← Book details Zaman Idda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 15

Sashe 6

Zaman Idda Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

COMMENT
SHARE
#NASNOOR
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*006*
_Yaseen in zaki fara tun yanzu ki fara karantawa tom babu tsarin turomin pls daga farko a wannan tafiyar in baki da raayin farawa tun yanzun ta ra abinki🦻🏽🦻🏽🦻🏽_

Tuno Naseer da kyakkyawan zamansu da da irin madarar ƙaunar da suke lasa yasa taji ƙarfi ajikinta wani farin ciki ya mamaye xuciyarta da ƙarfin guiwa ta fara shirya jikinta dan tarbar mijinta farin cikin zuciyarta sosai take jin haushin kanta da xuciyarta dake saka mata kokonto akan Naseer ta sani mijinta daban yake ko auren nan ma tasan ƙaddara ce da kuma matsin ƴen uwanshi akan rashin haihuwarta
ita dai tanason Naseer zata kuma cigaba da son shi har bugun numfashinta na ƙarshe zata kuma so duk macen da ya auro ya kawo cikin gidan xata rungumeta su zauna lafiya,
Tsaf ta shirya tayi kyau matuƙa kasancewarta dama mai kyan kwalliyar ta karɓi jikinta matuqa ta fesa turaruka masu sanyin ƙamshi
ta nemi gefen gadon ta ta jawo wayarta tafara laluben number ɗin Naseer so take taji me xaiyi dinner dashi sai tayi ƙoƙarin kammala wa kafin yadawo sai dai har wayar ta ƙaraci ring ɗinta ta gama bai ɗaga ba ta kuma kira nan ma shiru
_abin haushi_
sai kawai tayi murmushi tana ƙarfafawa kanta guiwar baya kusa da wayar ƙilan ma a mota yabarta sai kawai ta shiga tsara mishi kalamai masu daɗi ta tura mishi tasan zaiji daɗi ƙwarai itakam farincikin takeso akan murmushin shi xata iya bada fansar rayuwarta🤔
har ta aje wayar ta tashi sai kuma ta É—auka ta fita da ita dafatan ya biyo bayan kiran nata inya gani duk da tasan da wuya domin bin kira ba É—abiar shi bace sai dai in kaji shiru ka kuma kira
falo ta dawo ta zauna tana ƴen tunane tunanen rayuwa zuciyarta na ƙoƙarin sako mata tunanin mahaifiyarta da ta ɓata a hannun kidnappers tsawon shekaru uku kenan tana da halin biyan ransom ɗin da suka nema amma Naseer ya kanainaye ya hana ta bayar acewarshi zasu gaji da riƙonta ne su sakota
A lokacin kuɗin da ta haɗa 50m da suka nema a ranar ɓarayi suka hauro suka karɓe kuɗin a dangi kowa yabar maganar ma ganin itace dolen ta ta barta suma dole suka shafa wa kansu lafiya suka zuba mata ido duk wanda ya zo a lokacin akan maganar sai Naseer ya hanata cewa uffan shi yayi ruwa yayi tsaki har maganar tabi iska
ta share hawaye tuno da mahaifiyarta a mace? ko a raye? ALLAH masani

*********************
Cike da hasala baƙin cikin abinda Hunaifa ta mishi zuciya na zafi ya rattaba mata saki uku nan take ya lalubo number mahaifinta Malam buba ya turo mishi da gargaɗin duk wani abu ya samu cikin shi sai yayi shari'a dasu in zasu nemota su nemota aure ne batayi to ya saketa amma intayi kuskuren zubar mishi da guda jini to daga nan har kotun duniya sai sun je

Kareema kam ko da ta shiga cikin falon kai tsaye gidansu Hunaifa ta fara kira tana kuka take shaidawa mahaifiyar Hunaifa yanda sukayi da Hunaifa akan batun zubar da ciki tana kuka take faɗin "wallahi mama yarinyar nan aljanu gareta baki ga dukan da ta min kan na hana ta zubar da cikin hada wuƙa sai ta kasheni na gudu ɗaki dan tsira da rayuwata anan ta samu nasarar guduwa dan Allah ku taimaka mana wannan cikin mun saka mishi rai dan ALLAH ta dawo wallahi ko me takeso zan sa Alh yayi mata" ta ƙarashe maganar dz wata kafirar sheshsheka Maman Hunaifa batayi mamaki ba jin wai ta gudu kasancewar dama sun san bata son auren to ganin tunda akai auren babu wani abu da ya biyo baya yasa sukayi tunanin ta haƙura ta rungumi gatan da suka mata na aura mata miji irin Alh Ma'aruf dala burin kowace ƴa mace ashe tana nan kan bakanta
Ƙwafa tayi ta fara lallashin Kareema da bata tabbacin zasu yi iya yinsu ganin sun shawo kan matsalar afara sanin inda Hunaifar ta nufa tukun suka ajje wayar kowa cike da jimami
Kareema ta daka tsallen murna ganin plan É—inta na tafiya yanda ta tsara tabbas a komai ita É—in mai nasara ce,
Maman hunaifa na niyyar fita zuwa ɗakin mijin nata sai gashi ya shigo ɗakin hankali tashe yana waje saƙon surikin nashi ya riske shi cikin matuƙar tashin hankali ya faɗo cikin gidan dan sanarwa iyalin nashi salalar tsiyar da Hunaifa ta musu

#COMMENT
#SHARE
#NASNOOR#
#ZARAHBUKAR#
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*010*
_Yaseen in zaki fara tun yanzu ki fara karantawa tom babu tsarin turomin pls daga farko a wannan tafiyar in baki da raayin farawa tun yanzun ta ra abinki🦻🏽🦻🏽🦻🏽_
Chapter 6 · 0% Book details