← Book details Uwar Gidana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 19

Sashe 13

Uwar Gidana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Nanfa wuri ya kaure da murna,Anan nasake kiran layin Yaya ya d'aga yana cewa "Uwargidana kiyi hak'uri bana kusa da wayarne naga kiran ki da safe munje wani meeting ne nasakata a silent,Nace oky to congratulation Munyi Y'a dai dainan aka fito da yarinyar Fara Sol mai kyau Kama ta keyi da'Khadija sosai.

" Momi fa tarik'e yarinya tak'i bawa kowa. Yace A'i yanzu zantaho Amman turomun pics d'inta ingani Nace toh ya kashe wayar.Naje na d'auki hoton yarinyar har biyu "Momi kuwa sai gallamin Uwar harara takeyi.

" Na turamai ya bugomin yana cewa gaskiya Tunda kikaimin wannan albishir d'in Zan baki wani babban gift nayi dariya,Yace kinsan wannane'Nace A'ah yace saina dawo zakiji saiya turomun hoton k'aton ciki dariya nayi wato yana nufin ciki kenan,a take naji kamar zanyi kuka tunowa da nayi da ni bana Haihuwa.

*Ummu Maher ce*💚💖

*Vote*

*Share*
And

*Comment*
[11/10 16:20] 💖Rabee'atu Ummu Maher💖: 💖💚💖💚💖💚💚
*°°•°•UWAR'GIDANA*°°•°•
💖💚💖💚💖💚💚

_Written_ _by_
*Rabee'atu .B. Abdullahi*
{y'ar mutan Nigeria}🇳🇬🇳🇬🇳🇬🇳🇬
💚🤍💚

*🖊️⚔️ALK'ALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOCIATION⚔️🖊️*📚🔎🔍
*{A.Y.T.W.A}*🖊️📕📗📘📙

"K'ungiyar da ta kasance ta marubuta masu fasaha da sanin ya kamata.✍️

wannan page na kune

*Nabeela Dikko*
*Nabeeha Aminu*
*Nimcy Love*
*Farhat Osman*
*Zahra'u Naseer Aliyu*
*Amina Muhammad baso*

da dukkanin masoyan wannan littafi🙏🏻

"I'love this page💖💚

kuji dad'inku da wannan page inayinku sosai up up up kuna wuta__ 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*{بسم الله الر حمن الرحيم}*

*🅿️53&54*

_____" tuni nafara kwallah saboda tunanin KO wanni i'rin hali Zan shiga i'dan akace ban haihuba,Ina cikin wannan halin ne naji "Innarmu na cewa Humaira ki fad'awa su " Maryam da Murja da Hafsa Sha'awa "Khadija ta haihu ansamu y'amace'Nayi shiru cen " Innah tace Humaira dake nake fa nace to Innarmu Bari na fad'a musu tace toh bayan nafad'a musu ne,Likitan ya kirawoni yace mun daman sai anjima zamu sallameta saidai fa zata dinga zuwa karb'ar magani saboda tahad'u da matsalar yoyon fitsari saboda doguwar na k'uda da tayi, don haka bazamu sallameta da wuriba kina jina kifad'awa Mijinta don yasani.

°`tunda ya Fara magana nake sauraronshi Ina kallon shi saboda abun yayi matuk'ar bani mamaki daman har yara ma sunayin wannan yoyon fitsarin likita Yace to yanzu dai da yau zamu sallameta Amman sai zuwa gobe muga yadda jikin Nata yake nace to,Gab da Zan fita wata Mata ta shigo y'ar kyakyawa da i'ta hararata tayi ta wuce "likitan ya cire d'an farin gilashinshi Wanda ya k'ara mishi kyau don kyakyawane sosai kamar balarabe. kafun in fita naji tana cewa Wallahi " Sadiq kabani mamaki daganan kuma banji me tace ba nafita...

"Ina fitowa na iske su 'Momi da Su Innah sai su Aunty Maryam hardasu " Hamida ma duk sunzo 'Muka gaisa duk suka tambayeni ya me jiki nace da sauk'i na hango"Momi sai wani hararata ta keyi "Na ce Innarmu bayan nashiga wajen Likita ya ke cemun A'i " Khadija tana fama da matsalar yoyon fitsari..........A'i tunkafun in k'arasa najiyo "Momi nacewa keh'dakata munafuka d'iyar mayu keh har kin i'sa kice zaki rainamun wayo to Bari kiji kuruwar " Khadija tur dake 'Saboda kin yi gadon sharri shine zakice wai wannan ficiciyar Yarinyar kamar"Khadija tana fama da ciwon yoyon fitsari to Allah yafiki munafuka kawai.

