← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 35

Sashe 15

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****
******
Tafiya yake hankali kwance sai dai Yana cike da tausayi Inna Sumayya da son sani ya aka yi ido ta ya fashe. taya zai yiwa Hajiya bayani halin da yariyar nan take ciki, ciki ƙiyayar 'Yan uba.tsaki ya ja, ya shiga call ɗin number mahaifinsa sai dai bata shiga, Alamu ya nuna har yanzu bai sauka ba, sai da ya gama bucking ɗin duk wani abu da zai kaiwa Sumayyah da mahaifiyarta sannan ya nufi gida. Tun daga ƙofar parlour yake kwaɗa Sallama shuru babu kowa, sai dad-daɗan Ƙamshi wanda kullum haka Parlour mahaifiyar sa yake kasancewa, sai dai na yau ya ban-ba ta da ko yaushe dan Abin sa yau zai dira shiyasa gyran ya ban-banta dana ko yaushe. Kitchen ya nufa dan yasan yanzu Hajiya tana can.wani lace ne iya gani ka san sai sun Hajiyar, lemon green ne sai Flower's whit gyarare gashi nan har gado baya ta ko ina sheƙi yake yana zuwa ya rungume ta da saki mata lafiyaye peck a goshi. Juyowa tayi ciki yalwataciyar fara'a.

“Sannu da zuwa na zata zaka dawo min da ita.”Annuri fuskar sane ya ɗauke tunawa da halin da ya barta, kallo ɗaya Hajiya ta masa ta fuskanci akwai Matsala.Kafaɗar sa ta dafa.

"Ammar, ina fatan komi Lafiya in ce Babu matsala acan ɗin??”Iska ya furazar ya matsa kusa da Food flask cup ya ɗauka ya tsiyayi ruwan zafi,tea ya haɗa mara suga Sosai ya fara kurɓa.

"Ni Hajiya wai yaushe Abi zai shigo na duba tim har yanzu banji alamu zuwa sa ba.”kawar da zance yayi, ta riga tasan halin Ammar ba kowa ce matsala yake sauri faɗa ba matukar yana da ya ƙini zai iya gyra ta. Ammasar tambayar da ya mata ta bashi.“Bana ji zai haura 30 mintes bai sauka a Airport ba ka shirya da sauri zamu je tare.”

“Ok”yana faɗi haka ya fita zuwa nasa nasa part ɗin, Bathroom ya shiga ya faɗa bathtub ya juma yana wanka kamar bai yi wanka ba ɗazu, ya fito ƙugun da ɗaure da tawel sai da ya shafe jikin sa da Cram masu tsada da sa laushi fata duk da Allah ya wada tashi da laushi skin, amma yana amfani da mayukan gyran jiki.tsawa ya yi gaban waldrop yana tunani kayan da zai sa ya jima kafi ya zaɓi Trousers da T-shirt block tare da gyara sumarsa Sak asali Labanis ya bayyana a jikin sa diri da haiba ya sake bayyana nau'o'in turarika masu kashe zuciya yasa tare da ɗaura agogon diamond a tsintsiyar hannu sa cap yasa black da Sandal din ta takalmi baƙi. (Nuna OUMMU MUWADDAH sai da nace ma Tubarkallah masha Allah)

Taku yake iri na jarumai har ya ƙaraso Baban Parlour, phone ɗin sa ya ciro cikin aljaihu wando sa, bana ji mai Aka ce a ɗaya ɓangare, Ammar Ya lumshe ido kamar mai jin bacci."Tom Hajiya Ammar ɗinki dai yana Parlour yana jira”

Da haka ya gimtse kira ƙafar sa ya ɗauka ya ɗora saman Centar teble ya ƙaro Volume ɗin kiɗan wata waƙar Larabawa ce girgiɗa ƙafa yake tare da lumshe ido yana bin waƙar cikim ƙasan zuciyar sa ya shagala cikin wanan halin Hajiya ta fito har da siriri glass a fuskar ta duk da ta kai Shekaru 47 amma ɗauka zaka yi shekaru ta bai gaza 30 Year ba.tun da yaji ƙamshi turare ta ya buɗe ido.

