← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 35

Sashe 28

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewat Ummu da take ta mase hawaye, Abi ne yayi ƙarfi halin cewa.

“ Doctor zamu iya shiga mu ganshi shi da matar tashi”

"Yariyar dai Yanzu ana kan yi mata ɗinki da ƙara mata ruwa zuwa ajima zaku shiga”

Godiya suka masa suka fita lokaci da suka fita aka fito da Ammar daga room ɗin gashi da aka shigar dashi ɗaki hutu aka kai shi.

Ɗakin hutu suka shiga gaba ɗaya, kowa zuciyarsa cike da raɗaɗi. Ammar yana kwance a kan gadon asibiti, na’urar numfashi na amsa aikinta, idanuwansa a akafe, fuskarsa ta rame fiye da yadda aka saba ganinsa. Ummu ta durƙusa gefen gadon, ta kama hannunsa duk biyu tana shafa shi tamkar.

“Ya Allah… Ammar ɗana, ka bashi iko cin wanan jarabawa” ta faɗa cikin kuka mai karya zuciya.
Abi kuwa yana tsaye gefe guda, idanuwansa sun cika da hawaye, gani Ammar kwace babu inda yake motsi aikin sa,amma da yake namiji ne dole ya riƙe kansa. Ya ɗora hannusa kan kafadar Ummu.
“Ki yi haƙuri Ummu, komai daga Allah yake, kina daɗa ɗaga masa hankali.”

A ɗakin daban kuma Sadiya tana kwance, ruwan drip na shiga jikinta a hankali. Baba Zulai zaune a gefenta tana karanta Ayatul Kursiyyu tare da face majina da baki hijab ɗinta, Yusuf kuwa yana yawo a ɗaki ya kai mari ya kai gwaro.

“Wannan wane irin jarabawa ne Wallahi Babar mu nafi tunanu wanan Yar Mahaukaciyar da sa hannu ta aciki ture ne wanana baza mu yarda ba” Yusuf ya faɗa yana girgiza kai. Baki Malam na kufa saboda Azabar yinwar da yake ji ya fito tun farar sabiya bai karya ba tasar cewa.

"Yusuf Fatana Kada Sadiya ta mutu duk wani buri na Ya dori akan yaro nan Allah yasa yaro nan ya riga ta tafiya ko masa mu gado”
Da Sauri Yusuf yace.

“Ameen dai Baban mu, Amma ban taɓa gani masifa iri wanan ba daren aurenta?”

Bayan wasu mintuna Nurse ta shigo ɗakin da Ammar yake kwance.
“Dan Allah lokaci ya yi, zamu kai shi ICU domin kulawa ta musamman.”

Miƙewa Ummu tayi ta riƙe hannun Ammar da ƙarfi kamar za a ƙwace mata shi.
“Allah Ya duba ka ya baka kafiya Don Allah ku kula min da shi, shi kaɗai nake da shi.”

Kai Nurse ta girgiza cike da tausayi.
“In sha Allahu, za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu.”

Suka tura gadon Ammar zuwa ICU, Ummu da Abi suna binsu a baya, sai da suka isa ƙofar room aka dakatar dasu aka rufe ƙofar.A Respect ‘yan sanda ne suke tattaunawa da D.P.O, suna rubuta bayanai, suna tambayar masu gadi, kowa yana ba da nasa labari cikin ruɗani.

Numfasawa D.P.O yayi Ya dubi S.P.

“Wannan ba fashi na dare kawai ba,Wannan shiri ne tun da dadewa.”
Abi da tsaiwar sa kenan ya kalleshi cike da tsoro.

“Shiri? Kana nufin akwai wanda ya san Ammar? Ko yake ƙulla masa wani mugu abu Tom wane zaiyi wa ammar haka?”

D.P.O ya ɗan ja numfashi.

“Za mu bincika komai. Daga maganin da ya sha, zuwa mutanen da suka shiga gidan.”
Ummu da ke tsaye gefe guda ta jikinta ya yi sanyi. Ta tuna mafarkin da ta yi a daren jiya. Hawaye suka sake gangaromata

“Ya Allah… ka nuna mana gaskiya, ka tona asirin masu mugunta.”

