← Book details Uwar Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 19

Sashe 16

Uwar Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Babanmu ya dawo suka gaisa yana tambayarshi mutanen gida,Nanfa akayi ta hira,sai yamma Yarima ya tafi haryanzu baiga"Humaira ba tuni "Yarima ya cire kunyar shi 'yace Inna dan Allah i'nason " Humaira ta rakani k'ofar gida 'Inna ta kirawoni nafito "Tace zaki raka Sagir k'ofar gida kiyi sauri ki dawo.

" Cikin jin haushin shi Na ce to muka fito k'ofar gida ya kalleni "Yace Humaira cikin wata iriyar murya ya fad'amin Nace Na'am Yace banison in buye miki Abinda yake raina Sana diyyar haka garin kallon ruwar har kwad'o yayi mun k'afa don haka" Humaira inasonki so mai tsanani tun ranar da na bugeki nakeji araina inban Aureki ba Zan i'ya rasa komai nawa.

..."Ciki kuwa harda raina 'Humaira tace kai'Sagir kada kace zaka fad'amun Abinda kasan ba haka neba har zuciyarka'Nan take na Fara hawaye Ina cewa nadad'e inajin wannan furucin naku na Maza na yaudara Na K'ara da cewa ya Dade yana cewa I'nason ki"UWAR'GIDANA idan babu ke bazan i'ya rayuwa ba,Wallahi bazan tab'a rayuwa babu ke ba,idan babu ke Zan rasa komai nawa,Tun bansan meye soyayyaba har nasani na rayu dashi ban tab'a cin amanarshi ba Amman shi yaci tawa.

"Na kalli Sagir da jajayen idanuna da suka rine suka koma ja'Nace Kada ka b'ata lokacinka ka a kaina bazawara,zaka b'ata lokacin ka ne don bazan tab'a yadda da ta tsuniyarku ta maza ba.

" Na kalli Sagir da hankalinshi yake atashe "Nace Sagir kayi hakuri kaja jikinka kabar wajen nan saboda bazan tab'a yarda da wad'anan kalaman naka ba don haka katafi'Na fad'a da k'arfin gaske nayi hanyar gida da gudun gaske kamar Zan fad'i.

*Ummu Maher ce*

*Vote*
*Share*

and
*Comment*✍️
[11/10 16:22] 💖Rabee'atu Ummu Maher💖: 💚💖💚💖💚💖💚
*UWAR'GIDANA*
💖💚💖💚💖💚💖

*Written by*
*Rabee'atu .B. Abdullahi*

(Ummu Maher)
*Y'ar mutan Nigeria*🇳🇬🇳🇬🇳🇬💚🤍💚

*Page 66&67*

"Yarima kuwa yarasa yadda zaiyi da rayuwarsa dai dainan'Yaya Nura yazo wucewa ya hango'Sagir ya k'araso suka gaisa" Amman haryanzu nutsuwarsa bata jikinshi gaba d'aya'Ya bud'e motarshi yabawa Nura Yace wannan kabawa "Inna wannan kuma " Humaira.

"Yayi mai godiya shi kuma ya shiga motatshi ya yafi'Cikin B'acinrai,Yana shiga gida cikin b'acin rai yayi b'angarenshi da ka ganshi kasan baya cikin kwanciyar hankali,yana zuwa ya cire kayanshi ranshi na soya yashiga cikin Bab'Wajen wanka ya kwanta aciki'sannan kuma ya kunna shaya nandan ruwa ya Fara ambaliya.

" Shi kuwa Yarima Yana cen yana tunanin "Humaira Tunda yake bai tab'a cewa yanason wata Y'AMACE ba Hasalima shi baisan yadda zaice yanason Mace ba Amman yau ya furta shi kansa baima San ya furta ba Nandai ya cigaba da tunanin shi kwakwalwarshi kamar zata tarwatse saboda tunani Kala Kala.

" Fulani kuwa suna zaune da jakadiya"Tace waini Bara'atu Kinga kuwa"Yarima ya dawo Sam banji alamun hakanba,Jakadiya Bara'atu tace Hmmm Aini kam d'azu naga "Sha rubutu"Yace mun Yarima fa yau cikin b'acin rai ya shigo" Ta durkusa cikin girmamawa Tace'Ranki ya Dad'e yanzu daman Zan gaya miki kuma kika rigani"Fulani tace haba "Bara'atu kinsan halin Yarima da zuciya'Kuma kinsan zurfin ciki gareshi ba zaice ga Abinda yake damunshi ba kuma kikayi shiru'Baki kyau taba" Bara'atu Yanzu zo muje suka tashi"Fulani na gaba Bara'atu tana binta.

"Yarima kuwa tsabagen tunani har ya Fara nitsewa cikin ruwan nan gaba d'aya lokaci guda idonshi sunyi jawur kamar gauta.Dai dai lokacin Fulani ta shigo'da Bara'atu suka hango band'akin arufe ga ruwa yana fitowa ta k'asa cikin tashin hankali sukayi k'ofar ban d'akin Sukayi k'ofar ta bud'e tak'i bud'ewa ga numfarfashi suna ji daga ban d'akin.

