← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 35

Sashe 16

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Hajiya Fatiha tayi "Wanan me sauƙine, mu fara raba alaƙar Ammar ɗin da ita sanan musa duniya ta juya mata baya ta rasa madafa kaga dole ta neme mu. Kuma bariki da bata so tayi dole sai tayi shi”Dariya Alhaji Ɗan Dubai ya yi mai sauti"Bana bukatar ta,a yanzu bayanta kawai nake so gani”Yana faɗi haka ya fita.

*Nasarawa*

Tunda suka shiga mota babu mai magana dama haka tafiya da Ammar take da wuya kaji shi yana yawan surutu, sai ma in da Hajiyar sa ne ko kuma Abin sa suke tafiya.suna isa Airport ɗin Malam Aminu Kano driver ya nemi guri packing din mota yagyra packing ciki nutsuwa suka fita, Ammar ya kama hannu hajiya suka fara tafiya sai da su kayi nisa sanan ya kalle ta.

"Hajiya Gobe aiki zai miki yawa nasa a kawo kan sa zaki gyra zan kaiwa Innar Sumayya”
"Allah yasa zamu gani Ammar sai dai ina so naji halin da yariyar nan take ciki da Mahaifiyar ta.”peck ya mata a goshi sanan yace.

“Ummu zan kai ki ma sai ki ganta, yanzu taya zan baki labari nida ba ɗan Jarida ba ko marubuci labarai ”kunnesa ta kama“Ba sai ka kai ni ba zansa drive ya kaini”

Suna gurin a tsaye Abi ya fitowa har da Manager da P.A ɗinsa da suri Ammar Ya faɗa jiki Balarabe mutun wanda shekaru ne kawai ya ban-banta shi da Ammar.

“Abi, ahla wa daula....kif kéinit l-tari’? Kteer mshta’lak.”
“Abi,Sannu da zuwa..Ya hanya? Na yi matuƙar kewark.”Bayan sa ya shafa tare da peck ɗinsa a hannu ciki lafazi yaran Labanis.
“Ya Ammar! hibib Albi..ana kaman mshta’lak.
El-hamdellah ‘a Saléme.”
“Ammar! Masoyin zuciyata...ni ma nayi kewara.”P.A da Manager da suke tare da Abi ne suka rusina suka gaida Hajiya. kallo Ammar suka yi shima suka gaida shi hannu ya ɗaga musu dan bai cika so yana magana da iyaye sa ana katse shi ba Abin ya dube shi.

"Jeet men America deghri ‘a Nigeria...‘anjad eshta’telkon kelkon.” Peck ya masa ba tare da ya sake ce masa komi ba.Abi ya ƙaraso waje Hajiya.

"kin kara kyau Kamar ba Ummu Ammaru ba gaskiya budurwa nan tana jin daɗi”Duka ta kai masa a ƙirji“Wallahi kasa naji kunya Ammar da P.A ɗinka suna guri baka ji nauyi sai?”
Hannu ta ya kama yasan dama sai ta sako zance Ammar yana guri,kullum bata son Abin da zai sa ta jin kunya Agaban yaro ta. Mota suka shiga Ammar ya zauna a for seat driver ya ɗauki hanya.

Yau yajima bai yi hira iri haka ba Bacci ne ya fara ɗaukar sa ajiki Abinsa kira ya shigo masa ƙaramin tsaki ya saki.sanan ya picking call ɗi.

“Hello Fu'ad”Banji mai aka ce a ɗaya ɓangare ba sai tashi da yayi daga jikin abin."Ok ka shigo dashi ina Parlour Hajiya”Katse kiran ya yi babu jimawa Fu'ad ya shigo yaro ne matashin baza su wuce sa'anni ba,Sai dai daga gani yaro Ammar ne gaisawa yayi da Abi ya gaida Hajiya Sannan ya ajiya Leda biyu ta viva.“Ranka ya dade duk an gyra sai dai a ƙara wanke wa”

“Oky Hajiya gashi ya kawo.Fu'ad kai shi cikin Freigd”Yana kaiwa Ammar Ya miƙe suka fita da Fu'ad.

