← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 35

Sashe 2

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Zuciyarta ta cika da tambayoyi da za su zama asalin labarinta.
Saboda a cikin shiru, akwai sirri.A cikin hawaye, akwai gaskiya.
Kuma a cikin wannan yarinya da ake kira “’Yar Mahaukaciya”, akwai ƙarfin da zai girgiza duniya.

*Comment lik da Shering shine zai karfafa min gwiwa dan Allah a Amin kara free Book ne amma nace ba kullum zan rika Update ba*
[10/28/2025, 1:15 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a

*📚 🌸 ‘YAR MAHAUKACIYYA🌸📚*

Mallaki:
Husaina S Abdullahi (Oummu Muwaddah)
📚©2025 -haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.

________________free book __page-2

Sai da tayi 'yan Addu'o'in da tasani,kafin ta kwanta.Rana ta tashi kamar yadda take tasowa kullum, amma ga Sumayyah, kowace rana sabuwar jarabawa ce. Haske bai taɓa zama alamar farin ciki a gare ta ba, sai dai tunasar da ita cewa ta sake tsallake wata rana cikin
wulakanci da rashin tausayi.

Da safe ta tashi da kyar, jiki babu ƙarfi, idanu wanta sun kumbura saboda kuka. Ta ɗauki bokitin ruwa ta nufi rijiya da take nesa da gidan su,tafiya take da kyar da dama jiya bawani abinci kirki ta ci ba. Hanyar rijiya ba mai nisa ba ce, amma a gare ta kamar tafiya cikin duhun da babu haske take. Ji take tamakar anayi mata yasa acikin ta, tun da ta doshi guri yaran da suke wasa,wasu na wucewa, suka fara tsaiwa suna kallonta suna dariya.“Yar mahaukaciya, ki kawo mana ruwa mu sha, kar ki yi dariya ki haukace mana, Aguri nan!”

Ta tsaya, ta ɗan kalli ƙasa, hawaye suka gangaro mata. Ta yi shiru, ta juya ta ci gaba da tafiya.lokaci da ta isa ta samu wasu matan ƙauye suna hira. Tana isowa, hirar ta tsaya. Kowa ya juyo yana kallonta da murmushin raini hankali.

“O Allah ya rabamu da hauka koda bana tiburan bane?” wata ta faɗa cikin dariya.Wata mai ɗauri ƙirji ta bigawa Sumayyah harara tare da cilla guga cikin rijiya tace., “Eh ai ita ce ‘yar da bata da uba. Ai Malam Sule ma yana gudunta bare mu kuma mutane gari,yo hauka yake zai sake bari tsatson sa ya biyu ta guri
mahaukaciya.”Da sauri
Sumayyah ta jingina da rijiyar, zuciyarta kamar zata tarwatse. Amma ta yi haƙuri. Ta hanana zuciyar ta shiga damuwa, cikin ranta taji wata zuciyar na ce mata “Ki yi haƙuri Sumayyah, rayuwa ba ta tsaya kan baƙin rana ba sai dai tana koyar da juriya.”

Bata iya ƙarasawa guri su ba har sai da suka gama nasu jan ruwan kafi ta janyo nata.Da ta koma gida, ta iske Baba Hauwa zaune tana ɗinki. Tana zuwa zata wuce ta ce.

“Ke kuma, wane irin jinkiri ne haka? Ko kin tsaya kina tattaunawa da mahaukata irin mahaifiyarki? Yo in ba hauka ba ina dalilin zama haka!”Sumayyah ta sunkuyar da kai, ta mika mata bokitin ruwa.Baba Zulai da take aikatau ɗin awara ta ce
“Allah ya ƙyauta, amma irin su wanan yaran ba su da albarka. Haka uwar, haka ‘ya.”babu wand ta tankawa bare su samu abin kai wa Malam ƙara.Da ta gaji ma ɗaki ta shiga abinta guri mahaifiyar ta.

