← Book details Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 15

Sashe 14

Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari aka daura
wasu mami aure, da daddare aka kai mami gidan Nasir
dake unguwar sarki tun fara bikin sai yaune muka sake
nida Adams dan yayanmu ya kasa ya tsare yaki barina
na cashe ashe shi yana can suna yinta da anty mimi
yace ba zata zo ba ita kuma tace sai ta zo ya gama
shirinshi tsaf ta taso har gun mota ta biyo shi tana
cewa sai taje,ta shige mota itama tata kama murfin
motar yace sake min tace sai fa naje yace ke kina fa
cin darajar cikin jikinki ne bayan haka dakin san ina
fada kina fada ba zata yiwu ba amma zaki haihu ba zan
dau wannan iskancin ba wata macen arziki ce zata bar
gidan aurenta karfe goma kuma bata san sanda za'a
tashi ba to tunda lallashi baya miki zan biki da zafi yaja
murfin motar ya rufe sannan yaja motar,muna tsaka da
fira sai ganinshi mukayi tsakiya suka sani shida
Adams,Adams ya dubeni mun zata ba zaka zo dinner
kanwa ba?yace kasan mai iyali saida na lallameta tayi
barci Adams yana yayi kyau muma dai Allah ya kaimu
ga jarawa ,ni kam kumallon ya motsa don haka duk
haushi suka bani Adams ya dubeni yar gidana kina
gaya min kince zakuyi lunchn da mene?nace sai mun
zauna dasu Amira menene na sauri Adams da sauran
lokaci fa,yace ba wani lokaci gara ki fada min don in na
tafi sai ana sauran kwana daya biki zanzo in nasan
komi tun yanzu zaizo da sauki,na dubi yaynmu wanda
yake ta aikin danne dannan waya tamkar baya jin mu
nan ko yana sauraren komai nace to kafin ka tafi
zamuyi zancen, gobe fa zan tafi cikin kosawa da
maganar nace to baga waya ba Adams yace to shi
kenan ya canja zancen da hajiyata tana son jin
muryarki bari na kirata ku gaisa,nace haba dai daren
nan?ka bari sai da safe yace to na bari kinsan ni ba dai
cikin gimbiya ba nayi dariya nace to Allah yasa ka dore
ba sai naje gidan ba a canza min yace haba aini din
nan ko bawa kika samu kinsan yanda nake son ki
kuwa?kin san nutson da nayi a kogin kaunarki?in da
ace kinsan yanda jiki da jijiya da bargo da kashi da
tsoka........kai yaynmu ya daka tsawa ya cigaba haba
Adams ka tasa yarinya karama kana wannan
kauyancin?ai wannan soyayyar dace in kana sonta
idonka kadai ya isa sheda ba sai kanata wannan batun
ba ka gane wannan ai yar da girma ne da ga ni har
adams kallonshi muka tsaya yi sai da ya gama sannan
yace Maska kai komai naka daban ne kana da hali irin
na masu girman kai...yaynmu ya daga mishi hannu ya
isa yi tayi,Sai karfe sha biyu muka tashi daga dinner
washe gari muna sallama da Adams yace sam bikin
nan bai min dadi ba,dan naso muyi hotuna muyi hira
mai isarmu amma haka bai samu ba nace kar ka damu
tun daga waya maganar hoto sai na shiga na miko
maka munyi sallama nabashi hotuna ya diba son ranshi
mun rabu akan sai naji shi a waya haka muka
rabu,bayan gama bikin mami yaynmu bai kuma damuna
ba sam gaisuwa ke hada mu sai dai da naje gidan
babana ne yake cewa yayanmu yana zuwa yana
gaisheshi har yazo da mai dakinshi ya yabeni tare da
fadin kirkinshi,ranar ma muna zaune a falon babana
dani da Anty Maijidda sai ga yaynmu sun gaisa da anty
maijidda sannan na gaisheshi anty tace kije ki kira
babanki na tashi na dauki dan kwalina naje na sanar
dashi,yana fitowa naga ya soma fara'a ganin yaynmu
suka gaisa sannan yace yazo ne ya mishi sallama dan
gobe zasu koma sai kuma nan da wata hudu lokacin
bakina da abokinshi babana yayi mishi godiya gami da
sa albarka sañnan yace ga kanwar ka nan dama ta
dameni wai nayi sallar magariba na kaita gida don haka
sai ta tashi ku wuce,na ce sai gobe zani,babana yace
a'a ni kinga gobe kwatano ma zamu,na soma shagwaba
nayi takwa takwa da fuska nace nidai to ai baka sai
min abinda kace ba yace me nace zan sai maki?
