← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 35

Sashe 4

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda ya nuna isa da cewa shiga malam ne na gaske sanan ya yi wa Su Alhaji Ɗan Dubai bazara yasa shi cokewa ya bawa Yusuf izini yaje ya taho dasu,yana zuwa Yusuf ya yi musu jagora, ya durƙusa gaban Alhaji Ɗan Dubai har ƙasa abin da ko malam baya yiwa ya ce.“Ga shi can Malam ɗin.”Alhaji Ɗan Dubai ya miƙe daga jikin motar da tulu ciki sa, ya ɗan gyara igar sa tare da cewa abokan cin mushe sa.“Alhaji Dollar, Alhaji Iri bisimillah”suna Isa gaban sa Alhaji Ɗan Dubai har da cire takalma kamar su haɗa baki suka ce“Assalamu alaikum Alaranma barka da warhaka!” ya tamkar mutumin ƙwarai.hannu Malam ya miƙa ciki Murya manya yace.“Wa alaikumus salam warahmatullah!”cike da nutsuwa, amma jikinsa har yanzu bai daina rawa ba“Wallahi Alhaji Ɗan Dubai nake gani tsaye a gaba na! Na dade ina addu’a Allah ya haɗa mu, yau kuma ga shi ya cika!”Sai da Alhaji Ɗan Dubai ya saba ƙato tubisa kamar me tsohon ciki kafi yace.“Alhamdulillah, Malam yau gashi Allah ya haɗa”

Hannu Kalma ta sake bashi "A...Almajiri malam dai ai nasha gani ziyarar da kake kaiwa Manyan Malama iri su Malami buzu da sauran su wane mu” Dariya Alhaji Ɗan dubai ya yi ya kiftawa Alhaji Dollar ido sanna yace.

"Allah gafarta Malam na zo ne da saƙo daga gwamati te makawa malamai wanda ake kaiwa gari gari dan inganta masallatai shine mukayi tambaya akace ai guri ka zamu zo.”wani iri Farin ciki ne ya kama Malam giɗaɗo yasan zai ci kuɗi afili kuma gemu sa ya shafa yana furta"Masha Allah, Allah ya yi albarka ai inda zamu riƙa samu mutane iri ku da duniya ta zauna lafiya 'yan Aljana iri ku basu da yawa.” kai suka jinji Alhaji Ɗan Dubai ya sake cewa.

"Allah gafarta Malam Amma kuma, akwai wata magana ta daban da nake son muyi a sirri.”
Malam giɗaɗo ya haɗiye miyau, ya ɗan sunkuyar da kai. “A’a, babu matsala, za mu iya shiga ciki.” a tunani sa wani mugun hasafi zai sake masa asiri saboda idon mutane ya bukaci su kebe guri guda.
Yusuf ya sa a gaba yana nuna musu hanya, yana ta murmushi saboda yasan wannan ce damar da zai kashi rabon sa.
Suna shiga, Alhaji Ɗan Dubai ya zauna a kan babbar kujera, yana dube-dube da ido irin na mashuran masu kuɗi.Ya ɗan ja numfashi, Malm yana zuwa kan wani kato buzu ya zauna tare da tankwashe kafafu sa.ya yi gyran murya da matsar da tawada da alkaliman da suke bahe akan buzu.

Nutsuwa Alhaji Ɗan Dubai ya yi shida amini sa sannan ya ce cikin ladabi da sai ka rantse mutumin kirki ne.
“Allah ya ja kwana, wannan yarinya da na gani a waje nan, wacce Yusuf ya ce ‘yar gidan ku ce…? Ta kace itama?”
Malam ya ɗan karkata kai, tare da tafiya dan nazari Alhaji Ɗan Dubai ya katse masa tunani da cewa.“Naji kamar kamar ya ce Sumayya ko sakeena.!!”Ya fada yana satar kallo Malam. Hannu Malma ya tafa“O..O.. Sumaiyya kenan itama yariyar Guri nace sai dai mahaifiyar bata da hankali zargi da muke itama abin ya shafe ta har tayi suna ma dan Wani sa'ilu sai kace gidan su 'Yar mahaukaciyya zava kawo kanan.”farin ciki ne ya cika zuciyar Alhaji Ɗan Dubai fall da da alamu bazai sha wahala ba guri samu abu da yake so. ya lumshe ido, ya dan jinjina kai yana murmushi.“Toh… jinƙai kenan,” ya ce, yana duban Malam da wani murmushi mai ma’ana.
“Allah sarki Allah gafarta,na lura akwai wani abu a cikin idonta… sai naga kamar tana ɗauke da wata hikima da ba kowace mace ke da ita ba.” ya tsaigata dan yaga yadda zasu ɗauki maganar tasa.Malam ya yi dariya kadan.“To ai duk hauka tana da nata hikimar, Alhaji. Amma dai ka bar wannan, meye saƙon da kake tafe da shi?”Alhaji Ɗan Dubai ya zaro wata envelope daga aljihun rigarsa. Ya ajiye a gaban Malam Sule, yana murmushi da ladabi.

