← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 35

Sashe 32

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya ta ƙwakwallo.

“Wai Ummu har ta manta ta sani kwaso kaya baya shine da naji isakar guri tamin dadi na zauna”
Shuru Inna ta mata bata sake cewa komi ba.

Bayan Sallah Isha Ummu ce ta shigo ta same ta tana gyarawa Innar ta guri kwanciya tun da ta ganta Gaban ta Ya faɗi,

“Sumayya aiki kike Oya kawo Abi na Compound ina jiranki zaku tattauna”

Miƙewa Sumayyah tayi tazo gaban Ummu ta zube.

“Ummu dan Allah kiyi hakuri akan abin da Zakiji daga baki na Wallahi bazan iya aure Abi ba Ina masa kallo uba ne, Ummu ya kamata aduba iri halin da Ammar zai...

“dakata Sumayyah shi Ammar ɗin bai duba iri Halin da kika shiga ba ya auri yar uwarki dan Haka mun gama magana babu fashi gobe in Allah ya kamu za'a ɗaura aure duk wasu surutu ya ƙare.”

Ƙara Sumayyah ta gunza.

“Wayo Allah Shikenan zan mutum Dan Allah ummu an karki rabani da Ammar Ni wallahi shi nake so dan Allah ki tausaya mana”

Cak ta tsaya tana kallo iko Allah yau Sumayyah ke magana iri haka tabbatar Akwai sanya hannu ammar dan ta lura kullum yana yana saka mata dance Sumayyah tana basarwa wato shine daga ji maganar aure shine shi kuma zai yi mata tasa huɗubar.da sauri ta ajiye blanket ta fice, Inna da take zaune kam kujera tana kallo iko Allah ta mike kiran Sumayyah tayi tana zuwa ta dauke ta da mari.

Tana murɗa handles ta samesa a tsaye fitowar sa daga wanka kenan. Daure fuska tayi.

“Ammar me kace da Sumayyah, shi ka manta Maihaifinka ne yake nemana aure ta”

Sai da Ammar ya rintse ido tare da Haɗiye yawi mai ɗaci kamar bashi ya ce.

“Ummu akan me kike magana me Sumayyah tace wanda na zama abin tuhuma?”

"Wallahi Ammar zai mare ka kar kaga baka da cikakiyar lafiya Yariyar nan ta amince tun da jumawa yanzu kuma tace ba haka ba.”

Kamar yaro goye ya kamo Hannu ta.

"Haba Ummu Com down Wallahi I don't know ko Fu'at zaki tambaya ji da ita bamu magana”

Zama tayi kan kujera ta daidaita Muraya.

"Ammar dan Allah karkayi haka ne yasa kake so mai damu kannu mutane.”

Zama ya yi yadda da gaske zata yarda dashi yace.

"Ummu da kuna maganar ku dazu nasa muku baki?”kai ta girgiza."Tom me yasa baki yarda dani ba ki faɗan ita fasawa tayi?”

"Ammar na shiga Ruɗani taya za'ace Mun gama magana yanzu dakar nasa abi ɗinka yayarda zai je Compound wai dan su fuskanci juna Amma ina zuwa ta furje wai ita akwai wanda take so bashi ita Uba ta ɗauke shi.

“Tom ummu ku barta mana yanzu fa ko dan da ka haifane ba'a masa dole kuma shi kanshi Abi fa cewa kikayi daƙar kinga kenan baya murna da Haɗi kawai kubuta wanda take so.”

miƙewa tayi a zafafe

"Wallahi bazai yuyu ba Sai dai na sauya mata da Fu'at dan Wanda take so har yanzu bata rashi nikaum”

"Wane ya faɗa Wallahi ummu ina sonta a kullum santa karuwa yake Please sai yanzu saki fuskanci damuwar Ɗanki Ummu”

Sai da ya faɗa kuma yaga ta gafe shi da kallo kame-kame ya fara.

“uhum..Ahhh.ummu kada fa kimin mummunar fahimta bawai yana nufi nine na zuga ta ba”

Ficewa tayi bata re da tace komi ba.

