Sashe 2
Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Nayi sallama a dakinshi da tire a hannuna
shi kadai ne zaune kan kujera na ajiye tiren sannan na
gaisheshi ya bude kula me kika kawo min?nace gashi
nan dai duba,yace to sauran ki hada min kayana nace
wane kayan?yace gasu can kinsan yau zanyi kaura shine
nake aon insa kabir ya kai min kayana haushi ya kamani
ban ce komai ba na shiga dakin a raina nace me shegen
zumudin tsiya kawai,ba karamin gajiya nayi bada hada
kayan nan akwati hudu na cika banda wata jaka babba
wasu kayan ma ina ganin bai taba sa su ba,yawanci
kananan kaya ne manyan akwati daya na cika ga kuma
sauran nan cikin durowar kayan shi itako babbar jaka
duk JC ne da sauransu,na gama ina shirin fitowa naji
sallamar Haj yaya can cikin falon ya amsa sannan ta
shigo tana fadin kai da waye naga takalmin mata?
gabana ya fadi a sauri na shige bayan labule na boye ya
amsa mata da cewa ni kadai ne ta leko bedroom din tana
fadin wannan kayan fa?yace ina shirya su ne don inason
kabir ya kai min can gidan yakubu avenu,ta karasa
shigowa cikin bedroom tana fadin matsalarka kenan baka
son manyan kaya sai aukin dinkasu tazo kusa dani ta
tsaya tana kallon kayayyakin ni kam jikina rawa yake a
bayan labule gashi bata magana a hankali don tunda
dama haj yaya mafadaciya ce don haka ko maganar
arziki takeyi sai kaji tamkar tana fada ne,Yayanmu yana
tsaye a bakin kofa yace Haj menene kike nema ne tace
magana zamuyi yanzun maganar kayan nan fa ba kace
komai ba?yace kaya gasu nan ki diba dama inason rage
ma kabir ne don sun min yawa sosai kinga fa ko abikin
nan Nasir abokina set ashirin ya dinka min kuma duk
acikinsu ba yadin dubu goma sai sama da haka Haj tace
ina ruwan Nasiru, ta cigaba dama zancen da nake son in
maka akan abubuwan da kake yine,so nake ka gaya min
menene tsakaninka da yarinyar nan Iman?ta kuma daga
murya iye kai nake tambaya duk iskancin da kakeyi fa
ina sane kar kayi zaton ban sani ba ina daga kafa ne kai
amma naga alamar sai na warware ka naci mutuncinka
ko na tozarta ka ko?sai sannan yayi magana haj tsaya ki
jini ya shigo shima zo muje falo miyi wannan zancen don
Allah ta bishi suka fita tana fadin nidai ka fita hanyar su
bana son hulda da Habiba da ahlinta yace Haj zauna
suka zauna duk da kasa kasa yake magana ina jiyo shi
daga inda na sandare don na tabbata in har tasan ina
dakin kashi na sai ya bushe,yace Haj kin ga yarinyar nan
tana dawainiya dani tunda na dawo garin nan abinci
gyaran daki aike bafa biyanta nake yi ba sannan......ta
katse shi,don Allah ni rufa min bakinka baka da kannan
da zasuyi dawainiya dakai?yace to Haj su wadannan
yaran me suka iya?sam yarinyar nan ta fisu iya
komai......ta kuma katse shi tunda an baka kaci kasha an
baka cikin abinci ka kiyayeni, rannan aka ce min ka
dauketa cikin motar ka, kaf gidan nan baya ga Kabir wa
ya taba shiga motar?ko ni nan da na haifeka ban shiga
ba na biyu kaimata dinkuna masu tsada ba kaima yan
uwanka ba don wulakanci kuma sai ka ringa masu anko
da matar da zaka aura,sannan jiya har cewa akayi ka
rungumeta ko ba haka akayi ba?cikin daga sauti yace inji
wa?Haj ki daina jin irin wannan surutan da shiri ne
maganar shiga mota ta kuma kasuwa muka je ta siyo
kayan abinci da aka shiryawa abokaina da suka zo daga
England suka sauka gida Nasir,dinki kuma yana da kyau
ka kyautata ma mai kyautata maka sannan ni ban wani
rungumeta ba duk surutu ne,tace su Haj Lauren ne suke
maka surutu ne?yace to in banda abun Momi mene nata
na zuwa gun lunchn abin yara tsakani da Allah...ta katse
shi to ni ynzu magana ta ta karshe shine ana gama bikin
nan ka tattara matar ka ku tafi England,ya danyi shiru
sannan yace Haj mai ya kawo maganar tfy da mimi,kinga
fa ba gida ke gareni ba a hotel nake ya zan kai matar
aure hotel?tayi tsaki zancan banza ne kakeyi ba zan
amince ba kaje da ita ku zauna a hotel din tare ta ahiga
faa don kar ya soma magiya ni zaka gaya wa zancan
banza?bari kaji wllh wllh ba ka isa in maka kaffara ba
tare zaku tafi in kuma zaka nuna min cewar ban isa
bane to ina jira ta numfasa sannan ta cigaba hankalina
zaifi kwanciya in kuna can bata jira yayi magana ba ta
fice abinta ya bita a baya don Allah haj ki min hakuri
mana,ko sauraronshi batayi ba
jikina sharkaf da zufa na fito daga bayan labule a gefen
katifa na zauna ina maida numafashina sama sama idona
sharkaf da hawaye ba wai ina kukan cin fuskar da tayi
min bane a'a ina kukan tafiyar da zasu yi,don ina ganin
in har ya tafi da ita ni kuma shi kenan ba zan dinga
ganinshi ba zanji muryarshi ba ba xanji kamshinshi
ba,tsaye yake bakin kofa yana dubana ya shigo tashi ki
shiga ciki share hawayenki kinji karki damu wata rana sai
lbr cikin sanyin murya yake magana na mike ya matsa
min na wuce.