← Book details Zaman Idda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 15

Sashe 14

Zaman Idda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

GIDAN ALH MA'ARUF
Abu dai ya kacame babu wani sauƙi Kareema nata cin karenta babu babbaka hankali kwance take rayuwarta sai dai har kullum tana kuka da ƙaryata zancen cewa take sharri akawa mijinta iyayen Humaida suma hamkalinsun ya daɗa tashi jin wani sabon zancen ga ƴan bani na iya dake daɗa tunzurasu da aka fara jujjuya zancen da cewa ɗan mafiya ne matarshi ta ɓata da ciki anzo bincike an iske gawar mai gadi still kuma ga gawar yaro a cikin mota lallai da akwai wata a ƙasa kwata kwata ma ba a barin ganinshi a gida kuma madam Kareema ta dage tana ta ingiza wutar a media da wata wayarta ta buɗe sabon acc na facebook twiterr dasu instgrm to babu laifi kam kwalliya ta biya kuɗin sabulu dan haƙanta na cimma ruwa tana ɗaukar hankalin mitane da bayyana musu wasu halaye na Alh da take faɗar a ɓoye suke wanda a zahiri kaff halayyarta ce take buɗewa duniya a baɗini kuma take jingina abin ga mijinta
Media ta ɗauki ɗumi an kuma rasa wanene mai bada waɗan nan bayanan sirrin? duk ta saki post sai ta haɗa da hujja hakan yasa kyllum police cikin zarya suke gidan a kullum sukaxo kuma sai sun samu wata sabuwar shaidar kawunan mutane kam a ɗaure yake mutanen unguwa kuma suka fara boren xasu ƙona gidan duk wani wanda ɗanshi ya ɓata a unguwar ba a kuma ganshi ba sai ciwon abin yadawo mishi sabo to babu tantama alh ne ke sace musu yara yakaiwa ƴan ƙungiyar asiri madam kareema dai ta zama haddasana tana gefe kuma tana narkawa lauyoyi kuɗi da roƙon suyi duk mai yuwuwa su fiddo mata mijinta
ita dai burinta yayi baƙin jini sunanshi ya ɓaci aji ƙyamar haɗa xuria dashi ta tabbata xuwa yanzun mutum ko karen hauka ya cijeshi baxai yi gigin kawo ƴarshi gidan da sunan kishiyarta ba shine kaɗai fatan ta ta zauna ita kaɗai ƙwallin ƙwal a gidan ta da alamu kuma tana gab da cimma nasara,
_sai dai kana taka ALLAH na nashi bata sani ba wani matakin nasarar ta kuma cicciɓashi ya hau_
su Nadra dake boarding sun dawo gida sakamakon tsana gami da tsangwamar da ƴan uwansu ɗalibai ke musu basu da saƙat a cikin makaranta to dama Najma itace shalelen Alh so abin yafi dukanta Nadra kam kadaran kadahan ce harkokinta kawai take,

*************************
Oga nasir kam hankalinshi kwance ya nufi ɓoyayyen gidan nan da ya kashe Umman Nuriyya yana tafe yana shan kiɗa a mota duniya tai mishi daɗi ko banza yanzun ya fanshe kaso saba'im cikin ɗari na baƙincikin shi matsalar shi ɗaya hayyatu nuriyya tabi ta hayyaci rayuwar shi baiyi tunanin cewa zuciyar da take da ita zata barta ta fahimceshi ba sai dai abin mamakin abin ma sai ya juye yasan nuriyya tun tana ƙarama yasan baƙar zuciyarta da kafiya da mugun naci har a zaman su amma duk tasirin so ya dakushe karsashinta ya danne soyayar da ke tsakaninta da mahaifiyarta me zai yi ya gode wa Habeeb? da wanaan tunanin ya ƙaraso gidan ya fito a motar ya buɗe gidan ya koma ya shigo da motar yayi parkinng a ɗan madaidaicin wajen parking ɗin dake farfajiyar gidan da rangajin shauƙi yake taku cike da taƙama
ya buɗe ƙofar falon har ya nufi ɗakin da gawar take ya fasa ya nufi inda yake ajje takardu da duk wasu abubuwa masu munimmanci sai dai me tun kafin ya ƙarasa ya hangi wardrobe ɗin a buɗe a mugun hargitse ya ƙarasa babu komai sai filin wurin ko ɓallen paper babu bare wannan box ɗin da ya karɓ a hannun Nuriyya hannu ya ɗora a kai da gudun bala'i ya fice ya nufi ɗakin da gawar take ya tura toilet ɗin nan ma wayam babu gawa babu alamhnta
_ƙara ƙa ƙa ƙara_

