← Book details Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 15

Sashe 11

Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Adamssalin tara text din da aka saba yi min tsawon
watanni kullum ba fashi ya shigo,very soon zamu
kasance tare domin nasan i am always lucky akan duka
abinda nakeso,ban ma gama dubawa ba na kashe yau
kamna gane Adams ne yake min text yana boye no
haushin shi ya kara kamani na hau fada ina cewa nufin
shi sai ya min haka zan so shi?to yayi kuskure ni ba
sonshi nakeyi ba zan dai aure shi ne dan hujjar da na
ba yaynmu nace kai bari ma in mashi karara don ya
daina damuna na soma neman layinshi ai cikin sa'a na
sameahi ashe lokacin suna tare da yaynmu a wani club
ya dubi yaynmu yace ga yar gidana sannan ya dauka,in
kaga yaynmu zaka dauka bai damu da wayar da Adams
keyi ba amma ya tattara dukkan hankalinshi gurin
sauraron Adams dan ta maganr da Adams keyi zaka
gane me nace,ni kam Adams na dauka nace hello
Adams menene na boye no kana yi min text in ma kana
yi ne dan ka birgeni to wllh haushi ma kake bani,tunda
na soma maganar bai tare ni ba sai da nayi shiru,yace
calm down my wife wllh ba ni bane ba ban ma taba yi
maki text ba nace to wanene?ina zan sani inji adams
sannan yace don Allah kiyi hakuri karki damu kanki
kashe na kiraki,nace yanzu zanyi shafai da wutiri ne sai
da safe yace sai da safen yanda ya amsa har tausayi
ya bani,Maska ya dubi Adams dan san jin karin
bayani,Adams me Iman tace maka ne?Adams yace wai
cewa tayi ina boye no ina kiranta wai bata so Maska
yayi murmushi to dama kai kake mata ko?Adams yace
bani bane Allah maska yayi tsaki sannan yace kaga
abinda nake gaya maku ko ku nemi manyan babys ynxu
gashi kana yi ma yar cikinka rantsuwa ita kuma sai
masifa take maka ynxu ina girma?babu babba wani
abun ma sai taga gadon kwananka Adams yayi
murmushi yace wannan ra'ayinka ne kawai niko ina son
in auri yarinyar dan na more sadakina da kyau Maska
yace in ka samu big girl shine zaka more sadaki Adams
yace mu bar zancen haka Maska yace kai dai ka sani
yaushe zan bar yar yarinya ta juyani? ai ni in babbar ce
ma sai ta raina kanta in tace zata kawo min iskanci
Adams yace in baka sonta ba ba in kana sonta komai
zatayi maka zaka jure sai kaga karamar ta juya ka
babbar bata juya ka ba,tsaki Maska yayi sannan yace
baka gama sani na ba har ynxu don ina son mace tayi
kadan na jure iskanci, sannan ya mike ya tafi Adams na
mishi dariya.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Muna zaune a dakinmu muna aikin gyaran katunan
bikin su Mami yau saura kwana takwas bikin kuma
yaune su yayanmu zasu iso shine babban abokin ango
kuma babban yayan Amare,na dubi Mami nace ya kan
Badarawa,Malali,da Unguwar sarki ya kamata muje dan
yan skull zamu gayyace sosai mun dade bamu hadu ba
mami tace haka ne yi sauri mu biyama Amira,tare
muka shiga gari sai magriba muka dawo sai dai in
lokcin sallah yayi mana mu tsaya muyi,shirye shirye
sunki karewa saboda wasu abubuwan bada su Sa'a
zamu hada ba walima ce kawai tare sai Sisters day da
su Anty Mariya suka shirya a gidan yaynmu in sun iso a
Yakubu Avenue amma mu zamuyi lunchn sannan
angwaye sun shirya dinner,mun dawo mun sami yaynmu
ya iso saboda gidansu sai an gyara da yan share share
gurin su Sagir na sami lbr isowarsu sai ga kuma wayar
Adams yana ce min sun iso ynxu suna tare da ango
nace to sannu da zuwa me zan shirya maka?yace
komai ma nace to an gama nadai daure ne nayi
wannan maganar dan kar ya ce ban yi murna da
zuwansa ba amma zahiri hankalina yana kan yayanmu
da kuma masifar son ganinshi,nan na dan yi girke girke
na san Adams na zaci zan sameshi tare da yaynmu a
dakin yaya kabir din ina sai shi kadai na samu dan haka
shi kadai yayi ta surutanshi Adams ya dubeni kin kara
cika fa yar gidana ina son Maska ya ganki shi da yake
cewa zan auri yar cikina nace um!
Chapter 11 · 0% Book details