" Fulani cikin tashin hankali,tace Bara'atu kirawo min barde tace toh"Tana fitowa kuwa ta hango shi ta kirawo da gudu shima ya nufo bangaren Yarima,Yana zuwa yayi kukan kura ya bud'e k'ofar saiga ta ta wangale.

"Yarima suka hango cikin ruwan Har yafara nitsewa cikin tashin hankali Barde ya fito da Yarima,ya kwantar dashi akan gado,,Yace Ranki ya Dad'e ya suma fa,Nanfa aka ringa matsa cikinshi zuwa k'irjinshi,ruwan yana fitowa a hankali yayi atishawa.

" Yarima ya farfad'o"Fulani tana kuka tana cewa haba "Sagir akan b'acin rai zaka kashe kanka to Bari kaji duk Wanda ya kashe kanshi Saboda,wata damuwa to shi d'an wutane kadinga control d'in kanka shi mutun anason yadinga hak'uri da rayuwa,saboda arayuwa dolene sai kayi hakuri.

"Yayi ajiyar zuciya Yace'My mom kinsani ni mutun ne mai naci'Inason in Auri " Humaira i'nason ta sosai wallahi'Idan ban Aureta ba wallahi nasan mutuwa zanyi,bansan ya akayi,Sonta ba ya kamani da yawa haka ba.Amman bata sona bata ra'ayin Aure ayanzun ni kuma Aure nakeso'Kuma Humaira nakeso.

"Fulani ta jiyo ta kori su'Bara'atu da Barde,Suka fita suna mamakin Abinda " Yarima Sagir yake furtawa,Suna fita Barde yake fad'awa Waziri'Waziri kuwa ya fad'awa Sarki,Nandanan saigashi hankalinshi atashe yayo bangaren yarima.

"Yana zuwa ya talloboshi yana yimai sannu'Yace Fulani meke damun shi Nanfa tafad'amai komai'Cikeda mamaki Yace to A'i Fulani da wuri ya kamata kifad'amun kamar bakisan yadda nake jin" Yarima to yazama min wajibi nemar mai farin cikin,Fulani tace to Ranka yadade kana ganin haka zaiyiyu A'i gwara abi abun a hankali KO,Ya kalleta Yace babu komai da kaina zanje ba d'an sak'o Zan turaba.

************

Washegari da wuri aka shirya komai sarki da Waziri ne kawai Sukayi tafiyar'Suna zuwa Unguwar suka hango"Mahaifin Humaira da Baban Khadija suna hira'Sarki dakanshi yaje ya basu hannu sukayi musabaha'Babansu Khadija Yace Ranka ya Dade yau Kaine akofar gidan namu da kanka,Ya kalli Mahaifinsu Humaira Yace Mai martaba nefa dakanshi yazo k'ofar gidan nan,Mahaifin Humaira ya fad'ad'a fara'arshi Suka gaisa sosai cikin mutuntaka.

"Nandai waziri yafad'a musu abinda ya kawosu sukayi Na'am da maganar tasa,Saidai sunyi ce mai yarinyar bazawara ce sai an tuntub'eta tukun anji ta bakinta.

" Nanfa suka ajje musu Y'an rafas din kud'i,Fir suka k'i amsa saida ya b'ata rai Sannan Mahaifin Khadija ya amsa,Bayan Abbana ya shigo gidane Yake cewa Inna yana son zuwa gobe KO Wani d'an shi ya hallara'Inna ta tambayeshi KO lafiya Yace eh Tace to Allah ya kaimu.

****************

"Washegari kuwa kowanni d'an shi ya hallara donjin abinda zai faru,Humaira Abbana ya kirawoni,Na'Amsa ya kirawo KO wanni d'an shi suma suka amsa,Nandanan babu b'ata lokaci ya fad'a musu abinda ya kawosu Mai martaba gidan su,Neman Auren Y'arsa" Humaira da d'ansa "Sagir.

" Nanfa kowa abun ya bashi mamaki sosai,Kowa Nanfa suka amince don"Sagir da Mahaifansa mutanen kirkine,Nan danan Humaira ta Fara kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.

"Abbana ya kalleni yace " Humaira bazan miki dole ba illa i'nason ingaya miki Aure shine gatanki A'yanzu bai kamata kizama kullum cikin tunani ba"Yaron nan har ciwo fa Yayi akanki ki tausaya mishi"Humaira duk Wanda yace yana sonka A'i ya gamai maka komai,I'nason kifad'amun kin amince KO kuwa.

"Bansan sanda bakina ya ambata na aminceba,Hamdala duka y'an uwa na Sukayi suna godewa Allah,Ni kuma na tashi na koma d'akina kamar zuciyata Zata fashe,Abbana Yacewa Y'an uwa na gobe ba jibi ba za'ah d'aura Auren.

