← Book details Yan Uku Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 14

Sashe 11

Yan Uku Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina neman tsarinka daga sharrin raina, da kuma sharrin shaidan da shirkarsa, da in tsuwurwurtawa kaina wani abu mummuna, ko in jawo shi ga wani Musulumi.*
*Ya karanta suratu As-sajdah (Alim lam mim, tanzilul) da suratul mulk (tabaraka).*
*Allahumma aslamtu nafsee ilayk, wafawwadtu amree ilayk, wawajjahtu wajhee ilayk, wa-alja'tu zahree ilayk, raghbatan warahbatan ilayk, la maljaa wala manja minka illa ilayk, amantu bikitabikal-lathee anzalt, wabinabiyyikal-lathee arsalt.*
*Ya Allah!

Na sallama raina gare ka, na maid a al'amarina gare ka.

Na fuskantar da nufina gare ka, na dogara da kai (a cikin dukkan al'amurana) saboda kwadayin abin da keg are ka, da tsoron ka.

Babu mafaka, babu matsira daga gare ka sai zuwa gare ka.

Na yi imani da littafinka da ka saukar da kuma Annabinka da ka aiko.*
77-80
Anwar fa ya dage sai ya wulakanta easha a garin Kaduna {ba wai zai wulakanta ta bane yanda za a gani a a aurenta zaiyi yaci mata uwa}
A ko ina ya zuba mutane da hutonan easha idan sun ganta su kamata.
-----------------&
*Bayan sati*
Easha tana sane da duk take taken anwar Dan duk motsin sa yana tsakiyar hannun ta, time take jira sai taci masa uwa!

Sai ta banbanta masa tsakanin aya da tsakuwa wallahi!!!

Yau su baba Shariff suka dawo daga wajan boka da maganin makanta wai zasu sakawa umma a abinci taci sai ta makance bayan maidata kurma da sukayi bai ishe su bah!

Ramatu bata taba kawowa su umma abinci bah sai yau da ta barbarde shi da maganin, tana zuwa dai dai kofan sai taga easha juyawa tayi wai sai anjimah!!

Murmushi easha tayi tace ki gama kwana kwanan ki zaki dawo ...

Gwamma ki gama jin muryoyin mutane da sautin iska, kukan tsuntsaye duk ayau !

Ramatu abincin ta ajiye wai sai easha ta fita tukunna.
-------------------------&
Kullum dare suna wa umma karatu cikin ruwan zam-zam suna bata, easha ta bada kudi anyiwa almajirai sadaka sanna ayiwa umma saukan alkur'ani mai girma ...

Sanna anbata addu'o'i sunayi ; sun dage sosai basa sanya duk da su easha sun kusa tafiya .

Easha dai taki fita a gidan har dare yayi..

Ramatu bata so hakan bah....

Maganan boka ta tuna inda yace
_Gida uku zaki raba maganin sai ki zuwa gida daya idan har taci sau daya shikenan . ki dai tabbata taci_
Murmushi tayi tace akwai gobe...
--------------------$
*washe gari*
Aisha a wanna ranar za ta tafi barno makaranta .

Umma tayi kuka sosai da tafiyanta sanna tayi mata nasiha sosai da addu'o'i neman sa'a .

Har tasha easha ta rakata ta dawo.

Yau easha ya kamata ta tafi amma taki tace akwai sauran time tukunna!
------------------$
Amarya rabonta da faruq tun last da yaje yayi mata wulakanci har yau da aka kaita.

Sai zuba ido take ko ango zaizo shuru kake ji kaman an shuka dusa!

Sai hakura tayi ta kwanta baccin wahala da gajiya ga uwar yunwa yana cin ta!
---------------$
Faruq gidan abokinsa sultan yaje abunsa .

Babu irin fadan da basuyi bah
Haba faruq mai yasa ka aure ta indai baza kaje gareta a daren farkon Ku bah.

Aka dai aura mun ita ...

Ehe sai tayi ta zama har mahadi ya bayyana kuma idan kaga nabar gidanka sai na auri my angle tukunna.