Dafe kumci ta tayi wasu waye masu zafi suka shiga gangaro mata.

“Sumayya kin manta Halaccin Ummu a gare ki,ki tari tsabar ido ta kice kin fasa so kike duniya ta zage mu so mu zama masu don kanmu, me yasa baza kokari rama halaci ba.”

Ciki kuka Sumayyah tace.

“Inna ta In har Zan kamanta Adalci da kaunar, Ammar ya kamata na nunwa yayi ɗawainiy dani ya jefar rayiwar sa ciki haɗari duk raboda Ni kisani ciwo da ya affaka da Cin zarafi da akayiwa Sadiya duk nice Sila Dan Allah Inna ta ki bari ko yaya ne na zauna da Ammar na kamanta kaunar da sadaukarwa da ya min”

Tana faɗi haka ta zube a guri ta saki kuka mai tsuma zuciya.

*BANFAI*

Alhaji Ɗan Dubai ne da shi da tawagarsa aka tsaryar dasu gefe guda kuma Asp Muntaƙa dunbulum ne aka kafa masa camara bayani ya fara.

“ Assalamu alaikum kamar yadda kuka sani suna Asp Muntaƙa dunbulum mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jahara kano wa ɗan nan mutane da kuke gani ana zarginsu da aikata manyan laifika karkashi sashi na ɗari uku da goma shabi..gamar yadda kuke gani sun shiga gidan mata da miji ta sun aika fade tare da zubawa miji poisoning wanda sukayi kokari hallaka mijin a karshe matar tarasa ranta”

Juyara da Canada akayi kan Dama.

“Kai zaka iya fada mana yadda akayi kuka shiga gidan da dalili zuwanku kuma me yasa kuka aikata hakan?”

“Ni Alhaji Ɗan Dubai ne ya bamu kuɗi shi ya kaimu gidan ma tare da kashe mana wutar gidan sanan muka shiga shi ya faɗa mana yadda zamu in mushiga mu bamu tunani shi Namiji zai rayu ba”

Akayi daga kan Dama aka maida kan Alhaji Ahmed Ɗan Dubai nan ya bada labari duk abin da ya faru da dalili yi musu haka.

Bayan sati biyu kotu ta yanke musu ɗauri rai da rai sanan kutu ta bada umarni ake gidan da ya ke aikata haramci sa arushe gidan a gina kato masallaci.Soaai Alhaji Ɗan Dubai ya shiga tashi hankali atunani sa bazai jima ba zai fito sai gashi babu wanda ya nemeshi gudu kar sunan su ya baci.

Ta jima tana kuka hakan ya sa Inna ta jin babu dadi, a hankali ta jata jikin ta ta fara rarashi ta, cikin shasheƙar kuka tace.

“Inna dan Allah karki rabani da Ya Ammar wallahi har yanzu son shi bai dishashe a cikin zuciya taba, Ban taba Kallo Abi a matsayi Wanda zan Aura ba sai Uba Agare ni taya zan iya rayuwa da mahaifina matsayin miji”

“Shikenan naji Allah yasa hakan ya zama alkairi gobe In Allah ya kaimu zan koma Giɗaɗo zan nemi mahaifin ku da ya sauwaƙe min dan Bazan iya zama dashi ba in Allah ya kaimu zan nemi haya ko wanko ne na rika yi”

Sai da Sumayyah ya buga lokaci da ta furta rabuwa duk da tasan babu zama a tsakani ta da mahaifi nata.nisawa tayi tace.

“Inna dama...Fa..Uhum. Babanmu tun lokaci Bikin Sadiya Baba Zulai tasa ya sauwake miki yanzu babu sauran zama atsakani ku baki ga bai taɓa zuwa duba ki ba”

Ta faɗa ido ta na cukowa fall da hawaye, Murmushi tayi ta shafa bayan ta.

“Auta Karki damu Allah yasa hakan ya zame min alkairi Amma duk da Haka gobe zan koma can na nemi gidan na zauna kafi ta Allah ta kasan....

