← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 35

Sashe 6

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu wanda ya sake shigowa inda Samayya take har dare, hakan ya yi mata daɗi.Saffy ce ta murɗa kofa ta dawo ciki wata iri shiga mara kyau gani, ciki fashashiyar muryar ta iri ta 'yan shaye-shaye mai cike da umarni a ciki ta ce.“Ki shirya. Alhaji na son ganinki yanzu. Kar ki sake min tambaya,ki sani in kika bi umarnin to rayuwarki za ta canza.”Sumayyah ta kalle ta cikin tsoro.
“Amma… me zan je in yi wurin Alhaji da dare haka?”Saffy ta yi murmushi.“Zaki ga komai da idonki. Ki taho kada ki tsaya tambaya.”
Cikin fargaba, Sumayyah ta bi ta har suka shiga babban wani ɗaki me cike da kayan alatu.
An cika wurin da kayan alatu- kujeru masu sirdi, ƙamshin turare mai nauyi, da sautin dariyar maza da mata.
A can tsakiyar ɗakin, ta hango Alhaji Ɗan Dubai zaune a kan kujera mai faɗi, yana dariya da wasu manyan mutane masu kuɗi-wasu da babban ciki, wasu da farin gemu.gefe su duk yaran 'Yan mata masu ƙananu, a tskiyar parlour wata yarinya ce mai kyawu gaske,tana ta rawar banza cikin night gown duk ta kama jikin ta. Sumayyah tana shiga, duk suka juya,
Idanu suka zuba mata kamar yadda karnuka ke kallon nama mai ƙamshi.

Wani daga cikin manyan ya ɗaga kofi lemo yana dariya:“Alhaji, wannan sabuwar ce? Kai, kai! Ka ce kaya sun sauka!”
Wani kuma ya da gefe yace:

“Wannan fa ba irin tamu bace Ga ga duk kan alama sabuwa ce, ba ta saba da irin wannan rayuwa ba.”Alhaji Ɗan Dubai ya yi Murmushi yana kallon Sumayyah.
“Eh, sabuwa ce.. kuma tana da kyau. Ku bari in koya mata yadda ake zama ‘yar gari mai sanan sai ta fara kawo muku ziyara.”Yana rufe baki dariya ta cika ɗakin.
Sumayyah ta tsaya cak, jikinta ya mutu gaba ɗaya.

Hannu ta soma rawa, idanunta suka cika da hawaye.Ta tuna Innar ta, da maganarta ta ƙarshe, zuciyarta ta soma dukan uku-uku.Ta juya da ƙarfi za ta gudu,Saffy ta rufe ƙofar ta tsaya a bayanta tana murmushi.“Kin riga kin shigo,kaddarar ki ta fara daga yau.”A wannan lokacin ne Sumayyah ta gane cewa duk wanda ya shiga wannan gida- ko dai ya lalace.kifa kanta tayi tsakani tsinyar ta tana kuka, tana ambaton:“Ya Allah, ka bani ƙarfi. Kada in zama ɗaya daga cikin su…”

*****

*Tuna baya*

Rabi yarinya ce mai kawaici da kunya.A lokacin baya,Malam Sule Giɗaɗo yaro ne matashin ankawo shi almajiranta Bunkure, ya taso da ƙazo kuma shine Baban yaro aciki Almajirai Malam Idi hakan ya sa duk saure almajiran Malama idi suke shaka sa acikin wanan hali Ya hadu da Zulai ya aure ta haihuwar ta daya ya sake aure Hauwa, yana da haka ɗauka kaka ta tazo masa acikin ƙauye su,ya shahara, guri yiwa mutane kauye Giɗaɗo wa’azi, ya zama mai jama’a, wanda kowa yake girmamawa.lokaci Da ya sake zuwa gaida Malam Idi, ba don neman aure ya zo ba, sai don neman gaida Malami sa, wato mahaifin Rabi. Bayan su gauisa da nutsuwa Malam ya Kali Sule yace. “Sule ga yarinya ta Rabi,na baka ita a matsayin sadaka domin Allah.”Sai da gaban Sule ya buga dan Shi rabi bata taɓa burge shi ba Gasali na Matan sa biyu sun isheshe rayuwa.Rabi da tazo kawo masa ruwa ta tsaya cak. Kallon mahaifinta kawai take yi, idanunta suka cika da hawaye.
Ta so ta ce a’a, amma kalmar “na baka ita sadaka” ta rufe mata baki. Haka Nauyi Malam idi da kuma kwarjinin da yasa shi amincew da zumar washe gari zaizo da shedu a daure masa aure. Haka kuwa akan yi washegari Malam Sule ya dawo da magabatan aka ɗaura musu aure wanda a take a lokaci ya tafi da Rabi. Bayan kwana biyar da faruwar haka, cikl dare gobara ta tashi babu gidan da bata shigaba wanda yasa iyaeye Rabi konewa musru, hakan ya jefa Rabi ciki tashin hakali da damu wanda hakan shi kuma Yayi wa Malam Sule daɗi ga samu hanyar ƙuntata ma har ta gaji ta bar masa gidan.

