← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 35

Sashe 13

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa ƙarasa zagi da ya ɗako yayi saboda wanda ya gani agaban sa.Ɗan A tajiri mai kuɗi nan wanda Duniya take Alfahari dashi (Ammar Sheikh Kareem Al-Labban)Mashahurin attajiri.An san sa a ko’ina saboda yalwar arziki da sirrin
kasuwanci.yana tsaye kamar bashi ba,ya harɗe hannu sa, murya na rawa ya fara magana ciki ƙinƙina.

"Ammar ɗana kaine anan?Me ya kawo ka wanan kauye maye Alaƙa ka da wanan mutanan??”

Ɗaure fusak yayi kamar bai taɓa dariya ba“Ni zan tambaye ka me ya haɗa ka da ƙanwata ka sani ko scend ɗaya ka sake tamakar ka sallami kanka daga guri aiki ne bana ji akawai wanda zai mai daka matsayi da kake kai.”

Zubewa Alhaji Ɗan Dubai yayi gwiwa har ƙasa.“Ɗana Ammar ka teamka,kamin rai wallahi Alhaji shine gatana Aiki nan shine gatana ba..wai...

"Shut up your mouth here. Kasan da haka kake aikata haramci kana safara yara ƙanana kai Guba ne a cikin al'uma, karka kuma min magana in kuwa ka sake kasani Wallahi..! wallahi..!! Wallahi..!!! Ka kori kanka”

Da haka Ammar bai sake cewa komi ba sai motar sa da ya nuna masa.Takalman sa Alhaji Ɗan Dubai ya kwasa a hannu ya shige mota tare da bari layi da Gudu. Sai A lokaci Yusuf ya saɗaɗa kusa da Malam tare da yi masa magana cikin raɗa.

"Malam yariyar nan fa ta sake zuwa da Alkairi kasan wanan yaro waye kuwa?”Kai Malam ya girgiza yana kafe Ammar da kallon kamar wanda zai gudu ya barsa.

"Malam Maifinsa hata ƙasashe waje so suke su kulla kasunci dashi Ai nasan kana ji Sheikh Kareem Al-Labbani
Mashahurin attajiri nan a rediyo ko?”Malam ya daga kai jiki sa yana rawa kamar mazari Yusuf ya sake cewa.

"Tom wanan yaro da kake gani zubi Larabawa ɗansa ne wasu na cewa shi kaɗaine ɗansa aduniya wasu kuma sunce yana da ƙanwa”

Tun kan Yusuf ya rufe baki Malm ya zube a gaban Ammar."Sannu da zuwa! Yanzu kake tafe? Ke Sumayya dan Ubanki tarbiyar da na baƙi kenan kina gani ɓaƙo ki barshi a waje?”Tunda Malam ya fara Zuba, Ammar yake binsa da ƙallo yaga Son Abin duniya a ido Malam yaga tsantsagaro son kai a tatare dashi.

Sumayya ce ta ƙaraso inda Baba ya zube kamar kayan wanki ido nan yaci uban farin kwali kamar tsoho kwarto."Yace ka shiga.”

Kamar bazai magana ba, bayan wasu mintes ya dubeta“Ina Innar taki take?”yana faɗa ya sake tsuke baki sa gulma Jama'a suka fara.

"Kai kunji 'Yar mahaukaciyya ta yowa Balarabe asiri ya biyo ta har Ƙauye Giɗaɗo yana neman Mahaukaciyar Uwar ta”Duk iri surutu da suke yana jinsu amma bai ce musu uffan ba.Malam naji haka ya miƙe “tashi muje ciki dama tun yau kwana biyu muke nema ta Wallahi ko sama ko ƙasa Mun rasa ta, ai kasan Mahaukata da Ɗan banzan yawo tom ai kan nasu ne ba ɗaya ba duk nisan guri haukarsu gaya mus.....

Bai kai ƙarshe ba Sumayyah ta tafi luuuuuu zata faɗi sumamiya.