Dan-danan Labari ya yaɗu asibitin ya fara cika da jama’a. Kamar wutar daji, labarin abin da ya faru da Ammar da Sadiya ya watsu cikin dangi da abokai. Motoci manyan mutane suna jerin gwano ɗaya bayan ɗaya, zuciyoyi cike da fargaba.
Alhaji Ɗan Dubai ne ya shigo har da matar sa fusakar da gaba ɗaya ta gama bayyana tashi hankali yana tsaiwa ya kalli Abi.

“Abi, me ya faru ne, Allah yasa dai Ammar yana raye?” Alhaji Ɗan Dubai ya tambaya cikin rawar murya. Kamar wanda yake jira ya gunza ihu

“No ka kwantar da hankali ka AMMAR insha Allah zai tashi yana raye, kuma Alhamdulillah, amma yana cikin wani hali mai tsanani, Ammar yana bukatar addu'a mu.”

Suna ji haka, matar Alhaji Ahmed Ɗan Dubai ta saki kuka, tare da zauma kan kujerar tana bugun ƙirji.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji‘un! A daren aurensa kuma?wanne wace iri masifa ce Ita ina ita amrya ko tana wanne hali?”

Babu wanda ya kula ta saboda Da ‘yan uwan Ammar su fara zuwa ‘yan uwa na jini da na ne da wanda suke mazauna Kano haka dangi Ummu suma duk sun kewa asibiti,Kowa tambaya yake yi, kowa kuka yake yi, amma babu wanda ke da cikakkiyar amsa. Ummu tana zaune a kujera, hannunta a ɗauke da tasbihi, bakinta na motsi da zikiri, idanuwanta sun kumbura da kuka.
Ba da jimawa ba, daga ɓangaren Sadiya ma labari ya isa gasu Sumayyah da Baba Hauwa haka suka hauwo abin hawa suka zo Asibiti, Lubna da Sumayyah sunyi koka sosai dan sun shiga sunga Sadiya A halin da take cike ciki.

Karshe Nurse hana shiga tayi guri Sadiya.
“Dan Allah kuyi hakuri da fatan za a yi haƙuri, marar lafiyar tana bukatar hutawa.”

Wata daga cikin Innar Sadiya ta yi magana da murya mai cike da zafi, da masifa.

“Wane irin zalunci ne wannan?A dake mu kuma a hanamu kuka wallahi Allah ya tunawa Duk wanda yayiwa Sadiya Asiri?”

Sauran dangi suka amsa da Amee.
A gefe guda,manyan mutane ɓangare Ammar sun taru kusa da ICU. Wasu na addu’a, wasu na kuka, wasu kuma zuciyarsu ta cika da fushi. Wani ƙani Ummu mai Suna Masuwar yace.

“Wallahi duk wanda ya aikata wannan, aiki sai ya fuskanci fushin Allah!”
Abi ya ɗaga hannu ya ce.
“Ku kwantar da hankalinku. Wannan ba lokaci ba ne na hayaniya, lokaci ne na addu’a. Da Addu'a Allah ya tona musu Asiri ko suwaye”Da Ameen suka Ammsa, sanan kowa ya koma ga Ubangijinsa.

Alhaji Ɗan Dubai kam duk wanan haukar da yake bai kula da Sumayyah ba a tunani sa Sumayyah ce kwance buri sa Ya mutu shikenan buri sa ya gama cika ko yaji ta farfaɗo yaje ya faɗa mata shine sikar shigar ta wanan hali sanan ya karasa kashe ta...
[2/5, 11:40 AM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*

Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.

____________free book _page-28

*Kauye Gidaɗo*

Baba Hauwa ce da Lubna suka shirya don zuwa Asibitin Kofar ɗaki Su Sumayyah ta tsaya ta kira ta."Sumayyah ko zaki? ki fito muje kiga hali da take ciki?”kai ta ɗaga.

"Eh Baba zani bara na wanke kafa ta sai mutafi ”

Tom tace ta fita, Sumayyah tabi bayan ta wanke jikin ta tayi sanan ta saura kaya awaje ta samesu Sunjima sanan suka samu abu hawa.

