abdulkarim !
Hajiya ta katse shi da tsawa.
"Ka rabu da ita Kai dai kayi ta hakuri.....

"Ai dama da wannan manufar kikazo bakar munafuka annamimiya kin Kuma ci nasara don Ina me tabbatar Miki da yau wallahi aurena da abdulkarim ba zai Kuma kwana a duniya ba sai ya sakeni don in Kara gaba ko Zan haihu.

Ta dubi ak "Idan dai Kai din Dan halak ne cikin wannan tsohuwar banzar da wancen tsohon banzan na kushewa ka sakeni saki uku....

Kafin ma ta dire zancen ya furta Mata kalmar sakin
"Idan akwai sakin da ya wuce a lissafa shi fiye da uku to nayi Miki shi kije kije kije bana bukatar ganin bakar fuskar ki Arayuwa ta Ina fatan hakan zai tabbatar Miki Ni din Dan halak......

Ta dubeshi ta watsar
"Sai ka auro hajiya Mama kasaka dakin da Zan bari.......
Bata rufe Baki ba ya rufeta da duka sai da hajiya ta yi mishi tsawa kafin ya saurara Mata inda tafice aguje don ta tabbatar ba cikin hankalin shi yake ba

"Baka kyauta min ba abdulkarim me zaisa ka biye Mata ?
Zagi ai baya Kari don ta zageni sai menene?
Naso ka lallaba matar ka kuyi zaman ku har Allah ya warware maka lalurar ka don ba kowace mace bace zata hakura da Rashin haihuwa shi yasa kaga Nima nake lallabata

"Hajiya na gaji da halin matar Nan Kuma ba ayi wata mace da zata zageki ba in kyale ta ko Ruhin mu hade yake wallahi na gwammace in mutu da dai in Bari wani ya muzanta min ke bare izzatu dake home da barazana cikin rizgar arzina. Kuma Bari in fada Miki gaskiya hajiya da dai nayi nufin yin shiru har muddin Rayuwa akan matsalar Rashin haihuwa hajiya Ni lafiya ta kalau itace me matsalar ba Ni ba.............
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 9*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

........Hajiya Mama ta dubeshi azabure Jin Yana fadin ba shine me matsalar ba izzatu ce.
"Dama lafiyar ka kalau abdulkarim Amma kaja Baki ka tsuke? Lallai na sarawa hakurin ka ka Kuma yi halacci Amma anyi maka butulci.
"Tun tsawon wane lokaci ne kasan hakan?
Chapter 4 · 0% Book details