← Book details Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 22

Sashe 20

Zan Fasa Kwai Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga wannan Rana Bai Kara shiga cikin lamarin ta ba sai dai zai labe ya kalleta ya more ya koma gida inda kusan kullum sai yazo kuki internet cafee ya ganta batare da ya Bari ta ganshi ba

Hajiya sabuwa first lady matar Mr President take sanar da Mr President din maganar da ta taba fada mishi ta samowa Anwar auren diyar kawarta matar soja wato kudusiyya ta taso don haka atura mutane su nema mishi auren

Ya dubeta Yana murmushi
"Kice auren gata za ayiwa Anwar ba na fada Miki Yar gidan Kabir mashi Nima na nema mishi ba? Ta kwabe Baki da zaka yarda sai ince ka bar maganar Yar gidan Kabir mashi kudusiyya macece daya tamkar da goma.........
"Ba zanyi magana biyu ba tunda dai kema kin samo mishi wata sai ahada mishi biyu don haka itama Yar gidan Kabir mashi din sai muyi magana kawai

Wannan abin ya Bata ran haj sabuwa don tasan idan matar soja taji haka ba zata yarda ba Amma kome kenan zasu San yadda sukayi suka lalata Shirin Yar gidan Kabir din don kudusiyya kawai suke son tayi Rayuwa a gidan Anwar din baza ta tabs Zama da kishiya ba bare har ta Zama Bora

Sai dai da Anwar din ya shigo hajiya sabuwa ke mishi maganar kudusiyya da zaba mishi ita da tayi a matsayyin matar aure yayi saurin tareta.....

"Bana son ta hajiya ku barni na zabo matar da Nike so da kaina tunda Kuma zabar kanku kukayi ke da dady ba hada ku akayi ba.......

"Kayi karya ka bani kunya Wallahi Anwar Dole ne ka auri kudusiyya.....

'to shikenan haj duk abinda ya samu Yar mutane kar kiyi kuka da kowa......
Ya fice ya barta sake da Baki...............
[5/24, 7:50 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 38*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

........Anwar ya fito sukayi kicibus da mahaifin shi ya zube Yana rattaba mishi abinda hajiya sabuwa ta fada mishi akan Wai ta yi mishi Mata da kudusiyya wadda shi atsarin shi kudusiyya batayi mishi ba. Mr President yayi murmushi

"In Banda abinka Anwar meye na damuwa don ta zabo maka matar girma ? Nima fa nayi nufin Yi maka gata kanaji?
"Eh inaji dady.
Yauwa ai kasan gidan Alh Kabir mashi ko? Eh gaskiya kamar na sani Amma dai akwatanta min . Yayi mishi kwatance ya Kuma Gane inda ya bashi rafar dubu hamsin hamsin guda biyu ta dubu dari yace idan sun gama magana ya bada amatsayin kyauta
Ya dubi uban cikin Rashin Gane abinda yake nufi har dai ya tambaya

"Dady wa za a ba wannan kudin shi alh Kabir mashi din?

"A a kaje Zan kirashi zamuyi magana bashi zaka bawa ba ita wadda zaku yi maganar da ita zaka bawa amatsayin kyautar ka.
Ba don ya Gane ba ya taho don har ga Allah shi Bai kawo komai aranshi ba yayi nasarar Gane gidan ya Kuma tura me gadin yayi mishi sallama da alh Kabir
Atare suka iso inda Kabir kewa Anwar sannu da zuwa ya sauke shi a wurin da yake karbar Baki suka gaisa inda Anwar din yake sanar dashi dady ne ya turo shi

"Eh ai ya kirani bayan ka taho Bari in turo maka ita. Ya Mike ya bar Anwar sake da Baki Yana maimaita kalmar Bari in turo maka ita, to itawa za a turo mishi? Sai ya zuba ido kowacece itan

Fulani na zaune cikin ado da kwalliya tamkar me shiri fita party ta zubawa TV ido tana kallon India Wanda take son sanar da dadyn ta tana izuwa India don garin na burgeta sai Kuma gashi ya shigo Yana kiranta

Ta dago da sauri "gani dady
Yauwa dama bakone gareki Yana can masaukin Baki kije ku gaisa..........
"Bako Kuma dady? Ni yace maka yake nema?
Gaskiya dady bani yake nema ba sai dai in wrong address ya samu don Ni ban ba kowa address Dina ba.......

"Eh shi wannan din ma ba cewa ke Kika bashi ba Ni nace mishi yazo ku daidaita ke dai jeki idan kin dawo zamuyi magana.
Ta motse fuska don Sam acewar ta Bata ga mijin Aure a yanzu ba sai gashi Kuma ana son shigs Rayuwar ta

Tasa me aikin su talatu ta biyota da ruwa da lemu inda ta yi gaba don zuwa duba wannan marar kunyar da aka jajubo Mata

Ta taho tamkar tana Jin tausayin kasar fuskar ta murtuk Wai don kar yaga hakoranta ta shigo Babu ko sallama inda idanun su suka hadu su duka tamkar wuta taja su suka ji bugun zuciya Atare inda ta zauna tana auno mishi harara tamkar idanunta zasu fado inda talatun ta shigo dauke da tire Wanda ta jero ruwa da lemu tana Shirin ajewa humaira ta doko Mata tsawa.....

"Koma da ruwan Nan talatu wannan ba bako bane abokin Adawa ne.....