*RAMADAN PROMO*
💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
_Mutane na amana kuna ina? ku rugo kar ayi babu ku yaseen sauƙi ya samu ALLAH ya yarda yanda na samu da sauƙi kuma kuzo in sauƙaƙa muku albarkar watan nan mai zuwa akwai duscount na kifi so duk wacce bata siya ba ta rugo kar ayi ba ta ki faɗawa oga sauƙi ya samu kuzo mu samu sauƙin a tare kifi yayi wuta wlh amma cikin yrdr ALLAH ansamu mai kyau kuma mai sauƙi maxa ku hanzarto kafin ya ƙare💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼_
_KAR MU ƁATA WA JUNA LOKACI IDAN KINSAN BA SIYA ZAKIYI BA DAN ALLAH KARKI BIYO NI MASU SON SUJI DAƊI SU MORE DAƊI DA ƊANƊANON KIFINMU KAƊAI NAKE KIRA_

siyen É—aya ko sari
LOCATION:katsina ,kano ,Yobe, muna aikawa ko ina kiki siyan nagari maida kuɗi gida💃🏼💃🏼💃🏼
08038541511
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*An daina yayin zaman kashe pant hajiya ta ki dage ki nemi sana'a ki wuce gori kici halak ɗinki hankali kwance muna siyar da lalle ɗan gaske namu ba irin nasu bane ki siya ki ƙawata hannu da ƙafa a birge mai house ki kuma siyar kici riba muna sai da ɗai ɗaya muna bada sari akwai kuma wardrobe balls ƙamshi ƙamshi riba biyu kiji ƙamshi ya cika miki ko'ina ki siyar ki samu riba muna sai da ɗaiɗaya muna bada sari munayin logo da bussiness card da flyer akan farashi mai sauƙi domin ganin hotunan kayanmu da price ɗinsu ku tun tuɓi wannan lambar 08038541511*

*020*
_Yaseen in zaki fara tun yanzu ki fara karantawa tom babu tsarin turomin pls daga farko a wannan tafiyar in baki da raayin farawa tun yanzun ta ra abinki🦻🏽🦻🏽🦻🏽_

Hannu ya ɗora aka yana jin wata guguwar tashin hankali ta fara jujjuyawa dashi meke faruwa? ƙarasawa yayi cikin toilet ɗin yana ji kamar ya fashe da kuka sai dai kukan yaƙi bashi haɗin kai dube dube ya fara zuciyarshi na tabbatar mishi gawar na cikin bandaƙin amma idanunshi suna ƙaryata hakan duk wani lungu da saƙo dake cikin toilet ɗin ya duba babu ko ɓallen ɗan kunnen Ummar zama yayi akan tiles ɗin banɗaƙin haɗe da runtse idanu ganin abin yake kamar almara me hakan ke nufi? waye ke bibiyar shi har ya san da wannan ɓoyayyen gidan nashi har yazo ya kwashe abubuwan da ya kwashe shekaru yana adanawa? babban tashin hanklain ma ɓatan gawar da shi ga barta a cikin gidan cikin ɗaki sannan cikin wannan toilet ɗin da yake zaune, duk inda tashin hankli yake Naseer na ciki da sauri ya tashi ya fito daga toilet ɗin ya fara birkita kayan ɗakin yana neman ta inda gawar zata ɓullo duk ya watse ɗakin babu gawa babu alamar ta,
da sauri kuma ya fito ya koma ɗakin nan na farko inda yake ajje takardun nan ma ya birkice babu komai sai sannan wani mugun kuka ya ƙwace mishi meke shirin faruwa dashi? waye ya mishi wannan mummunar kwanton ɓaunan? me yayi wa mutumin da ya mishi hakan? shikenan asirin shi ya tonu me yasa meyasa sai da ya riga ya saka rai da fara rayuwar jindaɗi bayan fansa sannan lamarim zai juye? ina gawar? bashi da mai bashi amsa ya zauna yaci kukan shi har ya hangoshi ƴan sanda sun tisa ƙeyarshi zuwa station ƴan jarida nata ɗaukar shi hoto da watso mishi tambayoyi ga ga ƴan social media nata caccanja wa labarin salo wani mugun kukan ya kuma kufcs mishi shikam dai ya tabbatar baya cikin masu sa'ar zuwa duniya!
ko me ya tuna? sai yayi zumbur ya miƙe a guje ya fito daga cikin gidan dole kafin a kama shi yana buƙatar ganawa da Nuriyya tabbas buɗe get ɗin yayi da sauri yazo ya faɗa cikin motar motar a gaggauce ya tayar ya fito yaxo ya rufe get ɗin ya koma motar da wani irin speed yaja motar kwata kwata baya cikin nutsuwar shi burin shi ɗaya ne a yanzun shine yayi ido huɗu da Nuriyya
Chapter 14 · 0% Book details