← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 35

Sashe 29

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhaji Ahmed ko kaga Fu'at jiki Ammar ne ya motsa wai karkarwa yake zasu shiga dashi ICU Shine na fito ne mansa.”

Idanuwan sa ya Lumshe tare da saki wata ajiyar zuciya.ya saki murmushi godiya da Allah.

"A'A Alhaji ai tun da mukazo ban sake gani sa Amma Alhaji har yazu ina jinjina lamari nan yanzu Ammar ya auri wata ba Sumayyah ace nakasa samu labari.

Batare Da Abi ya tanka masa ba ya koma cikin hospital yabar sa yana bige-bige waya.

Bayan Sun Sumayyah sun fita daga gida babu jumawa Ɗaki Innar Sumayyah da ya tsage ya fara buɗewa,babu kowa a gidan sai Inna ciki hukunci Ubangiji gaban dagi ya shafece ya zube, ba tare da ya danne kowa ba ihu Inna take na kiran sunan sumayya da haka moƙota suka riƙa shigowa dan temaka mata wasu matasa ne guda biyu suka fitar da Inna gidin maina tare shifiɗa mata buhu ta zauna. Khalil ne ya shigo Baba Hauwa ya kira ya sanar da ita abin da ke faru Umarni ta bashi yakai Inna ɗaki ta, sanan su kwashe buliluka su kaisu gefe guda da haka suka yi sallama bata sanar da Sumayyah gudu karta ɗaga hankali ta.

Tare da maƙota aka rika fitar da kasar da har suka kwashe tass shawar suka yanke su haƙa fandisho kafi Malam ya dawo zaiji daɗi haka. Haka kuwa sunayi dan danan da Almajiran Malam suka fara haka ana ciki haƙan Ililu Almajiri Malma ya haƙo wata leda mai rubutu har da turare a ciki babu wanda ya sanarwa ya zare ya zura cikin aljihu sa ya fita, a babban zo zaure ya tsaya ya fito da takar dar takarda ce ta farraƙu mai dauke da sunan Ammar da Sumayyah salati yake yana jingina rashi imani na Babba Zulai sai gashi Allah ya sakawa Sumayyah abin da suka aikata ya koma kansu.

Gabaɗa yan gidan Malam ne a zaune a respect kowa zance zuci yake wani na Aiyana alkairi wasu akasin haka Nurses ce ta shigo.

“Ina 'yan uwan Sadiya zaku iya shiga ta farfaɗo , Amma dan Allah banda yawan surutu.”

Hamdallah sukayi suka tafi jiki babu ƙwari, tun da suka shiga Sadiya take zubar da hawaye, Malam da Baba Zulai ne jiki gado suna aiki yi mata saunu, ciki harɗewa murya ta fara kiran sunan Sumayya.

"Sumayyah zonan.. Zonan dan Allah?”Jiki babu gwari Sumayyah ta ƙara sa baki gado hannu ta miƙa mata.

“Sadiya Yajiki naki Allah ya baki lafiya Insha Allah zaki warke ki koma gidan ki ciki Aminci”

Katse ta tayi da cewa.

“Sumayya ba wanan nake bukata ba yafiyar ki nake nema da ta mahaifiyar ku na sani mun cutar daku ko iya hakin ku bazai bari na rayu ciki salama”

Kuka Sumayyah ta fara.

"A'a Sadiya ni bantaba ruƙe ki araina ba Wallahi na yafe miki har abada Allah ya baki lafiya kijin”

Goge hawaye ta tayi tace.

"Dan Allah in na mutum ki auri Ammar dama miji kine ba nawa ba,muka shiga muka fita Ni da Batun sai da muka raba gashi na aure shirye sai dai haka bai zame min alkairi ba”

Da gudu Sumayyah ta fita tana kuka kallo ta Ya maida kan Baba Zulai.