Haba dai ai baka isa bah tashi za kayi kabar mun gidan tunda ba naka bane.

Tsaki faruq yayi yace sai ka cicciben ka kaini ai...ya fada yana kwanciya a kan bed din sultan..

Murmushi yayi yace abokina babu mai iya maka...

Da mom tasan haka kake da bata aura maka ita bah...

Da zaka taimaka da kaje an raba auren nan wallahi!

Wa!

Ni Tabb Allah yabaka hakuri!

Da hakurin ta mutu sadakan nawa ka ban?

Babu oga masifah!

Sai sukayi shuru dukan su!!
--------------$
Asuban farko ta tashi da gajiya sosai ga uwar yunwa a tattare da ita.

Haka ta tashi tayi wanka ko gyara dakin batayi bah ta wuce dining table..

Empty ta gansa.

Kicin ta wuce ..

Akwai komai amma bata iya girki bah balle ta girka...

Indomie ta dauka take ce danye tana kukan dana Sani.

Can wajan 10:00pm drive mamar faruq ya kawo musu breakfast mai rai da lafiya
Tayi takaicin cin indomie danye ...

Haka ta kara cin abincin...

Kafin kawarta zee tazo sukayi ta fira.

Sai da yamma zee ta tafi da alkawarin dawowa gobe!

Yanda ta kwana ita
kadai jiya haka yau ma ko mai kama da faruq bata gani bah balle faruq!
---------------------*
Yau ma wani abincin ta sakeyi ta zuba maganin a ciki tayi dakin umma.

Tana shiga Easha tana shigowa gidan!

Easha na shiga ramatu kuma ta daibo a hannun ta zatabawa umma a baki!

Uban meye zaki bata!

Easha ce ta bugawa ramatu tsawa Wanda yasa abincin hannun ta zubewa!

Sai ta tashi tana karkarwa ...

Da sauri ta bar dakin tayi nata dakin.

Umma na kokarin daukan abincin taci...

Easha tayi short da kwanon abincin ya zube.

Nan umma ta hau yi mata fada akan bakyau wulakanta abinci.

Ana cikin haka shatu tazo!

Nan easha tace ko ruwa ramatu ta kawo kar ta sha Dan da dukkan alamu akwai wani kulle-kulle a ciki.

Umma dai murmushi tayi kawai,bata yi musu magana bah...
--------------------*
Sultan kasa ayi mun Dan wake dan bana son wanna ....

Ya fada yana nuna farfasun kayan ciki (har my fans sun hafiye yawu lol) .

Sultan zamansa ya gyara yace ba ga can Amaryar ka bah mai zai hana kaje kace tayi maka mana....

Ban son wulakanci fah sultan.

Ni fa ka tattara kabar mun gida Dan ga Amaryar ka can ba ka tashi kaje tayi maka !

Sai ka ciccibe ni ka kaini ehe...

Ya fada yana hararar sultan
Sultan sharesa yayi yana breakfast din sah
------------------*
Aisha ta isa cikin barno lafiya sanna ta karasa *University* dama already easha tasa angama mata komai har kama mata daki a hostel ...

Direct ta wuce taje dakinta ta shirya komai tayi sanna tayi wanka ta fita zagaya university ...

Tana cikin tafiya taji ance hey fine girl.

Juyawa tayi da sauri!
------------------*
Yau easha tayi Nisan zango hakan yabawa ramatu daman sake dafa wani abincin amma wanna katon a kwano biyu ta zuba daya nata daya na umma sai ta zuba magani ana umma tayi dakin dashi.

Taje dakin suka gaisa sanna ta mikawa umma nata...

Tana murmushin mugunta
Umma ma murmushi tayi tace tana son ruwa ...

Da maganan kurmaye
Jiki na rawa ramatu taje ta daibo ruwan ta dawo ...

Nan suka fara cin tuwan suna hira abunsu
Gefe daya ramatu tana tuna maganan boka inda yace
_Duk wanda yaci wanna maganin ya makance har abada kaman yanda gawa idonsa ke rufewa Dan bashi da makari_
Murmushi ta sakeyi tana mai jin dadi umma zata makance!