“Masha Allah Yajiya anya Kawai mace mai tsafta da kyau iri Ummu na banji hakan a kwana kusa”Sumar kansa ta sosa tare da ɗan ya mutsata.“Ammar kar ka zama mai son kai, Ka sani 'Ya'ya da yawa zasu ƙalubalance ka”

Miƙewa ya yi ya kama hannu ta suka fara taku ciki isa“Hajiya gobe zan koma Giɗaɗo zan kai wa Sumayya saƙo”Dariya tayi tana fata Allah yasa abin da yake ranta ne yake shiri faruwa,a fili kuwa cewa tayi

“Allah ya kaimu, nima kafin azumi yazo zan je na duba ta”
Kai ya jinjina Suka fita Compound, Back seat suka zauna shida Hajiya driver ya zauna mazaunin sa.

******
*******
Ta jima cikin ɗaki Malam sanan ta fito tana tura ɗan kwali gaba goshi, waƙa take mai cike da shaguɓe.Baba zulai ta cilla mata harara"Hauwa ya naga kamar kina min wani gani-gani ko da magana.”Dariya tayi me cike da takaici.

“Wa..! Nina isa nace banten sarki ya yi ɓurtu, ai ido ne wa, kuma duk nisan dare gari zai waye Allah na tuba mun jima munaji kar kyaran ka...”

Fitowa Sumayya ce ta dakatar da Maganar da Baba Hauwa take ƙokarin furtawa. Da ƙyar sumayya ke tafiya shiru suka yi suna binta da kallo. Har ta gama shin fiɗa tabarmar a ƙofar ɗaki su,ciki ta koma ta kamo Inna ta zaunar da ita sannan ta fito da uwar bolar da take ɗaki, ta bayan gida ta fitar da ita ta watsar.

Cak ta tsaya gani Akwatu kayan da Hajiya ta bata an gama badali su Sadiya turmi uku Lubna turmi atamfa biyu Amina kuma Aka hada ta da Baba Hauwa turmi biyun lass ɗin da Hajiya ta bawa Sumayya a rage mata girman su, ta gano hannu Baba Zulai kala uku.

"Hauwa Amma yariyar nan ba ƙaramar makira bace, da wanan kayan gidan Ubanwa zata kaisu.”Harara Baba Hauawa ta wurgawa Sumayya."Hoho mata muguwa mai mugun hali, Dangi hauka da Aljanu”

"Babar mu don Allah,ki barmi wanan Lace ɗin Gobe naje kasuwa dashi”Cewar Sadiya da take ta faman jinjiga Baba Zulai. tsaki tayi.“Kinga fa Allah bazan baki ba, da yau da gobe duk Malam a ɗaki na yake so nake na gwangawaje lass ɗin nan ajikina ko na samu ladan Aure”Tana faɗa ta kara lass ɗin a saman ƙirjin ta.

Hawaye ne suka zubowa Sumayyah masu zafi, Zuciyar ta ta sake karaya, lokaci da ta hangi Inna ta na miƙa hannu ita ma abata, ƙoƙarin miƙewa Inna take da sauri ta Sumayya ta ƙara sa inda take ta goge Hawaye ta.

"Inna ba na hana ki riƙa miƙa hannu in kika ga abu a hannu wani ba, Ko so kike nayi kuka, ki bari zanje neman gwangwani madara in nasiyar Zan siya miki Atamfar sallah”A fili Inna ta nuna murnar ta, tana nuna jikin ta tare da alamu zata shafa hoda tayi kwalli kai Sumayya take ɗaga mata hawaye da take ƙoƙarin hana zubar sa ya sake zubo mata.maganar baba Zulai taji.

"Sadiya Dan Allah tashi ki azamin wutar nan ki zuba dadawa can Kin san Malam kamar kure yake guri nama yanzu in ya fara tsaya min aka kamar tsohon maye haka yake.”Dariya Sadiya tayi ta tashi tana waƙar Kawu ɗan sarki ta Ungollo na ciwo.

