← Book details Zaman Idda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 15

Sashe 7

Zaman Idda Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Wata sassanyar ajiyar zuciya ta sauke sanda ta jita akan ɗan madaidaicin ƙirjin Naseer habiebyn nata ta ƙanƙameshi tana fashewa da kuka,
Turus ya ƙame cike da mamaki da al'ajabi to kukan na uwar miye? takeyi? laillai daɗi ne ya mata yawa a ƙasƙance ya ɓanɓareta daga jikin shi cike da ƙyama ya jefar a ƙasa ya wani kalleta sheƙeƙe ya tofa mata yawu a fiska ya doka uban tsaki yayi gaba
ƙamewa tayi a gun cike da waswasi tana tariyo ɗan abinda yafaru da sauri ta miƙe tana girgiza kai ta rufa mishi baya ina wannan ba Naseer ɗin ta bane ko kuma wani ya ɓato mishi rai a waje amma Naseer ɗinta bazai mata wannan tozarcin ba
gudu gudu sauri sauri ta tadda shi har ya isa falon ya zauna saman kujera yana cire takalmi
bata daddara ba ta zagaya ta baya ta sarƙafo hannuta a wuyanshi ta ɗan manna mishi fuskarta gefen kuncin shi
wani tururi da hadarin bala'i ya turnuƙo shi ya banƙare mata hannuwan ya wantsalo ta sai gata a gabanshi cike da fusata ya fara dalla mata mari idanu a rufe yake dukanta tun tana girgiza kai tana shanye dukan har ta fara kuka da ƙoƙarin ƙwatar kai bai ƙyaleta ba sai da yaga ya mata likis sannan ya jefar da ita ƙasa sai huci yake
ya nemi É—aya daga cikin kujerun falon ya zauna yana ta faman sauke ajiyar zuciya
kokawa take da numfashinta da kuma zuciyarta tana girgiza kai take tabbatar wa kanta ba Naseer bane wani ne yasa fuskar naseer ya zo ya yaudare ta ya ɓata Naseer a gunta ko kuma wasu suka bashi giya yasha dan yazo ya wulaƙanta ta wannan tunanin shi yayi tasiri a zuciyar ta tai wani ɗan guntun murmushi mai ciwo cike da ƙarfin hali ta fara ƙoƙarin miƙewa ta buɗe idanun da suka mata nauyi ta fara rarrafa wa zuwa inda yake zaune tana kuma bawa kanta ƙwarin guiwa
ɗago idanuwan shi da sukayi jajur yayi ya watsa mata wani kafirin kallo wanda yasaka ta gaggawar mayar da kanta ƙasa bata ankare ba ya taso ya damƙo gashin kanta da ɗankwalin tuni ya fice tasaki wata marainiyar ƙara ya ƙyalƙyale da dariya ya fizgota ta faɗo kan jikin shi cike da mugunta ya damƙi breast ɗinta ɗaya ya matse sai da ta saki wani ɗan guntun fitsari
bata dawo hayyacinta ba daga muguwar matsar da yayiwa breast ɗinta ya fara magana wacce ta saka nuriyya far a ƙyalƙyala dariya kamar wata taɓaɓɓa
"ki nutsu ki dawo hayyacinki Sa'adah ki buɗe idanun ki ki wanke kunnuwanki ki ji ki kuma saurari abinda nazo miki dashi ki yiwa kanki adalci ki kuma tabbatar wa kanki cewa ni dake tun can bamu dace ba nafi ƙarfinki da duk wata tsiya da kuka mallaka nashigo rayuwar ki ne dan in tarwatsa ahalin in kuma kassara ki in lalata future ɗinki kawai dan inyi farin ciki ban taɓa sonki ba asali ma kullum tsanarki ƙara sabunta kanta take a zuciya ta na daure ne domin in cika burina to Alhamdulillah buri na ua cika a yau kamar yandz zaki fice min a cikin rayuwata a yau!
ta runtse idanu jin wata almara yo almara mana da bala'i dai so ake taji haushin Naseer to ƙaryar mutum in ma asiri aka mishi to uban bokan ma yayi kaɗan
ta ɗan buɗe ido jin ya sassauta riƙon da yayi wa breast ɗinta yasa ta kuma narkewa ajikin shi ta fara ɗan shafa jikin shi cike da shagwaɓa tace
"relax nasnoor nasan ba kai bane an canja min kai ne ko kuma wasu maƙiya mahassada sun mana asiri dan su raba mu to kace musu nace ƙarya suke ni da kai mutu ka raba ne"
da sauri ya katse ta tare ingizata tayi gama ya cigaba da cewa" a gidan ubanwa zamu mutu tare? ke wai wace irin jahila daƙiƙiya ce ki buɗe kunnenki da kyau nine naseer ba ubanda yamin asiri ni kaina shaiɗanin kaina ne bana buƙatar wasu tsirarun sheɗanu a tafiya ta inaso ki kalli abin da zan nuna miki da kyau zuciyarki ta buga ki rage min aiki"
bai jira cewar ta bai kuma da mu da murmushin da take saki ba yanajin tana faɗin "nasani wallahi ba kai bane Naseer ɗina ba zai min haka ba sannan ko da ace kai ɗin ne to na maka uzuri nasan ƙilan laifi na maka na cancanci hukuncin da yafi wannan ma kamin indai zuciyarka zatayi fari kaji daɗi" bai ko kalle ta ba ya miƙa mata wayar shi bayan ya kunna videon yace "ina miki ta'aziyya uwarki yau ta baƙunci laheera tana tsine miki albarka na shigar saurin da kika mata bayan taji aikin maxa ba kamar soloɓiyon tsohon ki ba asha kallo lafiya"
ya wani lumshe ido yana girgiza ƙafa yana jiran yaji tayi wurgi da wayar ta taso ta cacumeshi sai yaji akasin haka,

*************************
Alh ma'aruf ya iso lafiya inda yazo ya iske wani ƙarin tashin hankalin na mutuwar mai gadin shi
mutane sun taru ana ta al'ajabi da taradda di mutane sunyi jigum jigum..
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*011*
_Yaseen in zaki fara tun yanzu ki fara karantawa tom babu tsarin turomin pls daga farko a wannan tafiyar in baki da raayin farawa tun yanzun ta ra abinki🦻🏽🦻🏽🦻🏽_
Chapter 7 · 0% Book details