← Book details Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 35

Sashe 12

Yar Mahaukaciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Nasarawa Kano*
Tsakani Hajiya da Ammar juna suka kalla ya ɗauke kai, Hajiya ta fara shafa bayan ta."Sumayyah kuma shine sai kinyi kuka kar ki damu insha Allah Gobe zan sa ya mai dake Ai zaki gane ko?”Kai ta ɗaga mata.sai da Hajiya ta lallashe ta sosai sanan suka fita har Ammar ɗin.

Suna fita ta sauke ajiyar zuciya,“Allah… badan niba, Allah ka bani kwanciyar hankali… ka raba ni da tsoron da ya cinye zuciyata.” hannunta ta sa ta sharce hawayen da suka gangaro mata.Sai da Tayi Addu'a sosai sanan ta kwanta.

Tunda ya koma ɗaki bacci gagarar sa ya yi a fili ya furta"Wai ita me yake damu ta duk da hawalar da tasha buri take ta koma cikin su?” tsaki ya ja ya sake juyawa ya gyara kwanciyar sa.

Tun Asuba Sumayyah ta shirya take juyi ciki ɗaki gajiya tayi ta zauna gefe gado ta sauke Nufashi a fili ta ce."Su fa masu kuɗi basa son tashi da wuri sai aita fama basu tashi ba, yanzu ma inaga tara tayi amma basu tashi daga bacci ba”

Sai tara 'Yar aiki Hajiya ta kira ta, jikin sai rawa yake ta fita parlour ƙasa, Hajiya ce kawai kan Daining tunda ta hango Sumayya fara'ar taƙaru "Sunu da zuwa yar albarka ina fata kin tashi lafiya?”kasa jurewa tayi tana zuwa zata gaida ta ta fashe da kuka, Murmushi Hajiya tayi ta ɗagota ta rungume ta kamar yarinya ƙarama.

“Allah ya mayar miki da farin cikin da aka kwace miki. Banso ki zama raguwa kizama mace me juriya da jajurcewa!,” Hajiya ta furta cikin tausayi, tana shafa bayanta.ajiyar zuciya kawai Sumayya take saukewa. cikin sigar lalashi ta ce.“Allah ya ba ki kwanciyar hankali fiye da wanda kika taba samu Abaya ina fata daga yau baƙin ciki ki ya ƙare, Zan cigaba da Addu'a Yariyata Sumayyah, farin cikin na har abada ya luluɓe wanan zinariyar zuciyar.”

Ammar da ya fito yanzu ciki Shadda sa bazum blue block ta masa kyau kamar sabo ago yana tsaye a bakin ƙofa, yana binsu da kallo baisan me yasa ba, yake jin ƙaunar Yariyar duk lokaci da yaga Hajiyar sa tana janta ajiki.basu yi tunani ya zo ba.

Idonsa ya sauka a kan Sumayyah, yadda take jijjiga kai da yadda take tsanan ta kukan ta, da hannunta da ke rike da Hajiya kamar bata so ta sake ta yaji ɓaci ran yanayin da hmya fara haduwa da ita.kasa shiga yayi ya kasa komawa.Zuciyarsa tashiga bugawa da sauri.“Wannan yarinyar… me suka mata haka?”Ya fada a ransa cikin zafin rai.“Me ya sa duniya tayi mata tsauri har haka? Kuma me yasa tun ranar farko da na ganta zuciyata ke jin kamar ina da hakkin kare ta?”

lumshe idon sa ya yi dan danan wani irin ɓacin rai mai zafi ya taso masa.ya furzar da iska mai zafi, ƙoƙarin juyawa yake Hajiya ta kira shi.

“Ammar.” tsayawa ya yi cak.
“kazo ka rareshe ta zan haura sama kayi break fast din da ita kafi na fito”Kai ya daga a hankali, don shi in akwai abin da yake masa wuya bai wuce yawan magana ba.kujerar daining yaja wace take kallo tata ya zauna shuru ne ya ratsa su, na wasu daƙiƙu gani ba zata yi magana ba ya fara juya Spoon aciki Chips wanda yake haɗe da soyayaye waina kwai, ya na kallo ta.“Kina kuka Saboda kin fiso ki koma inda za'a maida ki baiwa ko?”