“Wannan kuɗi ne na godiya, saboda addu’o’inku da taimakon ku da kuke yiwa malamai da almajirai. Kuma akwai wata ƙaramar bukata… amma sai in ka amince kuma akawai tari alkairi aciki.”
Malam Sule ya yi saurin ɗaga envelope ɗin da hannunsa yana dariya. “Subhanallah! Alhaji, kai fa mutum ne da Allah ya albarkace! Bana jin akawai abin da zaka roƙa baka damu ba..!”
Yusuf da yake gefe ya kalli envelope ɗin da idanu ji yake kamar ya fusgo ta da ido, yana taɗe harshensa.Alhaji Ɗan Dubai ya lumshe ido ya dan ɗaga kai. “Akwai wata ƙaramar magana da nake son mu yi game da waccan yarinya da ke waje…”
Ya ɗan ja numfashi ya ce cikin murya mai sanyi amma cike da mugunta: sai da gaban Malam da na Yusuf ya buga fatan su kar yace zai haɗa ta aure da iyali da gasu Lubna da Sadiya can a gida., kafi suyi dogo tunani sake jin muryar Alhaji Ɗan Dubai.
“Malam, ina son ka bar ni in ɗauke ta na duba ta a Legas. Akwai wata dama da nake ganin zata taimaka mata... kuma kai ma za ka amfana.”Malam Sule ya tsaya cak. Kalmar “ina son ka bar ni in ɗauke ta” ta ɗan girgiza shi a farko. Ya ɗan gyara zamansa yana duban Alhaji Ɗan Dubai, sai kuma ya saki murmushi fari ciki da yaji ba batu aure bane.
“Alhaji, ɗauka kuma? Kana nufin taimako kenan ko ya.....?”
Alhaji Ɗan Dubai ya yi murmushi irin na mutumin da ya saba wasa da hankali mutane.“Eh, taimako mana, Malam. Kamar yadda na faɗa maka- yarinyar tana da wata alama ta hankali da hikima, amma a karkashin hauka da talauci. Ina da wata makaranta ce ta matan marasa gata a Legas. Ina so in ɗauke komi Ni zan ɗau nauyi ta a can, zata samu kulawa, ta koya ilimi, kuma ta taimaka ma kanta. Ba komai bane illa taimako sanan kaima zaka samu sauƙi ci da iyali.”
Malam ya ɗan yi shiru. A ransa ya fara hasashen kuɗi, kuma idanunsa sun rufe da abin duniya. Ya kalli envelope ɗin da yake a gabansa.ko makaho yasan kuɗi ne ba nawasa ba acikin envelope dinnan.
Alhaji Ɗan Dubai ya ɗora da cewa.“Ka kwantar da hankalinka, Malam. Ba tare da wani matsala ba, zan ajiye maka abin da zai taimaka wajen kula da sauran yaran ka da kuma makarantar ka ta, tsangaya sannan zan turo wasu kudade daban don kula da da mahaifiyar ta wace kace tana da matsalar kwakwalwa.” sai Yanzu Malama ya samu damar
zaro ido gani Alhaji Ɗan Dubai ya sake zaro wata leda ɗauke da bandir ɗin kuɗi, ya ajiye a gefen kujera cikin nutsuwa.
Yusuf ya ji kamar ya fasa ihu saboda farin ciki. Idonsa yana kallo tamkar ɗan akuya da aka nuna masa gyaɗa.
Malam Sule ya haɗiye miyau, zuciyarsa tana rawa.

