← Book details Zaman Idda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Zaman Idda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bata ƙyale yarinyar nan ba sai da taga bata numfashi ta tashi tsaye tana ƙyaƙyata dariya cike da mugunta ranta fess ta nufi fridge ta buɗe ta dauko robar ruwa har sun fara dutsi ta bude ta kwar a mata wata iriyar ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da sheshsheka idanunta a rufe ta kasa buɗe su sabida nauyin da suka mata wata iriyar azaba take ji a dukkan sassan jikinta nadama take danasani take na kuskuren shigowa gidan wannan ƙeƙasashshiyar matar marar imani, ba tun yau ba ta mata kashedi yafi dubu akan kuskuren da zatayi idan ta aurar mata miji tana ganin wasa take ashe ita ke wasa da rayuwar ta tsawon wata uku da tayi agidan me ta ƙaras?
tunaninta ne ya katse sanda taji an jata ƙiiiii kamar wasu kayan wanki
Bata tsaya ko'ina da ita ba sai da ta kaita bakin ƙofar shigowa falon ta wurgar bayan ta ya bugu da ƙasan wurin ta rintse ido tana kiran sunan ALLAH
sai huci take tana haki tana maseefa
tace " ki kwana anan ki wuni anan daga yau wallahi kinji na rantse na haramta miki shigon min falo bare kice zaki shiga wani so called ɗakin ki ai wanda baiji bari ba zai ji hoho zan ga uban da ya ɗaure miki ƙugu tsaye nake ƙyam a gida na ke ɗin nan baki isa ki rushe min record ba wallahi kiyi shawara da zuciyarki kwanaki uku ya rage Alh ya dawo kina da damar zubda cikin kafin ya shigo ƙasar nan ki samu ƴenci kema in ba haka ba wallahi sai kin gwammaci mutuwar ki akan rayuwar da zakiyi"
Fuu ta kwashi ƙafafun ta tayi ciki ta bugo ƙofar hada saka key,
sai kokawa take da numfashin ta da kuma zuciyarta anya? anya ba zata xubar ba? bala'in yayi yawa duk ixayar da matar nan ke mata bata iya ɗaga ido ta kalleta ko ta buɗi baki ta faɗa wa wani halin da take ciki ta saka hannu ta shafo cikinta wasu hawaye masu ɗumi na zubo mata wani irin so ƙauna da begen abinda ke cikinta ya mamaye xuciyarta anya idan ta zubar dashi ta mishi adalci? wata zuciyar ta kawar mata da wannan tunanin ta jefo mata na ƙunci da bala'in da xata shiga a hannun kishiyarta ,
a hankali ta tashi zaune tana dafe bayanta
zuciyarta na rarrabuwa da neman mafita da maslaha ta fara buga ƙofar falon

*************************
Kusan awa ɗaya ya kwashe suna xubar da ruwan luv shi da Bintu ranshi fess yarinyar tayi ne ba ya jin ko ranshi ta nema zai hana ta tasan sirrin maza ƙwarai ta iya tafiya da xuciyar wanda ya faɗa tarkon ta
jin yarinyar yake ta cika ko'ina a zuciyar shi cike da farinciki bayan sunyi sallama kamar kar su rabu a wayar ya nufi toilet ya É—an watsa ruwa
Shaf shaf yafito da sauri sauri ya kintsa kasancewar shi mutum mai sassanyan kyau tsaf ya fitoo cikin dark blue ɗin shaddar data amsa kyakkyawar fatar jikin shi da bata cika haske ba ya kafa hula data dace da zaren da aka ƙawata ɗinkin shaddar dashi haka ma takalmin yabi jikinshi da turaruka masu sanyin ƙamshi ya dubi kanshi a madubi cike da ƙaunar kai da alfahri yana ta sakin murmushi
ya fito ya nufi ɗakin Nuriyyah yana sauya yanayin fuskar shi zuwa tausayi da neman agaji! a hankali ya tura ƙofar ya shiga ɗakin
bata ciki da alamu tana banÉ—aki ya fara wurwurga idanu idanunshi ya sauka akan miror ya hango wannan akwatin da sauri ya haÉ—e wani daddaÉ—an miyau wani sanyi na kwaranya a zuciyar shi
ya hango jakarta saman bedside drower da sauri ya ƙarasa ya zuge ziff ɗin ƴen canji yake so da zai zuba mai a mota bai ko tsaya ƙirgawa ba ya ɗebo kuɗin ya cusa aljihu daidai ta fito banɗakin ,

*ki fara bi tun yanzun in zaki fara ƙawata idan baki da raayin karantawa yanzun ki tara abinki kada muyi nisa kice kina nema daga farko*

_ƘARSHEN DUNIYA YA KAMMALA IN KINA BUƘATAR COMPLETE DOC #500 KACAL NA TABBATA BAXAKI NADAMAR SIYA BA_
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
Daga tsintuwa....loarding
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*005*