Lokaci da ake kiran sallah magari ba lokaci Farfesy Kayan ciki ya kammala, babban tire ta samo ta kasa shi kashe-kashe tare da zubawa Malam nasa a ƙaramar Samira, kowa kaso ɗaya aka bashi sai da kowa ya gama ɗauka Baba Zulai ta kwaɗawa Sumayyah kira da suke zaune Kamar kurame ita da Innar ta, Inna ce ma me yawan suru ita kaɗai.

"Sumayya..! Sumayyah..!!!”Shuru babu magana miƙewa tayi A zafafe ta tunkaro inda Sumayya take zaune tayi nisa ciki tunani rayuwa.Duka ta ɗana mata."Ke 'Yar mahaukaciya dan naga alama kinfi jin daɗi a kira da sunan ki kije ki ɗauka naki ne ke da uwar ki, naman bai yi afki ba shiyasa aka haɗa muku in kuma bakwa ci gaba takai mu”

Taji shigar dukan Sosai, jikinta na ɓari ta nufi in da nasu yake dan har Isakar tsakar gida ta tule shi da ganye maina duk ya fara tule shi da ƙura, ƙoƙarin ɗaukan faranti tayi Baba Hauwa ta daka mata tsawa."A jiye min faranti salon a zubami guba, ki kwashe a hannu ki, ki matsa ki bani guri.”

Ajiye tayi ta juya tana zuwa Inna ta fara miƙa mata hannu.“Sumayyah Zanci nama, zaki Bani Allah ina so zaki bani??”Hawaye ne ya cika Ido Sumayya tayi sauri gogewa da tafin hannuta, ta miƙa mata naman, kafin kace kwabo ta cinye shi. Jin-jiga kafaɗar Sumayyah tayi "Sumayyah ban ƙoshi ba, Allah zaki daɗa min Kinga fa yinwa nake ji kiyi Haƙuri Sumayya ki daɗami”Fashewa tayi da kuka ta faɗa jikin Inna.kuka take sai dai Babu ƙara ta juma ajikin ta Sanan ta ɗago kai.

"Inna kin manta da akwai samu akwai rashi? kinsan yanayi da muke ciki a gidan nan me yasa baza ki haƙuri da abin da kika samu ba”Turɓine fusaka Inna tayi wai itama tasan faɗa gani za tayi fushi yasa ta cewa.

"Gobe in na fita nayi aiki Sosai Nama zan fara sai miki kafi mu samu kuɗi ɗinki”kai ta hau kaɗawa tana murna da haka Malam ya shigo ya kora su ɗaki suna daga ciki suna jin hirar su har da su Sadiya da Iyaye su. Ciki farin ciki suke hira.

*Alhaji Ɗan Dubai*

Ko da ya tafi bai koma Lagos ba dan Business ɗunsa na safar mata ne yake kai shi Lagos ko aiki da da uban gidan sa ya tura sa. Safa da marwa yake ciki makeke Bedroom ɗinsa, Hajiya Fatiha matar sa ce da take kwance ta bisa da kallo."Alhaji lafiya naga tun da ka shigo banga walwalar kaba.?”Zama ya yi gefe Bed din kafin ya furzar da iska mai zafi“Kibari kawai Hajiya Fatiha Ban taɓa asara kamar na wanan Lokaci ba, Riba mai yawa ta tunkaro ni sai dai tsinane yaro nan Ammar ya lalata komai”
Tashi tayi daga kwanciyar da tayi ta dawo jikin sa."Ammar wane fa?”Ammar mana yaro Alhaji nawa”kafe shi da kallo ta yi.“kamar ya ban gane ba kamin bayani”kwashe komi ya yi ya faɗa mata. Ajiyar Zuciya ta sauke."Kenan yana da Alaƙa da ita kome?”

"Bana ce ba Amma wallahi sai na lalata rayuwar sa ba'a cin bashi na a zauna Lafiya sai na ɗai-ɗai ta shege Uban nan nata, dan shine kwallo shege,
Sai dai naga A-lamar tana so Ammar zanyi anfani da son da take masa na ruguza farin ciki ta, ban taɓa samu naƙasu aciki Kasuwanci na ba sai akan yariyar nan, naci buri a akanta Amma yaro nan har da min baraza nar Sallama daga guri aiki.”
Chapter 15 · 0% Book details