Washe gari Tin da Hajiya tayi Sallah bata koma Bacci ba, tana kitchen tana aiki,
Aiki biyu ta haɗa dana Ammar dana Mahaifinsa Sosai aiki ya kacame mata Deluwa 'Yar aiki ta bata gari taje gani gida shikuma kuku tin da aka kamasa yana zuba musu guba aka kai shi virus bata sake naiman wani kuku ba, tace ta haƙura da mai girki duk wahalar aiki tace zata iya kayanta. Sai 11 Ammar ya fito cikim shiri sa yadi ne light Blue yasa, iri aikin hannu nan da hula zanna bukar ya yi kyau sosai, ƙamshi kawai yake zubawa.ɓurintu Hajiya ya ji a kitchen da sauri ya faɗa ta baya ya rungume ta.

“Sorry Hajiya ta na saki aiki Sorry”Kan sa ta shafa aiki ya zame mana jiki karka damu ɗana kayi break fast aiki ka ya kammala”Godiya ya mata ya koma parlo Tea ya sha sai chips ya goge bakin sa da Tissues sanan ya koma kitchen.

“Wow Hajiya wanan flask ɗinan ya yi min kyau”
"kayi addu'a matar ka tazo ma da iri sa,Ammar zo ka tafi time na ƙurewa Ban so dare a yayi maka a hanya”Godiya ya yi ya kira Madu mai gadi ya dauka masa Flask ya saka a cikin but ya mata sallama tare da cewa ta gaida Abi in ya fito ba zai jira ya fitowar saba.Tun da ya ɗauki hanya yake jin wani iri farin ciki na ratsa zuciyar sa yanayi Fusakar Sumayya da tafiyar da suka yi jiya yake tunawa, sa'i² ya saki murmurshi.

******
******
Tinda aka fito masallaci Sumaiyya ta fita daga ɗaki tsunma tasa ta ɗaure ƙofar gudu Inna kar ta fita bata ganta ba tayi wani guri.Bola bola take bi ko zata samu gwangwani madara sai dai yau kamar baki ta gaza samu har goma da rabi gwagwani uku ta samu bakin ta duk ya bushe har jiri take ji gashi takalmi ta da tazo dashi Sadiya ta ƙwace sai wani haɗu bauta tasa, shima saboda tsabar yawo da tayi ya tsinke leda tasa ta ɗaure dashi.Sha ɗaya da rabi ta taki sa'a ciki wata bola da take gefe rami gwagwanaye ne birjuk da Alamu ba'a juma da zubar da su ba kasa boye farin ciki ta tayi.

"Allahmdllhi Allah na gode maka Allah yasa kaltu mai Alala ta siya kan naira ashirin na samu kuɗi siya wa Inna ta Nama”
Ciki sauri ta fara zuba gwangwani ciki buhu ta wasu yara ne da aka musu break daga makarantar boko suna hango Sumayya, suka tsayar dariya ɗaya yayi dutse wuta ya ɗauka ya saita bayan Sumayya ba zato taji saukar dutse tasss a gadon bayan ta miƙewa tayi tare da gantsare wa hawaye masu zafi suka sulalo mata. Dariya yaran suka sa.“'Yar mahaukaciya Uwarki kema kin fara haukar ne naga kin fara bin bola kinaci leda”Ihu suka fara suna mata waƙa ga mahaukaciya 'Yar macukule, gani yaran sun fara ihu suna tula mata ƙasa, ya sata haƙura da kwashe ragowar gwangwani tabar guri duk da haka wasu sai da suka raka ta da gudu.