"Washegari kuwa tuni Adaren Abbana yagayawa Mahaifin" Yarima Nanfa aka Fara shirin D'aurin Aurena da"Sagir,Dibban Jama'ah Suka taru'Inda Aka d'aura Aurena da'Sagir Akan sadaki na zinare da kyautar gidaje har biyu dankara dankara.

*Wayyo 😀😢 Allah na Zanso Naji Yadda za'ah karke"Yarima Sagir Ango da Amarya"Humaira🥰🧐🤪🥳🤩🥳🤗*

*Ummu Maher ce*
*Vote*
Share
And
*Comment*
[11/10 16:23] 💖Rabee'atu Ummu Maher💖: 💖💚💖💚💖💚💖
*UWAR'GIDANA*
💖💚💖💚💖💚

*Written by*
*Rabee'atu .B. Abdullahi*
(Ummu Maher)
Y'ar mutan Nigeria🇳🇬🇳🇬🇳🇬💚🤍💚

*Page68&69*

***********

Ina zaune zuciyata kamar zata fashe sabuda bak'in ciki Na'amincewar da nayi na Auren'Sagir'Na rasa yadda zanyi da rayuwata bak'inciki goma da ashirin wani irin kuka nakeyi'Mai cin rai da k'una.

Inna ta shigo ta kalleni "batayimun magana ba ta fita ranta ab'ace'tana fita najiyo muryar " Hamida suna gaisa,tana cewa Ina Amaryar ta kene'Inna tace tana d'aki.

Rik'e baki"Hamida tayi tace ikon Allah mezan gani'Humaira me akayi mini,Ai k'ara rushewa nayi da kukana Inacewa"Hamida narasa yadda zanyi da raina'Allah yasani banason "Sagir hasalima ban shirya Aure yanzunba,Saboda maza basu da Amana.

Hamida " Tace Humaira me yasa baki karb'ar Jarabta'Shifa Allah yakan jarabci bawane don ya gwada imaninshi'Idan mutun yanada imani saikiga ya karb'i jatabtar hannu biyu kiyi hak'uri,ki zauna da"Sagir lafiya komai yayi farko zaiyi k'arshe kinji.

Na kalleta Nace waini haryanzu baki gane me nake nufiba nifa banisonshine Na tsaneshi waini ma wannan yaron Zan Aura haba dai ni Wallahi bazan zauna dashi ba saina rushe da wani irin kuka mai k'arfi.

Hamida don haushi ta tashi ta fito zata fita,gaba d'aya ranta ya b'aci sosai,na janyo gefen zaninta Ina cewa"Hamida don Allah ki dawo bani da wani Wanda zai bani shawara nasan kece daga ke sai Abbana Ku kad'aine kuke bani shawara don Allah kidawo'Ita abunma dariya ya bata Tace to aini"Humaira abin naki ma dariya yake bani matuk'a ace mutun yasaka kanshi cikin matsala kullum kana cikin tunani,shifa Wanda kakeyi donshi baisan ma kanayi ba Amman duk mutun, yasaka kanshi cikin matsala,ta kalleni tace to "Maher din da kikeyi donshi ayanzu yasaka matarshi gaba ma basa k'asar sun nausa" London da y'arsu don haka sai kisan inda dare yayi miki.

shiru Nayi ina kallon"Hamida Nace gaskiya maza basu da adalci KO kusa ki duba fa kiga yadda fa nake kullum cikin tunaninshi Insha'Allah daga yau bazan k'ara kuka akanshi ba na karb'i k'addarata Insha'Allah na daina"Hamida.

Hamida"Tace Humaira kinsan meye yanzun ki karb'i kaddararki ki tsaya ki gyara jikinki kiso mijinki yadda yakesonki'ki soshi tsakani da Allah sai kici ribar zama dashi nace to,Nanfa mukayi ta hira,ta fito da wasu abubuwa Kala Kala nanfa ta nunamun yadda akeyinsu wani daga wajensu Aunty Maryam ta amso wai kunyata sukeji.

Nayi dariya na amsa sannan ta d'aukomun na wajen Malam Abubakar ta nnunamun yadda zanyi dashi da turare da wasu Addu'o'i Na amsa nayi Mata godiya.

Sagir kuwa shiri yakeyi kamar Ranar Sallah yasa ka shaddarsa matuk'ar kyau da tsada,ya fito yayi sashen mahaifan nasa ya gaushesu bakinshi har kunne,Fulani "Tace Babana Ango agaishemun da Y'artawa,Mai martaba yayi dariya " Yace to kasan dai mu gidan sa rauta idan aka D'aura Aure Amarya za"ah kawo mana ko'Sosa k'eya yayi ya fito yana dariya.

Yana isowa k'ofar gidanmu Munfito nida"Hamida tana bani number wacce zata zo donyimun gyaranjiki,Na hangoshi yayi kyau sosai cikin shigarsa sai kyelli yakeyi.

Na maze Zan wuce"Hamida tace haba"Humaira Mijinkine fa kike Neman wucewa,Sannan na wuce raina baiso ba don ni haryanzu gani nakeyi mazan duka d'ayane.
Chapter 16 · 0% Book details