"Kowa da yake wajen saida yayi mamakin irin furucin i'rin furucin da" Momi tayimun hatta "Innarmu ma saida ta girgiza awajen don jin furucin" Momin Maher.

"Aunty Maryam kuwa tace Hmmm to A'i gadon mayu ba'ah gadon mu take ba agadonku take kuma wallahi idan kika sake wannan furucin wallahi saikinyi Dana sanin irin halin daza kishiga Kafun ta rufe bakinta " Aunty Murja ma ta d'ora da cewa waike "Momi mekika d'auki duniyane kinbi kin saka y'ar mutane agaba da zagi da cin mutunci kibar ganin " Khadija k'anwata ce kiyi tunanin zagin "Humaira agabana da kuma danginsu kiyi tunanin zanyi shiru to A'i abinda yayi su " Humaira shi yayi mu,don haka Wallahi adaina zagar mana y'an uwa "Aunty Sha'awa ma tace " Tab'jar uba daman abun yayi tsamari haka to A'i naga KO mutuwa tana tsoron idon uwa Amman sai kace wata bama gujiya babu KO kunya ayita zagin mutun haka.

"Innah kuwa cewa tayi haba meyasa Baku da kunyane Ina ruwanku banason i'rin wannan Ku Kama bakinku bana son fitsara," Momi kuwa cewa tayi A'i lallai wad'annan yaran iskancin naku yakai kuce zaku zageni saboda an koya muku zagi to wallahi Bari "Maher d'in yazo Wallahi sai Sake ta muga abun da zatayi.

" Innah kuwa furucin "Momi da tayi ya girgizata sosai,don haka tace wa su" Aunty murja Ku taho mutafi gida dukanninku'Tace har sake"Humaira muka fito dukkaninmu suka shiga motata najasu zuciyata gal"Bak'inciki kwata kwata shekaruna 21 aduniya wanda yayi dai dai da shekarata Hud'u agidan Mijina"Yaya Maher, Amman na had'u da matsaloli Kala Kala.

"Muna zuwa gidana muka fito daga cikin motata Innarmu tace toh " Humaira zamu zauna anan zuwa yamma don Gaskiya abunda yafaru yayi matuk'ar girgizani.

"Da yamma bayan sun tafi sun rarrasheni sosai Sannan suka tafi gida,Ni kuma na tashi nayi wanka sai naga kiran " Yaya ya cemun ya taho Amman zai Fara zuwa asibitin nace to Allah ya dawo dakai lafiya ya cemun Amin.

"Wata sabuwa Ashe matar da nagani a'asibiti tazo wajen" Doctor Sadiq Ashe matarsa ce kuma wai tana zargina da Mijinta.

"Kuma bayan ta fito daga office d'inshi sun had'u da " Momi bayan sungaisane a gaggauce saboda "Maryam akwaita da kishin jaraba sosai,Kuma har d'aukar hoton su tayi Tunda lokacin da ta shigo Office d'in. kuma " Maryam muguwace bata da imani KO kad'an.

••Momin Maher tace wayyo gaskiya na tausaya miki bayanda "Maryam d'in tafad'awa " Momi zarginda ta kewa"Mijinta da 'Humaira baiwar Allah,Nanfa Momi tace yo aini matar d'ana ce tace To muga hoton tananu Mata,Momi tace i'nason Alalata hotunan ya zamanto duk Wanda yagansu ya yi tsammanin cewa akwai wani abu ak'asa suka saka dariya i'ta da "Maryam .

." To Maher yana isowa ya nufi asibitin"Momi na zaune da jaririya a hannunta sai ta hango Maher yana fara'ah sosai bakinshi kamar gonar Auduga.

"Momi ta maze don tasan abinda ta k'ulla i'ta da Maryam matar" Doctor Sadiq,Yana zuwa ya gaida Momi ta mik'omai jaririyar.ya amsheta yana fara'ah suna cikin gaisawa ne"Maryam ta shigo asibitin kamar mahaukaciya'Momi ta kalleta ta gefan I do tana murmushin mugun ta tazo zata wuce ta bangaje "Momi.

" Momi tace haba yarinya kina cikin hankalinki kuwa zaki bugeni ki wuce sai Sannan"Maher ya d'ago kansa wayar ta ta sub'uce a hannunta ta sunkuya zata ta d'auka abinda "Maher yaganine ya zabura yarigata d'aukar wayar" Maryam kuwa tace Dan Allah Malam bani wayata kada kaganar min SIRRIN mijina,Maher yacewa "Momi Kinga fa abinda nagani wannan ba" Humaira bace"Momi jikinta na kakkarwa tace A'i wannan"Humaira ce wa'ya zubullahi.

"Momi tayi saurin yin gaba Da hoton saiga wani yataho shima hotonne Wanda" Humaira take kallonsa kamar Zata cinyeshi.