“Alhaji Ɗan Dubai, wallahi kai mai taimako ne. Ba zan taɓa hanaka ba. Amma dai yarinyar fa, tana da mahaifiya, ko da kuwa tana da tabin hankali. Dole ne na faɗa mata ko?..”

*Dan Allah shering saboda manzo Allah kar ku manta free ne aiki ku shine Comment like*
[10/30/2025, 4:56 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a

*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*

Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.

____________free book _page-4

Alhaji Ɗan Dubai ya yi dariya mai sautin makamar ta tsofafi bokaye yace."Malam, irinawannan yaran mahaukatan ai abin a tausaya musu ne?Ni dai kawai ka bani amincewa, sai in zo in ɗauke ta gobe da safe. Kuma na bar kuɗin da zai wadatar da mahaifiyar ta da dawainiyar haukan ta.”
Ya tura ledar kuɗin ɗari biyar x10- bundun miliyan biyar.Sai da Malam ya zabura kamar wanda aka haɗa masa shokin. Hannunsa ya fara rawa yana ƙoƙarin ɓoye farin cikin da ke ratsa zuciyarsa.
“Subhanallah! Alhaji Ɗan Dubai, wannan alheri ne da ba zan taɓa mantawa da shi ba.ainda ka barshi ma.”Yusuf da ke gefe ya ƙaraso da sauri yana cewa,“Alhaji, wallahi kai mutum ne mai hankali. Na dade ina addu’a Allah ya kawo mana kai cikin gidanmu sai gashi kazo.”
Alhaji Musa ya yi murmushi yana shafa gemunsa.“Na gode. To kai kuma, Yusuf, zan baka aljihun ka na musamman. Kai ne zaka tabbatar ta shirya gobe da safe. Kar kowa ya sani. Kasan irin fitinar da mata suke yi sai kaji ƙananu magan ganu.”
“Na gane, Alhaji,” Yusuf ya faɗa yana kwaɓe baki cikin murmushi.Da suka fita daga falon,Yusuf ya bi Alhajin da ido kamar mai kallo aljanna.“Wannan mutum, wallahi, ba kamar sauran mutane bane,” ya ce cikin zuciyarsa. Bayan su gama tsara yadda zasu gobe har baki mota Malam ya raka Alhaji Ɗan Dubai ya raka shi yana sheƙa godiya.

Da daddare, Malam Sule ya shiga ɗakinsa hankali sa akwamce irin na wanda Aljihu sa ya cika da kuɗi. Ya ɗan gyara rawaninsa, ya ɗaga hannu sama ya ce,
“Alhamdulillah! Allah kai mai azurta bawanka ne. Idan wannan yarinya ta tafi, to wani alheri a gare ni.”

Inna ce kwance bacci ya ɗauke ta da wuri saboda abinci da ta samu taci yau Malam da kanshi ya zuba musu abinci ya basu wanda sai da Sumayyah tayi mamaki. Bacci ta ya yi nisa ta fara suru tai kamar me tabi aljanu tace."Sumayyah… za su ɗauke ki… za su ɗauke ki daga haske zuwa duhu…”Sumayya da take gefe tana cin tuwo tsari ta cire hannu ta ta fara tofa mata addu'a da haka ta daina surutai ta ci gaba da bacci ta.Washe gari da safe da wuri, Yusuf ya tashi da sassafe fada ɗaki su Sumayyah tin daga nesa yake ƙwallah mata kira a zabure ta miƙe jikin ta na rawa tunani ta tayi wani laifi ne, a ƙofar ɗaki suka haɗu, ya ɗaure fuska kamar wani boss yace.“Sumayyah, yau Malam ya ce ki shirya, akwai wani Alhaji da yake son zai taimaka miki.za ki tafi ki zauna a wajen shi lilimi zaki kyauta batare da ƙwandalar Malam ba. Ai dama Malam yana son taimaka miki ko dan hali da mahaifiyar ki take ciki damace da babu.”
Sumayyah ta ɗago kai, idonta cike da tambaya. Muryar ta na rawa tace.
“Ni kuma Yaya Yusuf? Amma Inna tafa?.”Baki ya washe.
Chapter 4 · 0% Book details