Daga wannan rana, rayuwarta ta sauya gaba ɗaya.a gidan Malam Sule, Rabi ta tarar da matan sa biyu- Zulai da Hauwa.Su biyun sun haɗu gaba ɗaya wajen wulakantarta.A wurin cin abinci, haka zasu fara yaɓa mata magana ciki waka ko wasa tauna kamar kullum suna zama Zulai ta kalleta ta ce.“Ke fa matar sadaka ce, ba ‘yar gida ba. Me kike nema anan?” haka ta zame hannu ta ta barsu, shewa sukayi suka ci gaba da cin tuwo su. haka rayuwar ta taita guda na acikin gidan Malam Sule.Idan ta yi ƙoƙarin shiga cikin su, sai su zage ta, su kwace mata abin hannunta.
Malam Sule kuwa, ko da ya ga hakan, bai ce komai ba.A idonsa, Rabi ba komai bace face kyautar da aka bashi-a matsayi matar sadaka.Kullum tana kuka cikin sirri, tana roƙon Allah:

“Ya Allah, ka bani haƙuri, ko da kuwa zuciyata zata tarwatse.”Haka rayuwarta ta koma kamar ta bawa a cikin gida,ana ɗaukar ta ba mace ba, tamkar wacce aka kawo don yi wa sauran mata hidima.Wata rana, Zulai ta zubar da abinci a ƙasa.ta kwaɗawa Rabi kira da gudu ta fito daga nata ɗaki jikinta na rawa haka ta durƙusa agab Zulai tace"Yaya Zulai gani.”tsaki tayi ta tura ɗaukali gaban goshi tace."Rabi, ki tsabtace nan. Ai ke ce ‘yar sadaka, aikin banza ya fi dacewa da ke.Ubanki saboda tsabar kwaɗayi ya liƙawa Malam ne Sadaka.”Haka Rabi ta durƙusa tana share guri, hawaye na sauka daga idonta.Cikin zuciyarta tana jin kamar wani abu yana murɗawa,Ba wai saboda aikin bane, amma saboda yadda ake kallonta tamkar ba ta da ƙima.

Da daddare, tana cikin kuka sai Malam Sule ya shigo, ba tare da jin tausayinta ba.“Kedai anyi mashiriciya Yariya ce ke da baza Afrika yi miki fada ba, in ba kaddara ba mai zai haɗa Ni dake ”Wannan magana ta sake d
ɗanna mata ciwo a zuciya.Haka ta rayu cikin wulakanci, zargi, da kunci.Zuciyarta ta fara yin rauni-amma ba ta faɗa wa kowa ba.
Bayan shekara guda da wannan halin, Rabi ta samu ciki.Sai dai maimakon farin ciki, ta fara fama da matsanancin damuwa.
Zulai da Hauwa suna ƙin taimaka mata, suna cewa: “Ke ma matar sadaka ce, dan masifa sai da kika bin malam da Asiri har kika samu ciki kin? Wallahi sai mu hana ki kwanciya hankali a gidan Malam.”Suna yi mata duka da wulaƙanci, Malam Sule kuma ya yi duma kamar bai san abin da ke faruwa ba.Rana ɗaya cikin dare, Rabi ta tashi da ciwon ciki da zafin kai.Tana ihu tana cewa: “Kai na! Kai na! Ya Allah ka ceci Ni ka ceci ɗana!”Sai da mutane unguwa suka cika gidan masu tausayi ta basu da yawa domi duk mutaneZulai da Hauwa ne kuma gasu haifaffen cikin kauye.Tun tana kukan kanta kashe ta koma yin dariya lokaci ɗaya.tana kaiwa mutane duka tana surutu. “Ni matar sadaka ce… amma ɗana ba sadaka bane!”Daga wannan rana, hankalinta ya tafi.Babu wanda Wanda ya taɓa kaita asibiti Ciwon zuciya da ta jima tana ɗauka a asirce, ya fashe ya koma hauka babu kasuwar da bata zuwa sai tafi tafiya mai nisan gaske ta dawo duk nisan dare.Duk wanda ya gan ta sai ya ce, “matar Malam ta haukace.