Tafiya take ido ta A rufe ji take kamar zata yanke jiki ta faɗi har Allah yasa ya sa ta ƙaraso gida, Ammar da yake waje jikin motar sa, gefe ɗaya motar da ta kawo kayan ɗaki ne da kayan abinci da ta riga shi yo gaba a gefe.Tana ƙoƙarin tashi babu wanda ta kula dashi sai kiran sunann ta da taji, muraya da bata taɓa zato sunan ta na da daɗi furta wa ba.

“Sumayyah....! ” Da ƙyar ta iya ɗaga Ido ta kalleshi, hannu sa da suke kan ƙirjin sa ya saki tsoro furgici ya cika shi iya jiya da ya Barta bata da maraba da mahaukaciya ciki ransa yace Anya Sumayyah da na bari jiya ce ko kuma wata da ban?”Jin bashi da amasa ya sake ɗagowa ya dube ta ido sune ya sarƙe da na juna wani iri yanayi ya shi ga,ya kasa tantace ainihi abu da yake ji akanta. Taku ya yi kusa da ita.

“Wannan duk na maye, Maye wanna ajikin ki,I na kuma kika je yanzu da safiyar nan??”Hawaye ta fara Numfashi ta yana ƙoƙarin ɗaukewa kasa jurewa ya yi ya fusgo ta ta faɗo jikin sa kuka ta fashe dashi, ba tare da tsantsamin ƙazantar da take jikin taba ya sake yi mata masauki akan kirjin sa yana shafa bayan ta alamu rarrashi.........
[11/23/2025, 4:27 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a

*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*

Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.

____________free book _page-13

Ga nin yadda kuka ta ke ƙara tsananta ne ya sa Ammar lumshe ido, zuciyarsa na kai komo tamkar ana murɗa ta. Wani irin tausayinta ya sake shigar sa, ya ji tamkar ya ɓoye ta a cikin kirjinsa har abada. Sai da ya jira kuka ya lafa kaɗan kafin ya matsar da ita gefe, ya kalli fuskarta a hankali.
“Sumayyah… me ya faru? Waye ya miki haka?”
Kallon da ta yi masa ba irin kallo bane na yau da Kullu ji take kamar ana daɗa Ƙawata mata fusakar sa Sai dai tasan Ya mata nisan da bata isa tasa a ran ta zai so ta ko ya ƙaunace taba.

Da sauri ta kauda kai tana share hawayen da ya ƙi tsayawa.
“Ba komai… kawai na gaji ne.”
Ammar ya girgiza kai, idosa ya ƙanƙance suka sauya.launi izuwa ja.
"Har tsawon yaushe zaki juri yi min karya? Sumayyah...! Ni ban zo nan don ki rikita ni ba ko Na zama silar shiga tsakani ki da dangi kiba. Ki sani duk abinda yake damunki, na san akwai wanda ya haddasa hakan kuma bazan iya shuru Na zuba miki ido ba ki duba jikin ki jiya ba haka Na barki ba.”yana Faɗi ya kafeta da Sihirtatu idanunsa.
Shiru ta yi,ta kama kallon ƙasa. Sai bayan wasu sakanni tayi ƙoƙarin raba jikinta daga nashi.

“Dan Allah ka barni… Zan je in duba Inna tun kafi Asuba Na fita nasan yanzu Yinwa take ji. Kuma In yaya Yusuf Ko Baba ya ganni da kai a haka Sai ya dake ni ya min faɗa…”
Zai yi magana,malam ya yi Sallama daga cikin, idon sa ya ci Farin kwalli, sauya sallon magana ya yi kamar ta tsofaffin waliye."To...to Ammar Ke tafe kuma kaƙi shiga ciki Ke Mai yasa bakya rabo da sakarci”Magana zata yi Ammar ya dakatar da ita.“Ni ne ban shiga ba, kayan nan na Mamar Sumayya ne ina so a naimo wanda zasu saka Na biya su”
Chapter 16 · 0% Book details