← Book details Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 15

Sashe 3

Tawa Ta Sameni Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?
_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347
Yau asabar tara ga watan sha daya aka daura auran
yayanmu da anty mimi a kofar gidansu dake Malali daurin
auran ya sami halartar mutane da dama cikinsu harda
matasa sun mafi yawa kasancewar shi fan kwallone
sunyi walima bayan daurin aure kamar da gayya nice
mutum ta farko da ya fara kira yace min an daura auran
a raina nace to ni ina ruwana amma a fili sai nace Allah
ya sa alheri,yace me kikeyi?nace ba komai ina kwance
yace kin san yau akwai dinner don haka ya kamata ki
zama cikin shiri nace ina jin fa ba zan samu zuwa ba
don kaina yana min ciwo bayan haka ga rigima nata
faruwa kasan ma jiya banda Alhj ya sa baki da rigimar
nan bata kasu ba don haka ina jin ba zan samu zuwa
ba,yayi shiru yana son yayi sallama amma bai gaji da jin
muryarta ba ya kan so tana magana yana kusa shidai
baya gajiya da kallonta shi dai ya san yana sonta kuma
yasha alwashin in dai yana raye sai ya aureta duk da
karancin shekarunta,nace hello danaji shirun yayi yawa
yace Iman kin sha maganin ciwon kan?nace eh a takaice
yace kin gane ina son gsky kije wurin dinner din nan in
kinji kan naki yayi sauki amma ba dalilin wani shirmen
fada ba can kin jini?nace in Mama ta hana fa?yace ba
xata hana ba zan mata waya nace to sai anjima
Amira dake gefena ta dubeni tace ke da wanene haka a
waya,nace yayanmu ne
Amira ta zuba min ido cikin tuhuma tana cewa anya
wannan yayan naku bashi ne gayan nan da kike boye
mana ba?na dubi Amira cikin rashin gsky nace haba dai
Amira ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi tace Iman
bai kamata kina boye mana sirrinki ba musamman irin
wannan kina bukatar mai baki shawara sannan mu sai
mu dinga kwashe sirrinmu muna fadi maki duk zurfin
cikin fulani bana boye maki sirrina amma ke sai kiyi ta
nuku nuku,nayi shuru tabbas zancen Amira gsky ne sai
dai ina jin nauyin ce mata ina son yayanmu ne dama dai
muna yin soyayya ne shi ne amma fa nice nake haukana
bai ma san inayi ba,ta yunkura zata dauki hijabi tace
daina tunani Iman ban fa ce lallai sai gayan matsalar ki
ba ni kin gama tfy ta da sauri na jawo ta muka kara
fadawa kan gado,sorry Amira zakiji ta zauna kusa dani
sannan tace kin cika abin haushi ne Iman,na nutsu
sannan na soma bata lbr sanda na soma son yayanmu
nace wllh Amira da ban yarda wai ina sonshi bane na
dauki tsoron da na keyi ne yasa na kanji muguwar
faduwar gaba a duk lokacin da na ganshi sannan jikina
ya shiga kyarma ashe wai duk so ne hawaye ya soma
zubo min Amira nayi adduar nayi addua tamkar ina kara
zuga son nayi kukan na tsine ma SO,so ko wahala nasa
Allah ya isa ga duk wanda yace so na da dadi don nidai
cikin wahala nake da kunan rai na soma kuka mai sauti
nace Amira ni so bai min adalci ba sona da ya tashi ya
kaini inda Allah bai kaini ba zuciyata ta kamu da son
wanda yafi karfina na tsaya ina jan ajiyar zuciya Amira
batayi min magana ba ta barni nayi kukana mai isata ba
ta hanani ba bata fara magana ba sai da nayi ya isheni
sannan nayi shiru ta soma magana ki bar kuka kuma kib
bar zargin zuciyarki da ganin laifin tsuntsun sonki sannan
ki daina cewa ya kaiki inda Allah bai kaiki ba gaya min
dalilin da kike ganin cewa yayanmu yafi karfinki,nace na
farko ba sona yake ba nayi ajiyar zuciya sannan na
cigaba ni ba ajinshi bace sannan ga rashin shirin da ke
tsakanin uwata da tashi ba zasu yarda mu auri juna ba
koda yana sona bare ma bai taba son ba Amira tace niko
ina ganin kamar yana sonki abinda yake maki yafi karfin
kyautatawa sai dai SO,nace banyi tsamanin ba shi da
yake fadin ba zai auri karamar yarinya ba a gabana
yasha fadin wannan zancan ke ko abokanshi sunsha
cewa suna sona sai ya hau su da fada gami da cewa shi
baya son raini basu san in suna cewa suna sonmu ba
zamu raina su ba?na dubi Amira na cigaba da cewa kina
ganin asir abokinshi da yake son mami in da yabi ta
yaynmu da bai nemi mami ba a gabana wata rana na kai
musu abinci naji yana ce ma Nasir mai zaiyi da mami yar
cikinashi dan dai rashin sawa kai girma gun kananan
yara,ga manyan babys a gari zai ce sai Mami wadda a
haihuwar kaji ya haifeta sannan kice zai soni?bayan
mami tama girme man da kusan shekara daya,Amira
tace to adduar dai zamu cigaba dayi sannan zamuga
shawarar da zamu baki ni da Mami sai in mun zauna
nace kar mu gayawa Mami,Amira tace dole ne Mami taji
zancan nan don bamu boye ma juna sirri kin sani sarai
dama ke ce mai mana nuku nuku kuma mun sani mun
dai kyaleki ne nace ni dama don ga cewar yayanta ne shi
yasa Amira tayi tsaki sannan tace dole ne Amira ta sani
nace aishi kenan, mukayi shiru na dan lokaci sannan
nace ynxu ma shi yayi man waya wai na shirya muje
dinner anjima nifa da bana son zuwa Amira tace me
yasa ba zaki je ba?nace ban son abinda ran mama zai ta
baci a banza amma shi cewa yayi fadan da akeyi ba
dalili bane da zai hanani zuwa,Amira tace su mami ma
da kyar in zasu don naji suna cewa yaynku yace kar ya
gansu a gun,nace to nima kan ba zanje ba Amira tace
wllh sai kinje ai ta haka ne zaki samu ki cusa kanki
gareshi kin gane shiga zakiyi ta alfarma ko ba haka ba
shi fa da kanshi yace kije nace cewa yayi ma zai sa azo
har gida a daukeni don ban ma san gun da za'ayi dinner
din ba Amira ta mike tana dariya gami da cewa kune
manya a gun.
Chapter 3 · 0% Book details