***
Kwanan Inna biyu a gidan su Tanimu ta samu kulawa Sosai kuma ido ta ya warke babu kumburin sai dai bata gani da ido ɗaya dan ƙwayar ido ta fashe, Abinka da cutar mara Lafiya hakan bai wani ɗaga mata hankali ba Inna Zuwaiara ce ta fita gidan Baban ɗanta Babandi Sai Tanimu kawai ta bari a gidan. Surutu kawai Inna take wanda baka gane mai take nufi shikuma yana duba takardu makarantar sa sai dai ƙirjin sa yana yawan bugawa ya rasa dalili haka.

Kafi Baba malam ya taɓa ta tuni Ammar ya ɗauke ta, ya kalli Malam."Ka nuna min ɗaki Mahaifiyar ta zan kaita can”

Dukan uku-uku ƙurji Malam ya shiga yi dan zai iya rantse wa da Allah tun da Sumayya tasa ƙafa ta fice babu wanda ya ƙara tura kansa ciki. Jikinsa na ɓari suka kutsa ciki gidan,Baba Hauwa ce ke wanki jikin tulu ruwa gani mutun ya shigo Salam daga kasan maƙoshi yasa ta miƙewa tare da dafe ƙirji.

"Wa'innahu Sulaimanu Wa'innahu..

"Ke sakarai Shasahar mutun ne Ba Aljani ba, kina nufi Akwai wani sheɗani da zai iya tun karan Gidan Malma Sule batare da Ayar Allah ta kona shiba, Tom wanan da kike gani babban mutum ne,baƙo Sumayyah ne.”Malam ya faɗa tare da nunawa Ammar ɗaki,tsaki ta doka musu.

"Matsee Yaya Zulai kizo kiga wani Iko Allah 'Yar Mahaukaciya ta jawo mai jan kunuwa”Da gudu Baba Zulai ta fito zani a hannu. Lokaci da ta fito Ammar ya juya musu baya ya shigar da Sumayya cikin ɗaƙi.Kasa jurewa tayi tabi bayan sa daga Window ta tsaya tana leƙa su.

Ammar yana zuwa ya shinfiɗar da ita kan ya galgalaliyar tabarma ido sa har ya canja launi ya ɗago ya kalli Yusuf"Inaso Mahaifiyar ta ta dawo kafi ta farfaɗo ko nawa ne zan baka, Abani ruwa”

Da gudu Yusuf ya fita har yana Turai Baba Zulai. Saboda tsabar kiɗima zaici kuɗi.tunda ya fita yake falfala gudu bashi ya tsaya ba sai atsakar gidan Su Tanimu yana zuwa ya fara kurma wa Inna kira.Inna da take gefe a zaune, ta miƙe ta koma bayan Tanimu tana kuka."A'a baza niba zai zaneni baza niba”

Ran Tanimu ne ya ɓaci“Kar ki damu babu Uban da ya isa ya fitar dake daga gidan nan.”Yana fadi haka ya kama hannu ta suka fita taskar gida. Yusuf yana tsaye ya zuba uban doro.yana Gani Inna ya tafi,Hannunta ya kama"Zo mutafi gida Ga shegiyar yar kican mai jaye jaye maza ta....

Jin hanunta ko motsawa baiba yasa shi waiga wa Tanimu ya gani ya ruƙe mata hannu."Babu inda zata duk lokaci da tatashi gani ta tazo ta ganta anan gidan Amma baza ta sake shiga wacan baƙi gidan naku ba marasa mutunci azzalumai.....

Mari Yusuf ya dauke tanimu dashi, ciki zafi nama Tanimu ya rama ko kawa ce ta kaure musu ciki Jim zafi Yusuf ya fara ihu.

"Wayo jama kuzo ku taimaka min Tanimu zaiwa matar babana faɗe,babu mutane a gari ne dan Allah ku fito kar ku bari yaci mutunci aure”

Ta ko ina mutane suka riƙa shigowa Abinka da kar-kara har da masu Sandina kamar 'yan farauta, batare da bincike ba suka rufe Tanimu da duka har suka far fasa masa jiki.

Inna Zuwaiara da ta tunkari gidan taji hayani ta kaure yasa ta faɗa da gudu, Fuskar Tanimu ta gani duk an bubuge ta har da jini sallati tasa ta tura kai cikim mutane tare da bawa ɗanta kariya, cikin hikima da dabara tayi musu bayanin, zagi Yusuf suka fara gani reshe yana neman juyewa da mujiya yasa shi Sulalewa ya gudu.