"Babarmu dan Allah ki tuba ki koma ga Allah wallahi wanan ishara ce Allah ya nuna mana tun anan duniya mun azabat da Innar Sumayyah da Sumayyah mun hana tayi rayiwar jin dadi yau gashi muda muke gani mun samu duniyar bata da Ana fani a dare Aurena agaban miji da na aura maza bakwai sunyi min faɗe sun yiwa zuciya ta baban ila wanda mune mukajawa kanku zunibi da muka aikata ne yake biyar mu, kisani ki da zan rayu sau dari zan mutum sauri saboda mijin da na aura zai riƙa kallo na da wanan abi duk da nasan bama rayuwa zan yiba.

Kuka Babba Zulai take tana kifta mata ido, Murmushi takaici Sadiya tayi.

“Babanmu kaine kashi bayan duk wani abu da muke aikatawa kaine ka daure mana gidan muci zarafi baiwar Allah nan tun da na taso ban taba gani kayi wa Inna kallo mace ba baka taɓa yiwa Sumayyah kallo 'yar da ka haifa ta a ciki kaba, kaine silar ciwo Inna, kaine ka wargaza gidan ka da kanka Shim wai wane iri uba muke dashi da yake ƙirƙiran malami kaci Ammar mahaifi Inna tabba Allah bazai barkuba.”

Tana faɗi haka ta fara firgita tana fisge-fishe da haka doctor ya kora su waje.

Bayan sati ɗaya Allahmmdullilah jiki Ammar kullu kara samu sauƙi yake dan Har likita aka kira daga waje har ya fara sarrafa jikin sa kuma yana iya furta ɗai-ɗai, Doctor ya kira Ummu da Fabi da Fu'at da zai riƙa kula dashi gida zaune suke suna jiran cewar likita. Bayan sun gaisa ya fara gargaɗi da cewa.

"Da fargo sai mugodewa Allah subhanahu wata'ala domin Ammar ya auna arziki ba karami ba sai dai ina gargaɗi ku, ba kowane abinci zaku riƙa bashi ba sai wanda muka umarce ku dashi. Kamar.Shayi mara kauri,Pap/custard, sai shinkafa mai laushi hankali turawa, kayan lambu, ku guji mai maiyawa aciki, da Yaji, abinci mai nauyi har sai mu sake dubawa”

Godiya suka yiwa doctor sanan ya dauko wata farar takarda zan rubta wanan magunguna sai a karni a pamis zaki riƙa bashi Vitamins (B-complex)saboda taimako jijoyoyi, da kuma kariya daga ciwo hanta da koda.zamu haɗa ku da kwarare likita wanda zai riƙa masa gwaji (monitoring& tests) da Blood test, Urine test,ECG, CT-EEG, wanda bama fata , insha Allah nan da Wani lokaci indai abin dokar likita after 1 month ma zai dawo dai-dai.”

Hannu Abi ya bashi sanan ya nufasa yace.

"Doctor ita fa yariyar naji kace ta haɗu da tsoron da firgici kuma har yanzu banji kuna faɗi mataki da Za'a ɗauka na gargawa ba....
[2/5, 1:09 PM] OUMMU MUWADDAH: *📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*

Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.

____________free book _page-29

Maganar ta domi Allah sai mun haɗa da rokon Allah cutar wace an riga an zutar da ita ba'yi reping ɗinta dan ta rayuwa ba ayin ne dan ta rasa rayuwar ta gaba ɗaya sai dai muna baki ƙokarin mu insha Allah zata warware baki ɗaya”

Tashi sukayi jiki babu kwari, sai da suka shiga ɗaki Sadiya suka mata yaji sanan suka miƙe kamar daga Sama suka ji maganar Sadiya.

"Maman Ammar...!!”Da Sauri Ummu ta dawo dan gaba ɗaya tausayi Sadiya take gani take kamar Aure Ammar ne ya ja mata.zama yayi ta kama hannu sadiya.

"Ɗiya ta Sadiya me ya faru kina son wani abune?”

Shirin hawaye da ya gangaro mata ta sa gefe hannu ta ta goge.

