← Book details Tabbataccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 14

Sashe 6

Tabbataccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina zaune a lalon Amina misalin karfe uku saura kwata
sai lokacin na samu yin wanka na zauna ina goge jikina da
ruwan man 10.0.6 sai da gama sannan na dauko lotion din
10.0.6 din na shafe jikina dashi, kusan minti talatin na yi ina
eyara jikina bayan na gama gyaran kaina AMina ta shigo ta
ganni na tasa kayan a gabana ina kallonsu dai dai yayin da
nake Rokarin rike gashina da wani talkcken ribon ta kalleni da
gefen ido cikin lara'a ta cemun ai gara ki saka mishi kayanshi
ya gani tunda ki ce zai z0 yanzu na sanya hannu na dauki
Ieshin mai ruwan malmalo da kore-kore a jikinshi dinkin half
bubucc na sanya bayan na sanya underwcar na gyara daurin
dan kwalina na dauko sarkata sabuwa na saka habawa na tsaya
ina kallon mudubi ina kara kwantar da gashin girana na dauko
turare ina Kara feshe jikina dashi Amina ta ce ai yaron nan yana
burgeki, nayi murmushi na ce mata na yi kyau ko?

Ta tayani
murmushi ta ce ai lada ma batawa nc, shi yasa nake so idan
Malam ya shigo in bashi shawara tunda ya cc zai
iyaycnshi su o to in suka yo din ayi muku baiko kawai kin ga
sai a sallami sauran jama'a, don hankalinshi ya kwanta.

Na yi sauri na bata fuska na ce mata a'a Amina kar ki yi
haka ni na gaya miki ina son Manniru amma ba zan iya
aurcnshi ba don ni gaskiya ba zan auri mutumin da na fishi
tsawo ba, nan da nan haushi ya turnikcta ta rufcni da fada tana
cewa a'a da sake, wannan zancen banza kike yi kina sonshi
amma ba za ki iya aurenshi ba to gaya mun meye amfanin son
da kike yi mishi?

Son inna kenan ta soka ta shanye ka kina son
shi don yana kashe miki dukiyarshi shi yasa kike yi mishi
dadin baki amma in na ce a isayar muku da magana ke dashi
sai ki ce wai ba za ki auri wanda kika fi shi 1sayi ba, to
tsawonshi za ki aura?

Ko kuwa yawo dashi za ki rinka yi kina
nunawa jama'a shi?

Na ce a'a, ka ji Amina ba zaka nunawa
jama'a shi ba miji kuwa ai abin adone ta ce mara kunya to zo ki
gaya mun wani yaro sabo ya shigo da sauri yana cewa Anti
Nali ga Manniru ya zo ko in je in ce mishi kina zuwa, na ce
barshi kawai gani nan fitowa, ya ce don Allah anti Nafisa bar
ni in je in gaya mishi kafin ki fito kin san kullum ya zo layin
nan in dai n aje na gaisheshi dari biyu yake bani, to balle kuma
yau sallah.

Amina ta yi murmushi ta ce ke kuwa barshi ya je mana
na ce jeka Sabo bayan fitarshi sai ta ci gaba mutumin dake
shirya miki irin wannan hidima in banda shirmenki ina ruwanki
da tsayinshi iye, na ce gaskiya a'a ni a barni kawai ta ce to
kuwa zan gayawa mallam ya gayawa mishi gaskiya don
wahalar ta yi yawa, na fita abina ina taku daidai ga takalmina
mai tsinin diddige a kafata ya yi matukar daccwa da kayan
jikina.

A kofar gida na wuce Yaya Habibu shi da Alhaji
Mainasara suna zaune suna hirarsu na nufi inda Manniru ya yi
fakin din motarshi kusa da shagon Danliti yana hangoni ya fito
daga cikin motar ya jingina jikinta yana murmushi ina isa
wurin ya ce barka da sallah 'yan mata ian fata kin yi sallah
lafiya, na mayar mishi da murmushinshi na ce lafiya kalau,
yallabai yaya su Hajiya?

Ya yi murmushin jin dadi ya ce tana
gaisheki na ce ina amsawa na dan kashe mishi ido ina
murmushi na ce yallabai bai yaba kwalliyata ba ko kayan basu
karbeni bane, ya kyalkyale da dariya har yana gyara 1sayuwa
ya ce Nafisa kenan ai don kar ki ce na cika zumudi ne yasa ban
yi magana ba kin san wani abu?

Na ce sai ka fada ya ce ina
1abbatar miki da cewar duk wani abinda kika sanya shi a jikinki
sai ya zamo tamkar don ke aka yi shi wannan yana daga cikin
baiwar da aka yi miki an yi miki wani irin structure na jiki da
sai ki tara mata dari baki samu irinki ba, na yi 'yar dariya na ce
mishi gaskiya kyaleni haka kar ka zugani da yawa kasa in
yarda haka din nake bayan ko yau da safen nan sai da Amina ta
karewa munina zagi, ya kyalkyale da dariya ya ce ta yi ne don
ta 6ata miki rai kawai tunda kin bata haushi.