Lokacin da Ta koma Sumayyah ta farfaɗo kalo kalo Suka fara da Ammar da Yusuf Malam ya gane tambayar Yusuf yake so yi amma girman kai tsiya ya hana shi magana cewar Malam.

"Kai yusuf Ina ita Rabi take?”Kalar tausayi ya koma"Wallahi Baban mu Tanumi ya hana kuma da duk kan Alamu ɗan Isakan yaro nan akwai manufar sa akan ta shiyasa duk iri dukan da aka masa ya hana na taho...

"Muje ka kaini gidan”Ammar ya faɗa. zubar Sumayyah ta miƙe"Nima zani saboda ya san nice na dawo zaifi yarda”

Su Huɗu suka nufi gidan Su Tanimu Malam,Yusuf, Ammar,sai Sumayya. Tun daga waje Malam Sule yake rafka Sallama har Inna Zuwaiara ta amsa tare da ratayo mayafi atamfa ta fito gani Malam yasa ta zubewa har ƙasa tana gaida su jikin ta har rawa yake,Saboda A ƙauye Giɗaɗo Malam tamakar Sahabi haka suka ɗauke shi duk abin da ya furta Umarni ne a guri mutane Ƙauye. da hannu ya nuna Inna Zuwaiara.

"Tashi Anan tshuwar banza ni zaki ci Ammana Tom ki sani ina so Rabi kuma yau sai na kwana akan buzu, za kusan Ba'a taɓa Malami soro,a wanye lafiya sakarya mara rabo”

Jikin inna Zuwaiara na ɓari ta fara bashi haƙuru."Ka temaka kayi haƙuri Wallahi babu komi a zuciyar Tanimu sai alkairi ka san....

"Inna babu an fani ki bashi haƙuri Don Allah ki tashi iri wanan malamai iri sune Ake janyo harshe su ayi..

Saukar Carbi Malam yaji a hannu sa."Allah wadaran da sami ɗa mara tarbiya iri ka Zuwaira kinyi Asara haihuwa.”

Malam ya faɗa yana gyra zaman asuwaki bakina. Zai sake janyo masa riga Ammar ya ɗaga musu Hannu."Stop, you know that I'm not going to sleep tonight.Ku fito da ita Bazan jure shirme ku ba”

Sai Yanzu Tanimu ya lura da Ammar da ke tsaye Wani iri kwarji ya masa lokaci da ya kalli cikin kwayar idon sa. murya na rawa yace.

"Tana ciki ɗaki”Taku Ammar ya fara kamar yasan gidan. Bai san me yasa yake buri yaga matar ba, ƙaunar matar ta shiga ransa.bayan sa suka bi hata Sumayya bayan Ammar tabi. A fili tsakar gidan ya tsaya yana wara ido Tanimu ya tunkaro ɗaki da yake bangare gabas mukulli yasa ya buɗe ya shiga ya kamo hannu Inna, Sumayya na ɗaga ido ta hango Inna, taga ido ɗaya babu wani iri ihu tasa ta zura da gudu ta rungume Innarta tana wani iri kuka mai gigi ta zunciyya...

*Ayi hakur Rashi Comments yasa gwiwa ta take sanyi da kuna comments zan iya Update sau biyu arana in kun gyara har Read more zanke yi da yawa*
[11/18/2025, 6:25 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a

*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*

Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.

____________free book _page-11

Ina na gani ta ta tafar hawaye ta ido ɗaya tana shafa Fusakar ta cikin kuka take cewa"Sumayyah tace wanan ta dawo, Sumayyah zo na goya ki mu tafi gida?”Ƙara rungume ta tayi tana kuka.“Me ya sameki Inna ta?waye ya ji miki ciwo Wallahi bazan yafewa kaina ba nice naja miki da inanan da duk haka bata faru da keba”Babu wanda ya iya magana sai malam da ya kaɗe Malin-malin ɗinsa yana taku ciki taka iri ta malamai na gari yaje har inda suke.

" 'Yata Sumayya tsautsayi ne tashi muje gida yanzu sai akaita asibiti dama mai yin jiyar ta aka rasa tunda gaki kinzo ba shike nan ba”Da wani iri kallo Mamaki ta bishi. Murya ta narawa.
Chapter 13 · 0% Book details