← Book details Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 15

Sashe 7

Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Washegari aka sallame ni na dawo gida da kundurin cusa
son Adams a zuciyata don haka duk sintirin da yaynmu
yake yi bai burgeni ba duk da in har ina ganshi sai
gabana ya fadi, kuma sonshi na nan daram a raina,daren
ranar sai ga Adams ya zo mani sallama yana min
bayanin dan dai zasu yi wani wasa ne a club dinsu kuma
wasan yana da muhimmanci sosai da ba zai tafi ba gashi
ba Maska bai kamata kuma shi ba ya nan ba,nace ba
komai naji sauki kuma ga waya ai,ya ce to bani no naki
in yaso in naje sai na dinga kiranki sannan ki bani
tabbacin kina sona dan Maska ya gaya min kina da
wanda kike so,haka ne?nace batun wanda nakeso dai bai
taso ba dan babu sai dai game da kai,in mun waya zan
sanar da kai ina jin kunya ne yanxu,yayi murmushi shi
kenan yar gidana a zuciyata nace kunyar karyar da zan
maka ne ya sa ba zan iya fadama baki da baki ba dan na
san ba wani sonka nakeyi ba ne burgeni kawai
kakeyi,kyautar wani kyakkyawan agogo da turare ya yi
min nayi mishi godiya mukayi sallama sannan yace min
idan ya sami sukuni zai zo ba da jimawa ba kuma jiya ya
gabatar da kanshi a gurin Alhj,da sauri na dubeshi me
yace maka?ya ce yace kar na damu gurin su manya ba
matsala in dai sunyi bincike sun gano asalina a
Ghana,nace yauwa Adams kana da yare ne?ya ce eh
yace mu asalinmu fulanin yola ne yan Adamawa zama ne
yakai kakaninmu suka haifi iyayenmu muma aka haifemu
a Ghana,nayi karatuna duka zuwa Degree wasan kwallo
kuwa ina primary nake zakara kuma ni ne babba a kaf
gidanmu kanne na hudu maza da mata,matan babana
biyu ne kuma har ynxu muna zuwa Adamawa kuma suna
zuwa babana yana da sarautar matawalle dan haka duk
salla familynmu a can muke yi ko ni in ina gida tare
muke zuwa,kin fahimci takaitaccen tarihina? nace na
gane yace to muna da yawa sai ki shirya in munyi aure
duk sallah zamu zo daga England Adamawa zamu sauka
haka nan in kin haihu a can zaki zauna ko in baby yayi
kwari sai nazo na tafi da ku dariya nayi nace Adams
kenan har ka tsara komai yace yes haka kullum nake
mafarki nace to ba ka fadamin me kayi Degree a kai ba
sannan cikakken sunan ka,yace nayi Degree
akan,cikakken sunana shine Adamu Salisu Adamu,
Abokaina su suka sa min Adams sai ya zama har JC na
Adams suka samin kinji yanda abin yake,sai naji Adams
ya kara bani sha'awa kuma zan iya kukutawa in aure
shi,mun yi sallama dashi nayi mishi rakiya har wajen
gate mukayi sallama akan sai naji shi a waya.

Ni,Mami da Amira tafe muke kan hanyar mu ta zuwa
kasuwar unguwar Rimi zamu raka Mami ne amsar dinki
muna tafe muna hirar Adams,nace mami ni fa yanxu
Adams kawai na tsaida ma zuciyata duk da na san cewa
bashi ne zabin zuciyata ba zai fi min kwanciyar
hankali,Amira tace na goyi bayanki Mami tace sam ba
zata yiwu ba kina tunanin shi ba wata matsala daga
dangin shi?sannan ba shi kike so ba in kika jure wani
abu wani ba zaki jure ba musamman ma da yake ba shi
kike so ba gara wanda kake so zaka hakura da wani
abun albarkacin son nan shiko daban ne,nace Mami Haj
Yaya da Haj Laure ba zasu bari na zauna lfy ba sannan
da wanda na ke sonshi baya so na gara wanda nake ki
yake sona zan lallaba da Adams,mun tsallaka daidai
shagon Ubale zamu shiga cikin kasuwa sai ga wata mota
ta tare mana gaba baka ce wuluk Mami tace motar nan
tayi min kyau,kafin nayi magana har mai motar ya fito
wani mummunan fduwar gaba naji yayin da muka hada
ido da mai motar,shima ni ya tsura ma ido yana kallona
mami ta ce kin sanshi ne?nayi karfin hali nace a'a naja
hannun Amira jikina ba karfi sai mutumin yace uwata ni
zaki gani ki wuce uwata?kin bani mamaki uwata zo kar
ki tafi ina Habiba?

Sai na soma kuka mai karfi mutane
kallona sukeyi ya bar jikin motar ya nufo ni da gudu na
tsallaka titi na nufi layinmu ina jiyo muryar shi yana fadin
uwata kar ki kuma tfy ki barni zo mana mamana,ai sai
gida ina tafe ina kuka kamar wadda aka ce uwarta ta
mutu ban damu da kallon da mutane suke min ba jikin
Mama na fada tana zaune a firgice ta tashi tana fadin
lfy?menene?

Ina sai kuka ruri nake Mami da Amira suka
shigo a sukwane Mama tace Amira me ya faru?
hankalinta a tashe ta ke magana Amira tace mama
muna tfy zamu shiga kasuwa sai muka ga wata mota har
muna cewa kai motar ta hadu kawai sai mai motar ya
fito yana ganin Iman kawai sai mukaji ya hau cewa
uwata dama kina nan uwata?zo nan kawai sai muka ga
tana kuka ta rugo shine mutumin yace mun san gidansu?
mukace eh shine ya dauko mu ynxu yana nan waje wai
mu kiraki,mama tace baku da hankali daga ganin mutum
sai ku nuna masa gidanku?dama ya tafi daku,ta daka
masu tsawa me zakuje ku ce masa ba zan fito ba a ina
ya sanni,Amira da Mami suka kada baki wllh mama yayi
kama da Iman sosai mama tace ba shi bane nace kuje
ku sallame shi mana,cikin kuka nace mama baba ne
fa,mama tayi shiru dama nasan ta gane can sai tace
Amira kije kuce mishi mijina baya nan dan haka ba zan
iya ganinshi ba su Mami suka sameahi ya kifa kai jikin
sitiyarin mota mami tace baba da sauri ya juyo yaushe
rabon da yaji wannan kalmar yana kishin jin kalmar nan
ga zatonsa Iman ce amma sai yaga yaran dazu,ya
dubesu ina Habiban?suka ce tace mijinta baya nan shi
yasa ba zata iya ganinka ba ba.
Chapter 7 · 0% Book details