“Dan Allah Inna ta ki daina faɗi haka in kika barni dawa Zan Rayu? bani da kowa faɗi duniyar nan sai ke?”

"Haba Sumayyah ki dan Mutuwa dole ce ko mu dade ko mujima dole wataran sai mu tafi”

"Insha Allah Inna ta Bayanzu ba Sai na tara kudi na biya miki Aiki Hajji ki ga iri 'ya'yayana”

Duk hirar da suke Ammar yana ji su lokaci ya fito ɗauka abu A parlour da yake manne da Ɗakinsu.

Washegari Ummu ce da Ammar sai Fu'at zaune A parlour magana suke duk da babu wanda yasan me suke tautaunawa guri suka nema suka zaunar Sumayyah ta gaida Ummu Ammar da Fu'at suka gaida Inna.Duk yadda ya kafe Sumayyah da kallo amma taki kallo sa, bayan jim kadan Inna ta kalli Ummu tace.

"Hajiya dama yanzu nake cewa zan koma ƙauye mu saboda zama na bazai yuyu anan ba ga shiri biki Sumayyah”

Murmurshi Ummu tayi

“Inna in kin koma wa kike dashi Acan sanan Nasan da Ku rabu da Malam ammar kuma ɗaki ya mallaka miki gida Anan Tarauni dan Haka yanzu Fu'at zai kaiku ku gano babu wani gyara da Za'a masa sai dai abu da ba'a rasa ba Yau kuma Abi ya tafi shi da Abokan wa dan neman Aure Sumayyah.”

Inna taso ta nuna rashi Amincewa ta wai dakwai kyar tayi yawa Sai Da Ammar ya marairaice kamar zaiyi mata kuka sanan ta Amince.

Gidan Ba wai Babba bane sosai sai dai Ya mutukar haduwa komi a kwai aciki ɗakuna Uku ne Sai Kitchen duk wani Kayan more rayuwa akwai aciki kayan sawa ne babu, Godiya ta rikawa Fu'at kamar shine Ammar ɗin Sumayyah kam fita tayi tayi kukan ta ta more ta goge ta dawo suka wuce gida.

*ƘAUYE GIƊAƊO*

Lamarin Baba Zulai ya dada ta'azara dan Har duka take kaiwa almau hauka ya bayyana sosai banda Kashi da fitsari da take a kwance gashi kanta kam duk ta tsige shi da Hannu Malam kam komi ya tsaya Sai ya kwana uku huɗu babu mutumin da yazo bare ya samu abin rufa wa kai asiri, komai na duniya ya jagule masa, Yusuf kam Yau ya faɗa wani gida ya garƙama Sata sai da suka masa lulus sanan suka yasar da shi abayan gari bayan wasu kwana lalura ta bayanna ciwo kafa ne ya kama shi duka kafa biyu (Bone cancer) wace take zaizaye masa kafa duk yadda yaso Malam ya kai shi asibiti amma furr yaƙi yace ba ciwo Asibiti bane.

Bayan wata Uku malam yana zaune Almajirai sa duk sun gudu sun koma wasu garuruwa ya zubar tagumi masu zama ma duk sun daina yafa gani baƙi motoci har uku baisa ran guri sa aka zoba dan atunai sa Alhaji Namadi ne Makocirda yake tashe yanzu ya yi baki, gani motar ta tsaya kusa dashi da sauri ya mike gani Abi, Abi na fitowa ya karaso yana masa sannu da zuwa ciki baban Zaure aka musu shimfida suka zauna bayan sun tattauna Abi yazo da bukatar neman Aure Sumayyah akan Ammar bai isa yace A'a ba dan yanzu yayi nadama gashi baisan ida zai samu Sumayyah ba bare mahaifiyar ta yanemi yafiyarta duk ya iske labari Alhaji Namadi yace ya taba gani ta A yankaba su je siyan kayan miyya da Sumayya da wani yaro sai dai baiyi tunani a gidan su Ammar take zaune ba nunfasawa yayi yace.
Chapter 32 · 0% Book details