← Book details Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 22

Sashe 1

Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 1*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*

*_Da sunan Allah me Rahama da jinkai ina godiya ga Ubangiji da ya yarda Zan fara sabon littafi na me suna ZAN FASA KWAI Ubangiji ka tsareni rubuta abinda ya kauce da tuntuben alkalami kasa ya zamo wa azi da izna_*

*Gaisuwa ga masoyan GIDAN IKO na kusa da na nesa Ina gaishe ku*

*_Sai Uwata haj Saliha abubkar abdllh Zaria gaisuwar ta muddin Rayuwa ce Allah ya dafa_*

"Talai Wai Ina Talai ta shige don tsohon wulakanci ta barni ina ta yage bakin kiranta?
Tsohuwar ta taho da sauri tamkar zata kifa saboda Jin Kiran uwar gijiyar ta akalla tsohuwar zata haurawa shekaru sittin koma fiye ta taho da sauri har tana cin tuntube kadan ya rage taci da kasa.

Ta wurgo Mata harara lokacin da take zubewa agabanta.
"Gani hajiya kiyi hakuri Ina bandaki naji kina Kira tun jiya Wallahi ciki ke murda min sai faman zagayawa nake......
"Ai nayi Zaton samun wuri ne yasa Kika fara nuna min kinaji Ina kwakwazon kiranki kikayi min kunnen uwar shegu dama ba Dole ciki ke rude Miki ba komai Kika samu wawab kin abkawa ciki sai kace jaka? Wani Abu ya daki zuciyar tsohuwa talai Jin Wai yau ita take Kira da jaka Amma ya ta iya tunda Ubangiji ya zano abincinta akar Kashin wannan Mata me masifar izza wadda ko saboda izzar tata ne ma aka rada Mata suna da izzatu? Ta katseta da wata tsawa tamkar zata fasa Mata dodon kunnen

"Da Allah Ni tashi ki Kai min jakata mota Kika sakani gaba kamar kin samu wata TV"
Tsohuwar ta Mike da azama ta dauki jakar ta hannu wadda Isa da izza ke Hana Mata dauka Wai sai an Kai Mata duk in zata fita.

Tabi bayan tsohuwar tana sababi inda tsohuwar kamar zata fashe da kuka saboda Jin abinda ake fada Mata ba Diya ba jika ma tayi da ita Amma saboda kawai tana Yar aiki sai ake sauke Mata kowane kalar wulakanci tamkar ita ta kawo talauci duniya.

Ta bude mota ta saka Mata jakar ta juyo zata dawo ciki inda ta maido ta. "Na sallame ki ne kike kokarin juyawa? Wai talai me kike daukar kanki ne a gidan Nan? Akwai gadon tsohonki aciki ne? Tsohuwar ta rusuna tana Bata hakuri

"Nace akwai gadon tsohonki aciki? "A a Babu hajiya na tuba ki yafe Ni nayi Zaton kin sallame Ni ne Amma ba Zan sake ba .
Ta wurgo Mata harara
"Idan na dawo na samu wankin tile din Bai fita ba sai kin sauya shi wallahi duk wata sai an biyaki kudinki Amma saboda kin kware a ha inci wankin tile ma sai kinyi cuta
"Zan kiyaye hajiya adawo lafiya
Taja tsaki taja motar ta fice tana sababi

Tsohuwa talai ta juyo ta soma aikin wankin tile tamkar zata sabunto shi yadda ya faro har dai ta tabbatar ya fita kafin ta Kama wankin kayan hajiyar inda Kuma ciwon cikin da tayi magana ya kayar da ita abin tausayi tsohuwar amai da gudawa ya sarketa ta Fadi Kan shinfida tana kwara amai zawayi na bin shimfidar inda harira ta me aikin girka abinci ta kawo Mata agaji da Dan ruwan gishiri ta Kuma tsabtace tsohuwar cikin ikon Rabbi Kuma amai da zawayin ya tsaya sai dai ta kwantsame Abu ga tsoho amai da zawayi ba Dadi

Sai San maraice hajiyar ta dawo inda ta iske talai akwance Babu lafiya Amma sai me? Sai sababi da masifa Wai lambone musamman da taga wankin da talai din ta fara ciwo ya kaita kasa Aiko ta SHIGA zubar da ruwan tijara Wai akan Dole sai talai ta taso ta wanke Mata kayanta

Harira ta kalleta "kiyi hakuri hajiya wallahi Bata da lafiya kwance ta wuni amai da gudawa ke damunta Bari Ni na karasa wankewa......
Ta zabgowa harira wata ashar
"Na tambaye kine gwana yar ka iya? Kauce daga Nan ko yanzu ranki yayi Baki Yar iska me shiga shirgin wani....

Tsohuwa talai ta taso tana daura Dan kwalinta ta fito dai dai da shigowar hajiya Mama uwar me gidan wadda tazamo dodan izzatu saboda masifarta

Tsohuwa talai ta Yi Mata barka da zuwa inda izzatu ta Sha jinin jikinta
Hajiya Mama ta amsa inda take duban talai.
"Baki da lafiya ne talai? Wallahi kuwa hajiya amai da gudawa ne....
Ta dubi izzatu fuska ahade tasoma zazaga masifa...