Jajaye ido ta ta ɗago."A'a saboda Inna tane kawai ina tsoro abin da zai sameta”
Shiru ne ya sake ratsa tsakani su sanan ya dago kamar me ciwo hamgum.

“Ki sani daga yanzu zan tsare ki. Zan kare ki. Kuma babu wanda zai kara cutar da ke.”Ya faɗa yana kallo fuskar ta.Goge guntu hawaye fusakar ta tayi."Nagode Amma Ina so na koma Bunkure Inna ta tana can tana..…”tsawa ya daka Mata ido sa dan-danan ya yi ja jikin sa har rawa yake gani ta fashe da kuka yasa shi ɗaukar gogar ruwa mai sanyi yasha,yana ajiyewa ya tashi ya matsa kusa da ita, ba tare da ya taba ta ba.“Ki daina tsoro.ki sani zan maida ki gida yau shikenan tunda bakya son zama damu”

Shuru tayi ba tare da tace komi ba har ya gama ci ya goge baki sa da tissues ya miƙe “kije ki shirya zan fito da mota”Har sai da hakonta suka fito saboda murna, kallo ya bita dashi har ta haura sama shikuma ya fita.

Bayan kamar 20 mintes Hajiya ta fito sai da ta fara shiga Bedroom ɗim da Sumayyah take ta kira ta sanan suka sauka ƙasa suna zuwa Ammar ya shigo yana duba agogo wayar sa ya kalli Hajiya.

"Hajiya zan kaita Daddy yana hanya nasan har na dawo bai iso ba”Kai Hajiya ta jinjina Hawaye ya cika ido ta,kwana biyu da tayi da Sumayya tashiga ranta sosai. Rungume ta tayi
"Allah ya kare ki ya duba rayiwar ki, Zanzo na duba ki kafi azumi sanan Zaki zomi da Sallah kinji 'yata?”

Kai ta ɗaga tana hawaye“Eh Hajiya zanzo Nagode Allah ya dubaki yadda kika kula dani”Babar Ket ta miƙa mata."Ammar zai baki kuɗi ɗinki kisa wasu,Wasu kuma ki bari sai Sallah”Har ƙasa ta zube ta sake mata godiya sanan suk fita Ya zauna A drive seat ita kuma for seat, tun da suka tafi, ya saka waƙar India mai sa tausayi kamar yaresa na gado haka yake bi waƙar cikin Sallo, satar kallo sa kawai take shikam idon sa yana kan hanya yana bin wakar yana jin daɗi yanayi hanyar ƙauye Saboda yanaso rayuwar ƙauye. Sai da suka yi nisa Sosai ya kalle ta."Ke Kar fa ki saida nifa.”

Jiki ta ne ya hau rawa tana rantsuwa"Wallahi Ya Ammar bazan sai da kaiba Ni ban san ma yadda ake sata ba, nan ne hanyar garimu ko...ko wan can Zaka tambaya mun kusa shiga Gari giɗado”

Burki ya taka yana kallo yadda duk ta ruɗe dariya ya fara mata, sai kuma tayi shuru,suman tsaye tayi bata taɓa gani wanda dariya take ma kyauba iri Ammar shi komi yayi kyau yake masa, maganar sa taji.

"Ki rage tsoro ko Kya samu sallama aciki ranki ”shuru tayi ya sake kunna motar...

****
Malam na shogowa ya bisu da kallo, wuyansa da kwato carbi mai dubu.gyran murya ya yi.“Tom lafiya aka tsaya cirko-cirko kuna kafe ni da kallo.?”Ajiyar Zuciya Baba Zulai ta sauke.

"Malam inafa Lafiya ace Matar nan shikenan kullum ta riƙa ja mana zagi da sunan Mahaukaciya ce ita gaskiya ya kamata ka ɗauki mata ki...”Duk abin da ya faru ƙarya da gaskiya sai da ta haɗa, Nan kuwa ya hau kamar fulawa da aka zan baɗa Mata yis. Cikin fushi ya kalli Yusuf.

"Kai Yusuf duk yadda za'ayi kaje ka dawo da ita ayau ba sai gobe...