"Maher cikin saurin ya yi wurgar da wayar yayi saurin wucewa yana wuci.

*Ummu Maher ce*.✍️yar mutan Nigeria🇳🇬💚🤍💚

vote

share
And
comment
[11/10 16:20] 💖Rabee'atu Ummu Maher💖: 💖💚💖💚💖💚💖
*°°•°•UWAR'GIDANA°°•°•*
💖💚💖💚💖💚💖

*Written by*
*Rabee'atu .B. Abdullahi*
{Y'ar mutan Nigeria}🇳🇬🇳🇬🇳🇬
💚🤍💚

___________

*🖊️⚔️ALK'ALAMI YAFI TAKOBI WRITER'S ASSOTION⚔️🖊️*📚🔍🔎

*{A.Y.T.W.A}*🖊️📕📗📘📙

K'ungiyar da ta kasance ta marubuta masu fasaha da sanin ya kamata.✍️

*🅿55&56*

"Maher kuwa gudu yake a motarshi kamar zai tashi sama tunanin yakeyi acikin zuciyarshi daman " Humaira tana cin amanarshi awaje da wannan likitan mai Kama da Aljanu to wallahi daga yau zai kawo k'arshen abun in yaso taje cen tayi awaje'Kanshine yaji yana saramai wani wawan burki yaja yayin dayayi dai dai da tsayawarshi k'ofar GIDANSHI.

"Yana fitowa ya bud'e k'ofar parlon da k'arfin gaske saidai" Humaira ta tsorata d'an kunnen da ta kesakawa ya fad'i k'asa.tayi saurin fitowa daga d'akin tayo parlo tana zuwa ta iske Maher ya bud'e k'ofar d'akinsa da k'arfin gaske,tsoro abin yabata don ba k'ara min firgita yayi ba tace a zuciyarta yanzu fa mukayi waya dashi cikin kwanciyar hankali to me ye yata damai da hankali?.

"Tana budewa ta iskeshi yacire rigarshi daga shi sai troxer ya d'aga kanshi sama idanunshi sunyi jawur kamar garwashi gashin jikinshi ya mik'e sosai.Ina zuwa kusa dashi "Nace Yaya sannu da zuwa me akayi maka naga kamar ranka ya b'aci, har lokacin bai d'ago ba kuma bai kalleni ba balle i'nsaka ran zai amsamin.

" Na tashi daga inda nake na matsa inda yake,Na rungumoshi ta baya'Ai tun ban kaiga gama rungumeshi ya tattaro dukkanin k'arfin shi yayi wurgi Dani gefe Na daki glass ji kake tasss...Go shina ya fashe saiga jini tuni na Fara kuka mai sauti ga azabar da goshina ya keyimun kamar zai fashe.

"Ya nufo inda nake ya ca kumoni Yana wani gurnani kamar tsohon zaki'Yace ni zaki ciwa amana " Humaira dame na rageki meye bana yimiki shine zaki dinga ha i'ntata abayan i'dona to Allah ya Toni asirinki,Ya k'ara hankad'ani na fad'i sosai Ina kuka Ina yunk'urin tashi ya fincikoni ya watsamin maruka har biyu saida naga wucewar taurari.

"Tuni nafara ganin duhu duhu'Ya d'ora da cewa" Humaira na sakeki Saki Uku kitafi gidanku'Sai ya fashe da kuka ya fita daga d'akin.

"A take nima na fashe da wani irin kuka mai ban tausayi,to me nayiwa" Yaya da ya d'auki wannan mummunar matakin akaina "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Kalmar Dana ringa mai mai tawa kenan afili da zuci.

" Na tashi Ina bin bango na bud'e Sif d'ita na bud'e Ina kuka mai cin rai na d'ebo kayana da bansan KO Kala nawa ne ba,na saka acikin d'an k'aramin Akwatina na d'auki ma kullin motata na fito Ina k'arewa d'akina kallon karshe.

"Ina fitowa na dinga kallon gidan Ina kuka sosai,Na bud'e motana na shiga ciki,Saidai na dad'e kafun in Fara tuk'ida kyer na daurewa zuciyata,Na Fara tuk'i Ina kukan ba k'inciki na Mijina Wanda nake so nake k'auna Wanda na yarda duk rintsi duk wahala bazan I'ya rabuwa dashi ba,Sai gashi shi ya rabu Dani akan laifin da ban sanshiba.

'koda ace yau" Maher zai mutu to da saidai in mutu banyi Aureba,Kalamanshi sai yawo sukeyi acikin zuciyarta A take na tuno kalmarshi ta k'arshe da yace ya sakeni Saki uku,Sai na kwallah wata k'ara a take na to she kunnuwana.
Chapter 13 · 0% Book details