Da yamma bayan ta gama ɗora wa Baba Zulai sanwa tuwo dare, ɗakin mahaifiyarta.Inna ta shiga tana zaune tana kallon sama, tana murmushi kamar tana magana da wanda ba kowa ke gani sa ba.“Inna ta..!,”Sumayyah ta ce cikin rauni.Inn ta juyo, ta ƙyalkyale da dariya, sannan ta kama hannunta.“Sumayyah, su sun manta, amma Allah bai manta ba kizo nayi maki wanka na goyaki na kaiki baki rami.”
Hawaye ta goge da bayan hannu takafi ta ce.

“Inna ta! me suke nufi idan suna cewa ba ni da uba? Ina ce Malam Giɗaɗo shine mahaifina?”Inna Sai da ta ƙarewa Sumayyah kallo kafin ta Ƙyal ƙyale da dariya tace“Sule Saurayi nane ya sai min kajal da janbaki kina so Na ara miki?"Inna ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta lumshe idanu.ta ɗora da cewa“Ki girma, ki sani da kanki. Gaskiya ba ta ɓoye har abada. Amma ki sani, wanda yake da gaskiya, sai ya sha wuya kafin ta bayyana.” kuka Sumayyah ta fashe da shi tare da cewa."Inna ta, na kasa gane wa,yau zaki magana da kyau ajima akasi ta Allah ka kawo sauƙi cikin rayiwar mahaifiyya ta ko nasan suwaye dangi ta.”

Tun daga wannan rana, tambayar “Wacece ita?” ta zama abin da ke damunta fiye da komai.
Ta daina jin zafi daga kalmar “’Yar mahaukaciya.”
Yanzu tana jin cewa wata rana, zata nuna musu cewa hauka bata gajiya bace, hauka na iya zama hikima da duniya ta kasa ganewa.

Da dare, lokacin da kowa ya kwanta,kasa bacci tayi a hankula ta buɗe ƙofar su ta fito ta zauna ƙarƙashin tsohuwar wata bishiyar kuka dake bayan gida ɗakin su.ta zauna ta ɗaga kanta samma Tana kallon sama wani siriri hawaye ne suka shiga gangaro mata cikin kasan zuciyar ta tace.

“Ya Allah, kai ka halicce ni, kai ka san dalilin da yasa ka saka ni cikin wannan gida. Idan akwai gaskiya, ka bayyana ta. Idan ni ba yar wulaƙanci bace, ka nuna min haske.”Sai da taji anna kiran Sallah ta maza ta faɗa ɗaki dan tasan yanzu Malam zai bi ɗaki-ɗaki yana tashi saboda sallah asuba.

Bayan kwana biyu yau ta kama ranar Litinin, duk yadda taso ta tafi makaranta akan lokaci bata tafi ba Sadiya da Lubna kuwa tun tuni su jima acan sai da ta gama gyara gidan da kwashe karan da Almajirai suke karatu dare kafi ta isa makaranta.

Suna zaune cikim aji Sabuwar malama ta shigo, sabuwar malamar da aka kawo daga birni,Malama Ruqayya, tun da ta shigo ta lura da yanayin Sumayyah. Tashi farko taji yariyar ta shiga ranta, kiran ta tayi bayan kowa ya fita break ta ce.

“Sumayyah, me yasa nake ganin kina da zafin zuciya amma kina ɓoyewa?”Sumayyah ta yi shiru, hawaye suka cika idonta.Malama Ruqayya ta sake magana cikin tausayawa.“Na san kaddara tana iya zama nauyi, amma Allah baya rubuta ciwo sai da magani. Ki ƙarfafa zuciyarki.”kai ta girgiza tare da aminta da maganar ta.sannan ta sallameta.Tunda tabar guru.Kalmar nan ta zama abin da Sumayyah ke maimaitawa a ranta kullum.

“Allah baya rubuta ciwo sai da magani.”
Sai dai tana tambayar kanta-a ina maganin nata yake?”haka suka koma ciki aji, duk da a kaso tamani bisa ɗari babu abin da Sumayyah take fuskanta a ciki karatun da ake musu.

Rana ta sake tashi a gidan da kalmar “adalci” ta dade da mutuwa.
Gidan da dariya ta wasu, ke nufin hawaye ga wasu.

