← Book details Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 15

Sashe 13

Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Amira
tace don Allah ku gama kwashe su mana sauran
abokan suka ce to,yaynmu ya kuma fitowa gurin
motarshi ya nufa Adams ya bishi ya bude mota suna
magana da Adams ko me suke cewa oho?sai Adams ya
dawo shi kuma ya shiga cikin motar sai kuma ya fito
ya dubi gurinmu da hannu ya yafito ni gabana ya fadi
nace Amira yayanmu yana kirana mami tace karki dade
fa banko iya magana ba na nufi gurin motar sai na
samu kaina da canza salon tfy cikin isa da kasaita na
iso gurin motar gefen kusa da dryva ya bude dan haka
sai na zagaya nayi magana sai naji yace shigo ba musu
na shiga kamshi da sanyi sukaimin sallama cikin isa da
jan aji ya tashi motar ba tare da ya dubeni ba cikin
gwaninta ya fusgo motar da gudu sai da muka hau titin
Bako Road sannan ya kara sautin wakar p square cikin
wakar su ta no one lyk u,na jingina da kujera ina
sauraro wakar na zata gurin lunchn zamu je sai fa naga
mun dau wata hanyar ban ankara ba sai gamu gaban
gidan yaynmu dake Yakubu Avenue gabana ya fadi
sannan tsoro ya bayyana a fuskata yaynmu ya dube ni
sai ya fito da waya yana yan danne danne shi ban sani
ba ashe hotona yake dauka ban sani ba,na rufe wayar
sannan yace bisimillah mu shiga nace me zan yi
yaynmu?kasan fa gurin Lunchn zamuje,yace nima
bazaniba dan haka kema ki hakura da sauri na dubeshi
cikin damuwa nace mami ba zata ji dadi ba fa yanda
muke da mami ban kyauta mata ba,dubana kawai yake
sannan yace to mimi taje mana ni dake dan haka ynxu
ma ni yunwa nake ji mu shiga ki min abinci na dubi
fuskar shi ba alamun wasa amma duk da haka sai da
nace bai dace matar gidan ba ta nan ba na shigar mata
gida ya daka min tsawa gami da cewa tsaran ki ne ni
kike yi min musu?bayan mun shiga ya tsaya da motar
na fito shine a gaba ina binshi a baya har falo ya zauna
nace inane kicin din bi nan ya nuna hanyar,na tafi
komai na kicin da ake bukata akwaishi dan haka na
shiga aiki gasky na raina tsaftar matar gidan banyi
karambanin gyra mata kicin ba nidai nayi iya aikina
farar taliya da miyar kwai da hanta nayi mishi a
gabanshi na jera komai na koma na zauna ya dubeni zo
mu ci kai kawai na girgiza dai dai lokacin da naji ringing
a cikin jakata na ciro wayar har ta katse na duba 11
miss call na duba su Mami ne da Adams na dubi
yaynmu dake faman cin abinci nace su mami na jirana
ya dubeni kin san bana son nacin magana ko?ya
kamata ki rike wannan ya cigaba da cin abincin shi sai
da yayi dam sannan ya shige dakinshi wanda an rubuta
master bed room a jikin saman kofar dakin da yellow
din kala kamar minti biyar ya fito zo muje
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
A ranar haka muka yi ta yawo a gari dan mugunta har
magariba kuka ne kawai banyi ba dan haushi wai ace
biki kamar na mami bana guri ai da takaici gashi ya
amshe wayata ya kashe na rasa irin wannan ikon,
gidan shi muka koma ya tafi masallaci ya barni wai
nayi sallah cikin dardar na zauna sai bayan ishai ya
dawo ko sallar ma banyi ba ya kuma daukata ya shiga
gari sai tara ya maidani gida lokacin an tashi daga
lunchn din dan haka dakinmu na wuce na fada gado ko
da mami ta shigo da fushi ganin ina kuka sai ta sakko
tana tambayata menene?cikin kuka nakece mata
yayanmu ne ya daukeni sai yawo yake dani ya hanani
zuwa gurin lunchn dinki tace ba komai kila shima yana
da dalili nace wanne dalili?shidai burinshi ya ga raina a
bace nan dai ta shiga lallashina.
Chapter 13 · 0% Book details