_Yaseen in zaki fara tun yanzu ki fara karantawa tom babu tsarin turomin pls daga farko a wannan tafiyar in baki da raayin farawa tun yanzun ta ra abinki🦻🏽🦻🏽🦻🏽_

Da ɗan ƙarfin da ya rage mata ta fara kici kicin ƙwatar kanta sai dai ta kasa Kareema duka ƙarfinta ta saka ta danne Hunaifa, ga jini nata malala ƙasa har yanzun wuƙar na jikin hunaifa ganin zata ɓata mata lokaci yasa da ƙarfi ta fixgo wuƙar ta kuma chaka mata ta ƙara zarowa ta saita saitin xuciyarta ta daɓa wuƙar take Hunaifa ta saki wata irin ajiyar zuciya ta lumshe idanu bakinta na motsawa a hankali har rai yayi halinsa,
wata wawuyar ajiyar zuciya Kareema ta saki ta daɓashe ƙasa agun tana sakin numfashi tana kallon gawar hunaifa datayi fayau sai wani ƙayataccen murmushi a fuskar kamar ba gawa ba
taja tsaki ta saka wuƙar nan ta karto jinin ta lashe tana lumshe idanu ƙirrr taji ƙarar wayarta da sauri ta dawo hayyacinta bata amsa wayar ba sai ma kasheta da tayi gaba ɗaya cikin sauri sauri ta fara haƙa rami da yake ta saba bata wani daɗeba ta haƙa daidai tsawon hunaifar ƙiii ta jawota haka ta wullata cikin ramin ta bi da ƙasar mai jini ta rufe ta mai da wacce ta haƙo ta daddale ko ɗar babu ajikinta sai ma wani iskan nasara da cikar buri da taji yana shiga sassan jikinta pipe ɗin da ake ban ruwa cikin lambun ta jawo ta yayyafa wa ƙasar ya saka ƙafa taɗan tattaka tsaf wajen ya shafe kamar ba ayi wata rami agun ba ta kwashi kayan ta maidasu inda suke ya kakkaɓe jikinta tayo hanyar dawowa cikin gidan tana ƙoƙarin kunna wayarta,

*********************
Tafi ƙarfin awa guda agun tayi kukan har ta bawa uku lada ta kasa faɗaɗa zuciyarta tayi tunani ciwo zuciyarta keyi kamar ta ciro ta jefar wa zata tunkara? bata da komai dik ta sadaukar dasu wa mijinta Naseer bama wannan ba kwanakin nan mafarkin da take yawan yi na dagula lissafinta zuciyarta ta kasa nutsuwa da auren da Naseer ke nema sai dai bata da ikon hanawa a yanzun da lokaci ya riga da ya ƙure
a taƙaice dai ita kanta bata san makomar ta ba ta guji yan uwa ƙawaye duk dan faranta ran Naseer tamishi sadaukarwa da yawa a rayuwa sai dai zuciyarta a yanxun rawa take tsoro takeji tana gudun watarana Naseer ya butulce mata,
tayi shiru tana jin karatun da sashen zuciyarta mai raunin ke mata _ki farka nuriyyah mata sun waye sun daina bari daɗin bakin ɗa namiji ya ruɗesu ki tashi kiyi yaƙi da zuciyarki raunin ki yayi yawa zaki kuka zaki koka a sanda Naseer ya lulluɓo wata ya kawota gidan nan dasu mata lokacin zaki gane true calour na maza_
da sauri ta tashi tana girgiza kai tana faɗin "stop stop never wallahi banda Naseer mijina ba butulu bane bazai min butulci ba akan wata mace ina!" ta ƙarasa faɗa tana matse rigar Naseer ɗin a ƙirjinta hawaye nata rigengyaton fitowa daga idanunta tana ƙarfafa wa kanta guiwa akan banbancin mijinta da sauran maza,
Ɗayan alƙawarin dz tamishi na mallaka mishi wannan gidan ya faɗo mata ta ɗanyi murmushi tana tuno kyakkyawan sajen da yake sake ƙawata mata fuskar Naseer tace "anything for u *NASNOOR*
xan mallaka maka duk wani abu da ya kasance mallakina dan kawai kayi murmushi ni da duk abinda ya zamo mallakina to ka É—auka yazama mallakinka!"

#COMMENT
#SHARE
#NASNOOR#
🥰🥰🥰🥰ZARAHBUKAR
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*007*
_Yaseen in zaki fara tun yanzu ki fara karantawa tom babu tsarin turomin pls daga farko a wannan tafiyar in baki da raayin farawa tun yanzun ta ra abinki🦻🏽🦻🏽🦻🏽_
Chapter 3 · 0% Book details