“bana son komi sai neman gafara Ammar na mucutar da shi mun rabashi da wace yake so yake kauna mun rabashi da farin cikin dan Allah ko bana raye ina neman Alfarma ki roƙamin gafara guri sa,.”da sauri Ummu ta rungume ta wasu hawaye masu zafi ta goge ta sau saita murya.

“kar ki damu insha Allah zaki tashi ki koma ɗaki ki, kuma ki Sani tun kafin zuwan mu Duniya Allah ya riga ya rubuta al'amari sa wanda babu wanda ya isa ya goge kisani da ke Da Ammar da Sumayyah wanan zane ƙaddara kune dole kuma sai ya faru, babu wanda ya isa ya goge ki ne mi. Gafara guri Allah maji roƙo bayi sa insah Allah zai yafe miki, Allah yayafe mana baki ɗaya”

Kai ta jijina Ummu ta miƙe ta dubi Baba Zulai.

"Yanzu Fu'at zai kawo muku abinci Zuwa Yamma dan dawo”

Godiya tayi da Sa albaka sanan Ummu tabi Abi mota wance Har da AMMAR aciki.

Tunda da suka shiga mota abubuwa suke dawo masa sabani Hoton Sumayyah yake dawo masa gaban sa na tsanan ta faɗuwa sai dai ya kasa manya lokaci da yake cewa Sadiya yake so ba Sumayyah ba wani waye ne ya zubo masa wanda Fu'at ne ya lura da hakan ƙasa yayi da Muryar yace.

“yaya dai ko jikin ne?”

Kauda kasa gefe yayi dan baya bumatar jin komo daga baki kowa buri sa suje gida. Su Abi na fita Sumayyah da Lubna suka shigo cikin Asibiti lokaci da suke shiga ɗaki da Sadiya take Lokacin Babba Zulai ta fara rafka Sallati.

“ Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun hassbinallahu wani'imar wakil ƙaluu Inaalillahi wa Inna ilahi rajuun me zan gano Sadiya..! Sadiya dan Allah ki tashi kar ki mutu mi barni wallahi duk Ni najawo don Abun duniya na da gani cewa Sumayyah naza ta hutaba gashi na kashe 'yata da kaina”

Da gudu Sumayyah da Lubna suka ƙarasa cikin ɗaki gani Sadiya a sankame ido ta akafe tana kalli saman ɗaki zaka san tafiya tayi nisa Lubna na ɗora hannu aka zata kallah ihu doctor da Nurses guda biyu ruka shigo kora su sukayi waje suka hau gwaje-gwaje babu bata suka tabbatar da rai yayi halinsa.

(Allah sarki Sadiya ashe cuta bata tashi ba Allah ubanji ya yafe miki Allah yasa mutuwa tazama hutu agre ki dama musulmi baki ɗaya. Shi yasa akullum ake so ka riƙa aikata alkairi baka san Sa'id da zata zoba ko kana tafe ka da ciwo ko babu)

Bayan sun gama tabbatar wa Doctor ya fito da gudu Baba Zulai ta tare shi.

"Ta mutu ko Likita Ni dama nasan tun da tayi Salati Nasan ta mutum?”

"Dan Allah Hajiya kiyi mata Addu'a duk wani musulmi in ya rigamu gidan gaskiyar addu'a yafi bukata ba koke ko....

Kafi doctor ya kai ƙarshe Baba Zulai ta sulale ƙasa asume Lubna kuwa tana guza ihu ta hau aljanu Sumayyah kuwa hawaye take da furta sunaye Allah. Sai da suka juma ahaka Yusufa ya shigo ciki kaɗuwa da tashi hankali tunda yaji abin da ya faru ya fara kiraye kiraye waya Fu'at ma da shigowar sa kenan Abi ya sanarwa da rasuwa tuni suka ɗungumo zuwa asibitin.

Cikin ƙanƙane lokaci asibiti ya cika koke-koke da Aljanu babu kalar wanda dangi Baba Zulai da masoyan ta basu baya kwanar Baba Zulai Ramatu ce ta guza ihu ta taho da gudu ta shaƙi wuyan Sumayyah. Tana Magana iri ta masu iskokai.
Chapter 29 · 0% Book details