"Kuma shine saboda Rashin sanin kimar Dan Adam bakiyi tunanin kaita Asibiti ba saboda ba uwar ki bace? Ke Wai wace irin Yar iskace ne ? Maza ki sa akaita Asibiti ko ruwa akara Mata me aiki Ba baiwa bace sun taimake ki ba kadan ba tunda ke agidan ku Basu koya Miki komai ba

"Kiyi hakuri hajiya Bari asa akaita ko kyamis ne.....
"Asibiti za akaita ke in kinji naki ciwon kyamis kike zuwa? Talai tace hajiya ai naji sauki ma ba sai munje ba.....

"A a talai kuje ko ruwa akara Miki Baki ga yadda Kika kwaltse ba? Haka ko akayi direba ya dauki talai zuwa Asibiti inda aka Kara Mata ruwa da magunguna suka dawo gida Inda hajiya Mama ta balle hancin tsiyar da ya kawo ta gidan Dan nata

"Ina da labarin duk irin cin Kashin da kikewa masu aiki izzatu kin mace ko wacece ke? Don me Zaki samu mutane kiyi ta cin zarafin su don kawai suna muku aiki? To Bari kiji abinda ya kawo Ni gidan nan yau shekarar ki goma Sha biyu Nan gidan Amma ko batan wata bakiyi ba to na gaji da gafara sa Banga kaho ba a yau nazo da magana wadda zanyi akan ke da mijinki don haka maza ki Kira min shi yazo yanzu Ina jiran shi..........
[5/16, 5:52 AM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 2*

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*________________________________*

..Hawaye ya tararowa izzatu Jin abinda hajiya Mama ke Fadi wata zuciya ta kuleta taji kamar ta tashi ta rufe hajiyar da duka sai dai Babu hali hajiyar zaune take da kuturinta.

"Kukan banza ne kike kukan wofi. Yanzu Nan daga gidan saminu nake Ina shiga yara suka taho suna min oyoyo abin farin ciki duk inda na waiga Yan dugwi dugwi ne ke hawa da sauka ajikina shi wannan haka zai lalace akan ki ba zaiyo aure ba ? To maza ki Kira min shi kice Ina jiranshi...

Ta wurgowa hajiyar harara kafin ta bude Baki cikin gadara da izza ta fara magana

"Hakan da kikayi yayi kyau hajiya ku sama mishi mafitar da zata bulle dashi don nagaji Nima magana ce kawai banyi ba to tunda har Anzo inda Kika gaji hajiya zanso ayau koma yanzu ki tsinke igiyoyin aurena sai ki kawo mishi wadda zata Rika haihuwa duk wata .......

Hajiyar ta dago Mata hannu "kar ki sake ki zageni don na Fadi gaskiya.....
"Ba Zan zageki ba hajiya Amma Nima ba Zan yarda ki fada min maganar da zata dameni ba kija bakin Ni Kuma Zan fassara Miki kowane kalar ciwo Zan fada Miki kalar maganin tunda na kula shekawa jaki shayi aikin banza ne ba iya Sha zaiyi ba....

"Ki Fadi komai damar kice Amma na rantse Miki sai an kawo wata mace agidan Nan wadda zata haifa Mana yara wallahi na gaji da sai dai kici ki kasayar

"Ai hajiya Ni tuni na gano kece Baki gano ba kice Rabon a bankado abinda zai saka zuciya tashi Baki taba tambayar ko shi Dan naki ne ke da matasala ba sai dai Ni kuke kallo? To za ayi duk yadda kike so tunda watan da za ayi magana ya Kama wallahi za ayi magana

Don haka yanzu sai kiyi hakuri baya gari Yana can kasar waje neman lafiyar da zata bashi Yan dagwai dagwai din da kike magana idan ya dawo sai kizo kuyi maganar kafin lokacin Ni na Dade agidan mu tunda nayi kawaici nayi hakuri ba ku San nayi ba to Ak ya dawo Ni kuma ya sallame Ni

Hajiyar tayi shiru tana tauna maganar izzatu kar dai matsalar daga AK din ne na Rashin haihuwar? Karfa allura ta tono garma Kai Bata zaton hakan Kuma ko daga gareshi ne ai akwai magani sai agwada.

Da haka hajiyar ta taso inda talai tayi Mata rakiya har wurin motar ta suka tafi ita Kuma ta juyo inda Kuma izzatu tace dawa Allah ya hadata ba da talai ba?

"Kinje kun zageni ke da hajiya to in zata burgeni Mata hudu ya kamata ta aurowa ak haihuwa Kuma sun Dade basu haife mishi singa da kasuwar kurmi ba
Haka tayi ta sababi tamkar zata aro Baki ta hada da nata talai dai ta wuce daki ta barta

Kwana biyu tana cikin takaici da bakin cikin da hajiya Mama ta guma Mata inda take ta jiran zuwan me gidan don ayi ta ta Kare Wai ramamme ya zagi maye

Ya Kira wayarta yake sanar da ita kanwar shi asma,u ta haihu har gobe ake suna hajiya Mama ta kirashi ta sanar dashi inda ya bukaci ta dauki kudi dubu hamsin ta kaiwa asmau kudin aski
"Gaskiya ba zanje ba ak sai dai na tura talai ko harira Amma Ni dangin ku nayi wuri na aje su gaskiya saboda nagane basa kaunata........

"Babu komai tunda har Kika iya fada min kinyi wuri kin aje dangi na na gode.......
Dit ya tsinke wayar inda Kuma taji lallai Bata kyauta ba kamata yayi ta amsa mishi da to in yaso sai ta tura wani kawai don haka sai ta Kira wayar tana bashi hakuri cikin kissa da kisisuna har tana fadin tayi kuskure yayi hakuri da haka suka aje wayar t
Chapter 1 · 0% Book details