Talatu tayi dabar dabar don Bata fahimta ba inda kuma humaira ta Kuma daka Mata tsawar
"Nace ki koma dashi ko bakiji ba?
Da sauri talatu ta dauki tiren ta koma ciki inda ta fusknce shi shima Yana mamaki abinda suke nufi da turoshi inda atake ya gano gatan da dadyn yace yayi nufin yi mishi har yayi murmushi don yasan ba zasu taba daidaita wa da wannan marar mutuncin ba

Murmushin shi ya Bata haushi. "Au harma na Zama abin dariya agareka ?
"Uban me kazo yi agidan mu? Ko Nan ma kazo ne don ka sake bawa Yan sanda damar su kulle Ni ? Ta fada tana Kada kafa alamar masifa na Shirin tashi

Ya Kuma yin murmushi Wanda ke kuleta da haushi da takaici
"Kiyi hakuri Ranki ya dade............
"Kai bari fa in gaya maka dama inajiran Allah yasake hadamu don in Rama abinda kayi min
To Ni nan da kake gani wallahi uban kuturu ma ya Yi kadan bare na makaho da ba gani yake ba duk uban da ya daure maka.....

Ya gaji da Jin zagin da take mishi don Babu abinda ya tsana a Rayuwar shi irin zagi don haka ya cire hannu ya tsinke ta da Mari Marin da sai da taga giccin koriyar wuta

"Nafi karfin zagi agareki ko Zan zagu ba dai ga irin ki ba jahila marar tsinkaye wallahi ba Irina Mata ke zagi ba nafi zagi ga irinki dabba dake Kuma in har kece ake Shirin abinda aka shirya zanyi maraba da hakan ko don in koya Miki tarbiyar da uwarki Bata koya Miki ba
Ya Mike afusace ya watso Mata kudin da dadyn ya bashi ya Bata
"Gasu Nan ki kaiwa Kabir mashi don saboda su yayi tallar ki inda ya San zai samesu Ashe ke da uban naki duk nema kuke akarkashi na to ku biyo Ni Zan baku na cin abinci

Tana dafe da inda ya zabga Mata Mari har ya fice ta kasa cewa komai Akan cin fuskar da yayi mata
Me yake sanar da ita? Da gaskene tallarta dadyn yayi? Eh ai in Bata manta ba dadyn ya fada Mata shi ya turo shi don haka ta tabbata sai dai tanajin ba abune me yuwa ba matukar Kuma akace hakan sai ya yuwu to za ahaife da marar ido

Ta kwashe kudin ta nufi cikin gidan inda take ganin karfin halin shi na zuwa har cikin gidan su ya zabga Mata Mari

Kabir ya tareta
"Yaya Yar dady Yaya Kika ganshi ? Yayi Miki?
"Wai dady baka San shine yayi min wulakanci har sau uku ba?
"To dady bana son shi don fansa ma Zan dauka akanshi ba Kuma Zan kyale ba don bashi da mutunci to nima Zan gwada mishi bani da mutunci.....

"A a karkiyi haka Anwar Yana da kirki Baki fahimce shi bane don haka dama fada Miki ne bamuyi Anwar shine mijin da aka tsayar Miki Nan da lokaci kadan za ayi biki.....................
[5/25, 7:19 PM] Aunty Fauzah Yar Amanah: *ZAN FASA KWAI*

*NA*

*HADIZA BARA'U GIDAN IKO*

_Hakkin Mallakar na gidan iko ne_

*Page 39*

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

........."A a dady wallahi bana son sa don ya gama saka min kiyayyar sa idan kuma kace Dole sai na aure shi to wallahi Zan bar gida ne kawai in SHIGA duniya........

"A a ba za ayi hakan ba cewar izzatu tunda dai Baki so an Bari.
"To hakan dai yafi momy....
Ta fada tana hayewa saman bene
inda Kuma Kabir yace
"Ba fa Zan janye hadata aure da Anwar ba don auren su shine tabbata ta Akan aikina don auren ta zai zamo min tsani..........

"Nima ba zanso fasuwar auren ba Kabir na dai fada ne don kar ta gudu Amma ai gata can gidan Anwar din da haka suke rufe zancen

Koda Anwar ya koma gida Mr President ya tambayeshi "ya ka ganta ne Anwar? Ya shafa sumar kanshi
'dady batayi min ba wallahi Bata da tarbiya.........

"In Dan tarbiya ai me sauki ne Anwar sai ka dorata Kan irin taka tarbiyar munyi magana ne tuni da ubanta Kai ai Dan gata ne Mata biyu lokaci Daya? Tashi kaje zamuyi magana dashi Kabir din Kai dai ka zamo me adalci agare su Allah yayi jagora

Ya tashi ya fito yanajin shi Kam baiyi sa ar aure ba don kaf Matan da ake Shirin bashi Babu wacce yake so Amma yanajin zaiyi biyayya tunda duka iyayen shi ALHERI suke nufin shi dashi don haka ya zari key din mota ya fice wurin abokin shi badamasi Wanda ya zamo Dan gidan Alh uba Dan yaro don ya sanar dashi irin auren da ake Shirin yi mishi
Yana tafe kamar Wanda akacewa kalli can sai kawai idon shi ya hango mishi ummita wadda ke tafiya akasa zuwa kuki

Gabanshi ya amsa inda ya kusa buga motar Amma Allah ya tsare ya dawo Kan doka da oda inda Kuma ya nemeta sama ko kasa ya rasa
Chapter 20 · 0% Book details