Bayan ta haifi ɗiyar ta, Sumayya, mutane suka fara kiran ta da
“Mahaukaciya.”Sumayya ta taso cikin wannan hali, tana kallo mahaifiyarta tana kuka tana dariya, tana sai ta tafi yawo da Sumayyah a bayan ta tayi tafiyar kwana biyu uku batare da ta waiwayi gida ba haka kuma babu mai neman su.Duk abin da ta tsinta abola tare zasu ci da Sumayyah yariyar yar wata bakwai.Ruwa ko da na kwata ne bata fargabar sha ko ta bawa Sumayya tasha.Hakan yasa aka fara kiranta da *Yar Mahaukaciyya*

Wannan shi ne asalin haukar Rabi-hauka da ta samo asali daga zalunci, wulakanci, da ciwon zuciya, ba daga aljani ko sihiri ba.wanan labari yana nuni da irin zafin rayuwar mace da aka tilasta mata aure saboda “sadaka”, wanda ya jawo bala’in da ya rikide zuwa hauka.

*Gundari labari*
Daren Da haka Alhaji Ɗan Dubai ya kama hannu Sumayyah zuwa wani hadaɗe ɗaki, tun da ta shiga hakali ta ya sake tashi dan Alhaji Ɗan Dubai baiji kunyar taba a gaban ta ya jire rigar da take jikisa ya tun karo ta, zubewa tayi kamar mai sahafar aljanu tana roƙon sa.

“Dan Allah Alhaji kaji tausayi na kar ka lalata min rayuwa wallahi bani da kowa sai Inna”dariya ya bushe da ita"Hahhha Haba yariya duk iri dukiyar dana narkar akan ki kuma ta tashi abanza kamar ki fara dan Wallahi ba tausayi ne da niba, an gaya miki a banza muke neman kuɗi?” ya fada yana labe lebe kamar tsoho busuru.yana sake zuwa zai kama ta sai kuma taya lumshe ido ya kifa kan gado Shaɓar kamar matacce bacci ne mai nauyi ya dauke shi da alamu giyar da yasha ga tafiyar mota da yayi yasa shi bacci.Zubewa tayi ƙasan gadon, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

Wani irin shiru ne ya mamaye ɗakin, ta bishi da kallo ko afuska Alhaji Ɗan Dubai bashi da kyau kallo bare wata mu'amula ta haɗa ka dashi.tana juyo hayaniyar mutane har da ƙarar kiɗa.ta goge hawayen da suka zubo mata.“Ya Allah,ka ɗauke ni daga nan,ina Inna ita ne take yanzu? Me yasa aka kawo ni nan? Wannan ba makaranta bace… guri yaɗa alfasha ne...”

Tana fadi haka ta rufe fuskar ta da tafin hannuta, tana rawar kuka mara sauti. Da haka bacci ya ɗauke ta bata san Lokaci da Alhaji Ɗan Dubai ya fita ba sai jin kara buɗe ɗaki tayi. Da sauri ta gyara zaman ta a tunani ta Alhaji Ɗan Dubai ne ya dawo.

Wata mata ta ce ta shigo Fusakar ta taci Bleaching har wani tantarewa fatar ta take saboda tsufa da kuma mai lalata mata fusakar da Bleaching shugowa tayi tana cin chew gam. idanunta duk sun jeme alamun wahala da shekaru sun bayyana.

Tsohuwar ta kalli Sumayyah da yan zuma take kuka, ta zauna kusa da ita.“Ki daina kuka, yarinya. Idan kika yi kuka anan, Zaki mutu cikin ƙunci da hawaye. Kin riga shigo inda mutane ke haɗu da kaddara.”
Chapter 6 · 0% Book details