Sallamar Alhaji Ɗan Dubai ce ta hana kowa motsi Yusuf ya miƙe yana rawa."Yau kace akwai cin uwar sabada agidan nan tab Malam Mutumin kane yazo wata ƙila wasu kuɗi yazo ƙarawa.”

Tafiya Malma ya yi da sauri har Malin-malin ɗinsa tana niyar kada shi.Baba Hauwa tace.“A'a Malam yi a hankali”

Yana fita ya iske Alhaji Ɗan Dubai a tsaye cikin nan nasa agaba, kansa sai tsatsafar gumi yake na azaɓa,yana niyar Zubewa Alhaji Ɗan Dubai ya shaƙi kwalar Malam Sule Gidaɗo.

"kar ka tsunguna min Tsoho Alla kwankwan nunafiki dama gadar zare ka shirya min na gama baka kuɗi shine kuka sa Police sukaje suka karɓa maka yar ka tom Wallahi baku isaba yadda kake ganina tsohon ɗan tasha ne goge ɗan bariki, Bani da dama guri neman na Abinci”Ba Malam ba hata Yusuf da Khalid sai da tsoro ya shigesu lallai yau su haɗu da ƙwallo dan Iska, yadda yake ruwan Ashar tsaf zai danfara malam A ƙasa.

Duk layi da motar Ammar ta gilma sai Yara sun bita suna “laaaa ga balaraɓe tare da 'Yar Mahaukaciya kamar bai san da zaman yaran ba haka yake tunƙi cikin nutsuwa.

Tunda suka tinkari ƙofar gidan su gaban ta ya fara faɗuwa.

" Inaalillahi wa'inaalaihi rajun, Wa nake gani kamar Alhaji Ɗan Dubai.”Ta faɗa tana me sake kallo Ƙofar gidan nasu da mutane suka fara taruwa, Gani shine yasa ta sauri riƙe hannu Ammar.

"Shine wallahi..!Kar muje shine Wallahi..! shine nasan zuwa ya yi ya maida ni dan Allah mu koma kar ka kaini gurinsu nasan Babana basu ni zaiyi kuma ga Yaya Yusuf aguri.”

Kuka take kamar zuciyar ta zata fito, Ammar kam kamar be san akan mai take magana ba ya cigaba da tuƙi sa cikin kwanciyar hankali har suka ƙarasa inda Su Baba Malma suke......

Shering and like
[11/17/2025, 1:01 PM] OUMMU MUWADDAH: https://whatsapp.com/channel/0029Vb1QRwY5vKACPNI7B73a

*📚🌸YAR MAHAUKACIYYA📚🌸*

Mallaki:
Husaina S Abdullah
(Oummu Muwaddah)
📚©2025 -- Duk haƙin mallaka na musamman ga marubiciya.

____________free book _page-10

Cikin fidda rai ta cire hannu ta daga jiki hannu sa ba tare da ya kalle taba yace.“Wan can ne Mahaifi naki?”Kai ta ɗaga masa hawaye masu zafi suka gangaro mata "Amma Kace zaka kula dani kuma Hajiya ta ce Amana ce ni A hannun ka.me yasa zaka mai dani in da na baro?”

Sai da ya buɗe murfi motar sanan yace"fita muje”Jiki babu ƙwari ta beɗe 'Yan matan ko nace ƙwailaye kwaye su Sadiya ne ɗaya daga ciki ta waiga karaf ido ta ya kai kan Sumayya, Rashida da take gefe Lubna ta kwaɗa shewa.“La Shikenan ma Baban su Sadiya ga 'Yar mahaukaciyar nan ta dawo sai ya tafi da ita can su ƙarata”

Ido Malam da yayo waje ya fara kar-katar da kai yana kallo In da aka ce Sumayya na guri da sauri Alhaji Ɗan Dubai ya saki Malam Sule Gidaɗo ya tako inda Sumayya take tsaye jikin sa na kyarma.Hannu Yasa zai riƙe ta Muryar Ammar ta karaɗe guri.

“Kar kayi kuskure ɗora hannu ka a kanta,Otherwise, you will regret it in a way you have never experienced in your life.” DA fari ya ɗauka Wanine daga ciki Yaran Malam,Ciki matsanan cin ɓacin rai ya waigo."Ko Ubanka Malam gashi Bai isa...ya..”
Chapter 12 · 0% Book details