← Book details Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 15

Sashe 10

Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Kwanaki suna shudewa,Lokaci na kara wucewa mun
gama Diploma a Comp, sannan munyi jarabawa sai dai
jiran abin da zai biyo baya Adams yana kirana a waya
duk da bani sonshi a raina ina dan sauraranshi yaynmu
kam bai taba kirana ba sonshi dai yana nan makale a
raina ,Alhj da Babana sunyi bincike akan Adams ashe
ma mahaifin shi abokin Alhaji Adamu garko ne me
gidan Babana dan haka basu sha wata wahala ba wurin
bincike sun shirya magana tasu ta manya sannan sunce
sai sunji ta bakin Adams sun kira shi sun mishi bayani
yayi murna sannan sun bukaci ya fadi daidai lokacin da
yake son a sa bikin yace su bashi kwana biyu zai sanar
dasu, a son Alhj ayi bikinmu rana daya dasu Mami da
Sa'a da Bilki,to amma da kyar hakan zata samu.

Yau laraba zaune nake gonar kawu kabiru kanin mama
a kauye gefena Jimmala ce kanwar yaya Ibrahim tunda
naje kauye kullum sai naje gona kota dangin mama ko
ta dangin babana,daga inda nake ina hangen kawuna
yana bawa masara ruwa wayata ta soma ringn Adams
ne na sani dan haka sai na dauka gami da sallama yar
gidana na jima ina nemanki ban same ki ba?nace
matsalar ntwk ne yace to ya gari?nace gari na
hannunku mutanen England yayi dariya,to yaya?na me?
na zancen mu mana kinsan yau ne na yanke musu zan
sanar dasu date din daya kamata a sa fa,na dan
yatsina baki nace kai yaushe kake so,nafi so asa watan
goma kin ga yanzu muna watan hudu nan da wata
shida kenan ko?nace to hakan ma yayi daidai, su Mami
zasu rigamu dan su saura wata biyu yace insha Allah
dani za'ayi bikinsu Mami,Amira fa?nace ita sai tayi
HND tukunna yace Ok! to duk yanda sukayi zan kiraki
nace kai yaushe zaka zo yace sai bikin su mami zamu
zo tare da yaynku ne,gabana ya fadi sam bana son
tuna shi dan yaynmu shi kadai nake so so mai tsanani
rabona da ganin shi tun bankwanan nan da mukayi
yace kina jina?nace ina jinka Adams wai dan Allah kuna
shiri da yaynmu?yace sosai ma dashine muka sa date
din bikinmu gabana ya fadi nace haba yace Allah gaske
ne fa nace suna lfy yace kalau shine ma ya tsaida date
don nace nan da four month yace gara six din,nace
Allah ya kaimu yace amin...

Adams kan abin motsa jiki yaynmu ne ya hada zufa
tamkar mai tukin mota yanata faman yi can ya dubi
agogon dake manne jikin bangon dakin karfe takwas na
safe ya jawo tawul ya soma share gumin da ke zubo
mishi sannan yasa baki ya kira Mimi,Mimi ta shigo da
sauri gani ya dubeta ina shayin wai yaushe ne zaki koyi
yanda ake kula da miji ne?kin san kawo shayin nan
aikin ki ne daidai wannan lokacin amma kullum sai
nace ki kawo?to za kije ki kawo din koko?kin tsaya min
akai,ta juya shi kuma ya ja tsaki sannan ya sauka daga
kan abin motsa jikin ya hau kan wata kujera a gefe ya
zauna yaci gaba da share zufar,ta shigo rike da kofin
tangaran babba da karami,ta ja wani dan tebur ta tura
mishi ta juya ba tare da magana ba ya bita da kallo
sannan ya girgiza kai sam Mimi bata dace dashi ba ta
kowanne fanni sannan yana son a inganta mishi ciki
dan kowa ya san yan kwallo da cin abinci,ya kurbi
ruwan na lipton mai hade da wasu ganyayyaki can sam
sai yaji komai ya ishe shi ya kwana biyu kenan baya
cin wani abin kirki tunda Adams yazo mishi da zancen
sa ranar shi da Iman ya kuma nemi shawarar sa ya
bashi shawara ya bari sai nan da watan goma ne dan
yana son ya nemi mafita sam ba zai bari adams ya auri
yarinyar da yake masifar so ba,so mai tsanani sannan
yasan tana sonshi taurin kaine yasa taki fadi to shima
yayi alkawarin sai ya aureta muddin yana numfashi a
doron kasa,yayi lissafi Mimi tana da ciki wata biyu zata
haihu watan sha daya yana son sai mimi ta haihu
sannan ayi bikin nashi ,amma ba zai yiwu ba,ya danyi
shiru na wani dan lokaci sannan yace na san abinyi ya
mike tsaye ya fita bayi ya shiga a cikin dakin shi ya
hada ruwa yayi wanka a gagauce ya shirya cikin JC
blue da ratsin fari ya daura takalmi mimi ta shigo kana
da bako,ya dubeta wanene?ta dan tsina baki ko Adams
yake ne oho?haushi ya kama shi me yasa yarinyar nan
batada kunya ne yanxu?amma zaiyi maganainta yace
fita anan banza kawai ni zaki cewa baki san Adams ba?
ta fita tana yin kuna kunai na gaji da wulakancinka
komai kace sai an maka ni ko gsky ko a gidanmu ban
kauda tsinke bare wani girki ina dan wanda zan iya kai
kuma kana ganin kasa wata yana jiyota sai dai bai san
me take fada ba yace zaki gane kuskurenki.Ya sami
Adams zaune shima da shiga irin ta Maska Adams ya
dubeahi kace ka shirya Maska ya zauna sai dai ban
karya ba,haba baka karya ba kai da kake da iyali
ma,Maska yace kasan bata da lfy gata dama da son jiki
sam bata son aiki Adams yace sai hakuri nidai Allah
yasa nayi dace in har ka dace ka sameta din to Adams
kar kayi shakka zaka sami yanda kake so,Adams ya ce
ya kake cewa in har na sameta?kana ma shakka
kenan?kar ka manta fa har na biya sadaki an sa mana
rana kuma kaine ma ka tsaida min har na sanar da
manya,Maska yayi wani murmushi Adams ya kalleshi
Maska bana son wannan murmushin naka fa tuni na sa
mashi suna murmushin mugunta dan ko a fili muke
gurin wasa abokan wasa suka sako mu a gaba kana
irin wannan murmushin sai kaga Allah ya bamu
nasara,Maska yace tashi mu tafi a can zan yi break
kafin mu shiga fili.