computer yaynmu ya harareni na kauda kai babana
yace to in na dawo ranar sati monday sai na sai maki
shi kenan?nace eh yace to uwata maza tashi yaynki na
jiranki na mike ina fadin ko kana korata ne?ba zan sake
zuwa ba suka sa dariya shida anty Maijidda yace wane
ni na kore ki ban isa ba nayi kadan anty tace naje daki
na dauki kayana na dauka tace na gaida mamana,tunda
muka dau hanya ni da yayanmu ba wanda yayi magana
can yace gobe zamu koma sai kuma bikinki na dubeshi
to Allah ya tsare hanya na fada cikin karfin hali,tunda
muka zo gida muka samu haj yaya a harabar gidan na
soma tsuma,cikin tsoro nace gasu haj,to menene yace
yana fakin na fito da ido suka bini shi kuma ya nufi
gurin su ni kam gida na wuce,yace haj daga ina?ta
daure tace nan makwafta muka shiga barka ta cigaba
matarka tana jiranka ashe kai kuma kana nan kana
yawon banza daga ina kake?daga tudun wada,gurin
wa?gurin baban iman ta kuma dubanshi muje ciki gani
nan tana mamakin halinshi shi mutum ne wanda baya
shakka ko karya komai zai fada in dai gsky ne zai fada
sai dai a mutu
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Haj yaya fada take tana karawa tace eh dan shashanci
matrka ta na nan tana jiranka kai kuma ka tafi gidan
kanin ubanka yace to haj dan naje munyi sallama shine
damuwa?to kiyi hakuri ta dan sassauto kai baka da
tunani yanzu in kai wanine yaushe zaka bar Adamu
abokinka ya nemi yarinyar nan ga kannenka?yace
wadanne kannen kuma bayan sunyi aure?ko ba ma
haka ba ai matar mutum kabarinsa....tace nasan haka
amma ni na sha alwashin sai na hana auran Iman da
Adamu in dai ina numfashi yanda bana son ta rabeni
kaima bana son ta rabi na kusa da kai kaf yayana
wacce ce ta samu mai kudi dan mai kudi kamar
Adamu?babu dan haka itama ba zata aureshi ba,sororo
yayi yan dubanta sai da ta gama sannan yace to haj ke
me zakiyi akai?dan Allah ki bar maganr nan,tace nasan
abinda zanyi kai dai tashi ku tafi Allah ya tsare hanya
kana can zakaji lbr,yaso yayi mata nasiha gami da
shawara amma sai taki ta hau shi da fada,dan haka sai
yace to haj zan wuce ba zan samu dawowa da safe ba
saboda sammako zamuyi ta kano zamu tashi sakon ki
gobe in Kabir ya kaimu kano ya dawo zaije banki ya
amso maki kudin,ta ce zaka kara min dubu talatin akan
na da yace ba komai zai kawo maki ina Mimin mu
wuce,haj tace tana gidansu, ya dubi haj wa yace taje
jiya fa can ta yini haj tace ai ba'a gajiya da gida ka dai
biya ka dauketa yace Allah ba zan biya ba tunda ban
aiketa ba in ta dawo shi kenan in bata dawo ba ta
zauna,Haj ta dubshi gara da ka nuna na gani dama ta
kawo min kara kana wulakantata son ranka yace haj ni
kinsan abinda take min ne? bata san kula da miji ba
bata san darajar miji ba bare yanda zatayi biyayya son
jiki bata iya girki ba,ni nasan ina da mata amma sai na
fita yawon gidajen cin abinci,tace to ai komai dan
lallashine yace wane lallashi ne ban mata ba amma
nasan maganinta zata gane bata da wayo,ya mike mun
tafi haj tace Allah ya tsare kar dai ka yarda naji wata
magana.
Chapter 14 · 0% Book details