A yau, an shirya babban liyafa a gidan Malam Sule.wanda bisa addu'a da Malam Sule ya yiwa wani Alhaji Musa mai da'awa kan wata kwangila da yake so ya samu buri sa ya cika shine ya haɗa musu Babbar liyafa.kowa ya shirya Sadiya da Lubna kamar sun shiga kanti ɗan kurma saboda tsabar ƙamshi, kwaliya kam har da su barbaɗa kumatu.
Ana jiran Alhaji Musa mai da'awa ya ƙaraso har da iyalin sa.

Baba Hauwa da Baba Zulai jikin su sai rawa yake burin sun bai wuce ko Sadiya da Lubna zasu dace ba guri yaran Alhaji musa mai da'awa.Ko tsinke ne ya faɗi sai su sa Sumayyah ta ɗauke, ko wanka sun hana tayi wai bazata yi wanka ba kar wani yace yana so. Itama bata damu ba dan bata jin za'a barta taje guri walima bare har ta ga wani yace yana sonta hasalima ita bata sha'awar aure wani me kuɗi.

Inna kuwa, Malam ne ya kulle ta da kanshi aɗaki wai kar ta zo ta kashe musu guri da wari, Hankali ta kwance jikinta yayi busu-busu da ƙasa tana waƙar da babu wanda ke fahimta.

Sumayyah tana ta hidima, tana ɗaukar abinci tana kaiwa Babbar falo Malam wanda sai ka ɗauka ba acikin gidan yake ba saboda tsabar haɗuwar da har da sol.Ba kowa yake shiga ɗaki ba sai Manyan mutane masu zuwa temako guri sa. Bayan ta kammala lokaci da take ƙoƙarin zama motar su ta ƙaraso babu wanda ya bi ta kanta guri tarbar Alhaji Musa mai da'awa da matar sa da samari yaran da guda uku, Baba Zulai da Baba Hauwa har da zubewa har ƙasa suna yiwa yaran ciki gaisuwa su kuma suna fusgewa waisu 'ya'yan manya.

Ko da ta gaji da jira, babu wanda ya lura da ita hada-hadarsu kawai suke.shawara ta yanke ta tafi ɗaki guri Innar ta Baba Hauwa ta fito daga cikin ɗaki tana washe baki kamar gonar audiga, Muryar ta har,har ɗewa take saboda sauri magana.

“Ke... tsohuwar..manya.. yanzu ..Allah kinan..? A nan naɗe kamar tsohuwar manya! Aikin banza in aka ce maka Mutum ba kanshi kallo ba. fa ka banu!”

Sumayyah ta ɗago kai cikin hawaye, ta ce cikin murya mai rauni,
“Baba Hauwa na yi kuskure ne? Ina tsaye ne ko zaku buƙaci wani abun kar ku kira kuji bana kusa”Baba
Zulai da ta biyo bayanta tana dariya, “Eh ai kin yi kuskure, kin haihu daga Rabi! Haka kawai, asalin ku kuskure,haka kawai kusa a riƙa kiran dangimu da masu cutar hauka!”

Da sauri Sumayyah ta rufe kunnenta da hannuwan ta, tana girgiza kai tace.
“Ya Allah, kai kaɗai ka isa, kai kaɗai ne mai ganin ɓoyayye.” ta sake buɗe ido ta da lokaci daya suka juya zuwa jajaye, ta ce
“Ya Allah maye laifina dan Na fito daga jikin mara lafiya?” tsaki suka buga Baba Zulai taja hannu baba Hauwa tace."Kin ga zo mu koma mar su san yana da wata 'yar baje ya lalace.

Da haka suka sake fadawa daki Malam, tana juyo muryar Alhaji musa da'awa yana cewa"Hajiya gashi kowa turmi biyu babu yawa”

Kamar Zasu kifa haka suka fara yiwa Alhaji musa godiya"Alhaji Allah ya saka ya kawo nasarori ya kaɗe hau da bala'i”Ciki isa Yake amsawa da haka suka miƙe zasu fita da sauri Baba Hauwa ta kaɗawa Yusuf ido tun da yaga ni ya gane me take nufi da sauri ya fita. A tsaye ya samu Sumayyah tana tsaye. Tsayawa ya yi daka mata tsawa “Ke tsohuwar muna fuka wato laɓe kika fara yi mana ko?” Jiki ta har rawa yake ta zube akan gwiwar ta ta fara magiya.
Chapter 2 · 0% Book details