Tass suka cinye tuwon ramatu ta kwashi kwanuka tayi gaba tana mai murmushin mugunta!

Umma ma murmushi tayi abunta !
*Aishmar ce
[11/11, 1:36 PM] Queen Indo: *
YAN UKU
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION
*~We are bearer's of so golden pen
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen
,behold our words.~*
*~A product of our pen
,savour our words, for it will cause you no pain.~*
*Addu'ar Bako Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci*
*Allahumma barik lahum feema razaqtahum, waghfir lahum warhamhum.*
*Ya Allah!

Ka albarkance su a cikin abin da Ka azurta su das hi, kuma Ka gafarta musu, Ka ji kansu.*
*wiring by Aishmar(Queen Indo)*
*saura yau ma kuce nayi rowar page
*nagode sosai da love da kukewa book nan
.

Nima a love u cikin kwando
96-100
Yaya faruq please kasha ko dan kadanne naga yanzu ka dawo daga rana!

Idan zansha ke ce kike bani da?

A a amma dan na baka yanzu ba laifi bane!

To bazan sha ba sai kiyi mun dure .

Kayi hakuri kasha please?

Wai kin dauka nima Adamz ne?

Shuru tayi batayi magana bah.

Girgiza kai yayi yace
Kin barbade abu da magani sanna kice nasha mai kika maidani?

Stupid ko useless?

Ki kiyaye ni tam!

Mtsss sai yabar wajan!

Kukan bakin ciki ta fashe dashi tayi dakinta!
**"**
*Ahmad isa shinkafi*
Wanna ne asalin sunan sa.

Mazaunan Kaduna ne . baban sa shi kadai ya ne dan da yazauna dan mamarsa tayi ta haihuwa amma basa zama sai su rasu..

Shi kadai Allah ya raya musu.

Tare sukayi makaranta da faruq tun daga secondary school har degree duk akan kasuwanci sukayi shi...

Faruq yana aiki a kamfanin shi wanda yasa masa suna *SHAFA* (Sunan sa dana easha) tun kan yasan su nan ta wanna ya radawa angel din tasa shiyasa ya hada ya zama shafa sunan kamfaninsa.

Kamfanin furniture's ne su kafet, set na kayan daki da sauran su dai.

Ahmad kuma kamfanin robobi ne dashi Wanda yasa masa suna *MADTU* (WANDA BANSAN MA'ANAR SA BAH)
Mahaifinsa hamshakin mai kudi ne Wanda ya samu kudin ta hanyar kasuwanci dan yana shigowa da kaya daga kasashen wage zuwa nan gida Nigeria.

Dalilin hada auran su da easha shine!

Akwai wata rana da Alhaji isah shinkafi yayi cinikin gwala-gwalai ya siyo tsurarsu Wanda ba a sarrafa bah.

Barayi masa dirar mikiya a gida suka kwashe wanna gwala-gwalan da duk takardun gidajen sa da duk wani kadarorinsa.

Yayi kuka ranar ya rasa ta ina zai fara!

Sai matarsa tace ya kira Ahmad ya fada masa
Yace a a sai dai amininsa Abdullahi yakub
Nan ya kirasa ya fada masa
Ya girgiza sosai nan ya hau motarsa yazo sukayi ta jimami har Abdullahi yana niyyar tafiya sai labarin kububuwa ya fado masa ...

Nan ya shawarci aminin nasa akan su gwada kiransa.

Ba musu suka kirashi
Bayan yazo suka fada mishi abunda ya faru
Murmushi yayi yace shegun gari kenan amma nawa zaku biyani?
4m .

Alhaji isah ya fada
Baiyi bah!
8m..

Inji Alhaji Abdullahi yakub
Baiyi bah!

To mai kake so?

Danka Ahmad nake son ya auri jikata guda daya..

Ya fada yana murmushi
Kaman yaya?

Yau shekaransu bakwai cif su ukune duk kamarsu daya sai ya auri daya a ciki idan son samune ya auri EASHA !

Baiyu bah!

Shikenan kuje Ku kwato dukiyarku sai anjima!
Chapter 11 · 0% Book details