Mun dan jima muna hirarmu mai dadi sai ya ce jiya baba
ya dawo daga Jidda na ce mishi kai madalla ya ya jikin nashi
ya cc a'a da sauki na ce to madalla, gobe da safe in Allah ya
kaimu zan zo in dubashi ya ce kin ga kuwa da kin burgeni
dana ga ya bude kofar mota zai shiga nuna alamar zai atfi sai
na dan kara rapge muryata kasa ta kara sanyi na ce naga aike
yallabai Allah ya kara budi ya kuma saka da alhcri, ya yi
murmushi ya ce amin Nafisa don Allah ki rinka tayani addu'a
Allah ya bani ke mana, na yi murmushi na ce iun kana s0 ai sai
in yi maka ya miko mun envelop din da ya ciro daga aljihun
motar yana cewa ga wannan barka da sallah ne na dan yi dim
kamar ba zan karba ba, ya ce karbi mana nasa hannu biyu na
karba na ce na gode, Allah ya saka da alheri ya tafi nima na
Juya zan shiga gida.

Yaya labibu yana zaunc shi kadai ya dan sha mur kadan
na zo zan wuce shi sai ya ce in kin shiga gida nan da minti
goma sha biyar ki zo ki sameni a dakina, na ce mishi to, a
dakin Amina na bude envelop din Manniru katine na barka da
sallah sai naira dari biyar biyar guda ashirin dubu goma cifina
juya kudin ahannuna Amina ta shigo tana ganinsu ta shiga
vagina 1ana cewa ni da kike gani na Allah bai sanya mun
kwadayi cikin zuciyata ba, ban ga dalilin da zai sa ki ce baki
son mutum amma kina zuwa kina karbo kayanshi ba tunda kina
son kayanshi to kuwa babu makawa za a bashi ke ai dama kuda
wajen kwadayi yake mutuwa, ladan da yake yi mun shi ya 1una
mun da kiran da Yaya abibu don ina son fita in bar mata
dakin na dauki tsintsiyar zabori na nufi waje ina ce mata zan je
in sharewa Yaya Habibu dakinshi.

A falonshi na sama yana zaune kan kujeramai zaman
mutum uku ya jingina da jikin kujerar ya mike kafafunshi kan
stool din dake gabanshi yana zukar karan sigarsinshi a hankali,
duk da bani son warin sigari yanda naga sigari ya yi kyau a
hannun Yaya Ilabibu sai na ji zan iya zama ina shakar warin
sigarin don ian rinka kallonshi yana zukar tabarshi, ya kalli
Isintsiyar hannuna yayi murmushi yayin da yake kade tokar
sigarin a cikin ashtray din dake kusa dashi ya ce Nafisa kenan
daga na ce ki zo sai ki zaro tsintsiya ki zo da jin an ce miki ni
ban iya sharc banc?

Kawar da 1sintsiyar gefe daya ki zauna kan
kujera na dan durkusa a kasa, ya ce a'a in kika zauna anan ba
zan iya yi magana dake ba, na zauna kan kujera sai dai a takure
nakc ban sake sosai ba.

Ya yi murmushi ya ce kika zaunar dani ina ta jiranki ashe
ma kin mance dani na bude baki na ce lah ban san kana jirana
ba, ya cc a'a Nafisa ba kc kika ce za ki dawo ki gaisheni ba, na
rike baki na ce af haka ne ka yi hakuri ya ce babu komai dama
yanu na kiraki ne don in lambaycki na gyara zama ina
sauraron lambayar da ai yi mun sai na ji ya ce anya wannan
saurayin naki bai cika rigima ba kuwa?

Na dago kaina na
kalleshi ya sanya sigarinshi a baki yana zuka a hankali cikin
nishadi ban yi maganaba har ya fitar da sigarin daga bakinshi
yana busar da hayakin tabar ta hanci da baki a nishadance ya
ce baki yi magana ba, Nalisa kallon da yake mun ya sanyani
sunkuyar da kaina kasa, ina kallon 'yan yatsuna cikin zuciyata
kuwa a ruda nake ban ganc dalilin wannan tambayar ba, na
daure na cc mishi ai ban gane bane, ya yi murmushi ya ce
saboda Allah Nafisa mutum dan 1sugul dashi in azai kai
santaleliyar mace doguwa kamar ki?

Na yi sha'awar acc dazu
da kuke tsaye akwai kamera kusa dani da na yi muku hoto
kyauta don ki gani ban ce mishi komai ba, sai ya cc hala
saurayin naki bai taba jin wakar da wani mawaki ya yi ba inda
yake cewa ((Dogo sai da doguwa gajera sai gajere)) bari da
akwai kaset din a dakin nan zan duba in baki ki kai mishi na ce
ai shima yana dashi, ya cc au to bai yarda da maganar mawakin
ba kenan ko?

Na yi shiru na ki yin magana sai ya ce anya
Nafisa kina da kirki kuwa yau sallah, rabonki da ki ganni tun
kina 'yar kankanuwa amma gaisuwar kirki ba ki yi mun ba,
balle ki kawo mun ruwan sha, na ce bari inkawo maka na tashi
zan fita ya ce ki zo mun da sakamakonki na jarrabawa, in gani,
na ce to na je na kawo mishi ruwan matsattscn abarba da na yi
na hado mishi tare da sakamakona ya karba yana fara'a ya ce
ba dai wannan dan kankanin mutumin ne ya sha ya rage ba ko?

Na ce a'a wannan yanzu nayi na juya na fita.
Chapter 6 · 0% Book details