Malam ne da Baba Zulai sai Doctor suke gudu zuwa room ɗin da sadiya take kwance kuka Baba Zulai take tana kwaɗa ihu suna zuwa kofar aka dakatar dasu Doctor yashiga gudanar da aiki sa. Sai da ya shafe 1 hours ya fito yana yakice gumu Malam ya kira lokacin ya yi dai-dai da Fitowar Abi daga room din da Ammar yake tare suka shiga Officer din Doctor sai da yayi rubuce-rubuce sanan ya dago ya kalle su.

“Da Farko ina me baku haƙuri domin yariyar nan ta gamu da Gang rape (ma'a fyaɗe na kungiya , ma'ana mazaje fiye da ɗaya sun haɗu sun tilasta wa mace yi abu ba tare da yardarta ba.)
Wanda ya haifar mata STIs ma'ana matsalar ƙwaƙwalwa,da yawan tsoro da firgici,”

Doctor na tsaigata zance sa Malam ya kurma ihu.

" Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun Shikenan Sadiya yanzu duk buri ki bazai cika ba Wallahi da zanga wanan mutane da Kashe su shine mafita agare Ni tsinanu na Ala....

"Assalamu alaikum Abi wai Wanan mutum shi kaɗai aka ilata yake tamana surutu baya gani Ammar ko tashi yar yar Gwal ce da duk zai shi...

"Dan Allah Alhaji Ahmed kayi shiri tariyar Abin a tausaya mata ne dama Haka Allah ya ƙaddara akanta wanan abu zai faru bakan marainiyar Allah wace Mahaifiyar ta Ta jingina da ita Sai gashi Sadiya ya Allah kabawa Sadiya Lafiya ka dub iri zalunci da akayi wa barwar ka Ka tona Asiri wanda suka aikata mata wanan mumunan aiki”

Ras gaban Alhaji Ɗan Dubai ya buga Muryar sa na rawa ya fara tambayar Abi.

"Alhaji..wai... Wai..me naji kana faɗa ne kana nufi dama Ammar ba Sumayyah ya aura ba wata ce daban?”

Kai ya jinjina.

"Tabbas Ammar ba ita ya aura a lokacin da Kuma je Ɗaura aure........Ni kuma na gargaɗi kowa kan kada a sanar da kowa barshi a haka”

" Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar³”

Sai da ya mai-maita sau uku sanan ya fita yana yarkata gumi yana zuwa respect suka hadu da Sumayyah da Baba Hauwa da Lubna da suke neman ida ɗaki Sadiya yake sai ga Gaban Alhaji Ɗan Dubai ya sake bugu gani Tabbas ba Sumayyah bace saboda kaɗuwa da tashi hankali baisan Lokaci da suka bar guri ba fita ya yi ya fara kiran number Dama duka uku ya ɗauka.

"Hallo....!hello..!! Dama ban taba sani kai mahaukaci kauye bane sai yau da kasan ba yariyar bace shine baka sanar dani Dama Wallahi ka guji haɗuwa ta dakai Sai na kashe ka sai ɗai-ɗaita rayiwar duk wani dangika tsinanene ɗan Haram”

Dariya Dama ya bushe da ita.

“Hhhh karya kake Ɗan Dubai na daka na ba da ruwa uban waye yasan yariyar in ba kaiba.”

"Dakata ƙarami ɗan iska duk abinda kaci nawa dai-dai da nera ɗaya ka dawo da abu na Nabaka nan da awa 2”

Dariya Dama ya sake bushewa ya yi, cikin kaukausar furci ya ce.

“Ahamed wallahi yadda aka n manaci ya mutum baya dawowa Tom naci kuɗi nan kasani duk yadda kakai da tauri rai guri kazo kuma duk wani shiri da zaka yi na riga ka yi shashashan banza da yofi”

"Haka kace Dama zan nuna ma Ni kwallo shege ne zan nuna maka na fika zafi kai kasani Ni rayiwar Lagos nayi kai ka faɗan ina kaje abariki.”

“Matseeeeee Shasha tsohon banza”

Yana faɗi haka Dama ya katse wayar. Kafa yayi yana juwa suka yi ido huɗu da Abi rassss kirji sa ya buga kame-kame zai fara Abi ya dakatar dashi da zaiwa.
Chapter 28 · 0% Book details