Ni kam lokacin ina kauye ranar
kwana na sha takwas daga sati daya ina jikin tsohuwa
kakata tana fadin daga ni takwara kar ki karasa ni nace
kai dan Allah ki barni na dan huta mana infa na tafi sai
na dade zan zo tace ai ba zaki kawo min Adamu mu
gaisa ba?nace ni ina naga wani Adamu yana can
kasashen turawa yana kwallo tace ai Ball yake?ynxu
dan Ball din zai rike ki?nace to ai tasu ta gaske ne ba
irin ta nan ba,ta tureni ke ja can da ban haushi baga su
nan muma muna dasu ba yan bal din yanxu jibi yaron
nan na gurin karima shima aikinshi kenan bal asubar
fari yasa gajeran wando da wani kwandallelen takalmi
raf raf ya tafi bal kusan shekara biyar ance har yau baa
taba nuno shi a cikin talabijin ba shi bai tsaya yayi
noma ba shi kuma bai tafi rani ba,sai dai yau yana
waccan unguwa gobe yana waccan yawon bal,tunda ta
soma magana nake dariya,tace dariya ma na baki?
dama wannan shirmen Adamun keyi shine za'a bashi
mata?ko mu da muke karkara dan gidan karima an
hanashi mata,na kuma tuntsurewa da dariya ta dau
mafici ta bini kki bani guri ta kai min duka da gudu na
fita ina kwasa dariya sai naji tsayuwar mota da sauri na
leka motar babana na gani da gudu na fita na
taroshi,Ya kira wasu yan samari suka shigo da kayan
abinci na rike mishi hannu muka shigo, dakin Baba ya
soma shiga kafin ya shiga dakin Tsohuwa na nufi
madafi na dauko masa abinci a kwano na debo masa
ruwa a randa na aje a gabanshi ina fadin Babana kamar
nasan zaka zo na yi abinci da yawa,yace to na
gode,nace yasu Mama?yace suna lfy sune ma suka
matsa min akan na daukoki daga sati har kin kusa wata
jiya Alhj ya kirani a waya yace in mashi kwatance yaje
ya daukeki,nadan yatsina fuska nace ni ban son tfy
tsohuwa tace to ai ya zama dole nace muna gama
bikin su Mami zan taho nan,baba yace a'a muma muna
son ki zo mana kafin bikinki daga nan nayi shiru ban
sake magana ba,tsohuwa tayi caaraf tace yawwa ashe
kai yanzu Adamun dan bal ne?shi ne zaku bashi yar?

Babana yayi dariya sannan yace ai sana'a ce sosai
suna samun kudi fa shima dan mai gidan Habiba
kwallon yake tare ma suke, ai shi kenan amma ko ga
tarihi bal ance bata da kyau,yace to ai wasu malaman
sunce za'a iya yi in ta zama lalura saboda kishin kasa
tace tunda kuna so ai komi ma cewa zakuyi ni dai ina
jin su har suka gama.
Chapter 10 · 0% Book details