← Book details Tabbataccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 14

Sashe 14

Tabbataccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Na fara yi mishi kuka, ganin ina kuka sosai ya sa shi ya
kidime yana cewa dakata dakata Nafisa, Wallahi bani nace
malam ya hanaki fita ba shi da Baba nc suka cc in ba hanaki
fita aka yi ba mutane ba za su daina zuwa kiranki ba, shi ne na
cc to amma in za ki gyaran gashinki kar a hanaki tunda na san
ba kya kitso don Allah ki yi shiru kin ga Amina tana daki zata
ii kukanki ta dauka wani abu ne ya faru daidai loakcin Mansur
ya shigo yana dauke da hoton Yaya lHabibu Window Size, sai
da ya zabo wanda ya fi kyau cikin hotunan da suke lalon ya
dauko ya cewa Yaya Habibu matsa ni ka gani tuntuni kana
shigowa daki kana kallon wani kato kusa da kan matarka ka
kyaleshi kai baka san wannan hoton da kake gani sai ya rinka
yi mata gizo yana tsoratata in baka kasa ba, ya dauke hoton
Mannir ya ajiye mun na Yaya Habibu ko ni dana kalli wurin sai
na ga hakan ya fi dacewa, ya cewa Yaya Habibu to ko kai fa?

Dubi yanda ka zauna a wurin Yaya labibu ya yi murmushi
alamar ya ji dadi ya ce yau Mansur ai lare da kaine muka yiwa
malam maganar a sassautawa Nalisa maganar hanata fita ko?

Mansur ya ce kai ni ba wani shiri nake yi da kai ba da har zan
bayar da shaida a kanka tun jiya kake sa kanwata kuka ko
kanace dadin hakan da kake yi nake ji?

Ya kalleni yana
murmushi ya ce in an kawo miki taswira sia ki yi nazarinta
kalin in zo ni ne zanzo a lara aikin akan idona tunda Habibu
Zai tafi Canada sati mai zuwa kirifko?

Na ce mishi to na share
hawaycna na tashi na dauko wani kwali da na yi rapin dinshi
na je na ajiyc kusa dashi na ce mishi ka kaiwa Ummina kayan
wasantanc a ciki sai 'yar bcby shi kenan, ya yi murmushin jin
dadi ya ce zata yi murna sai ta zO yi miki godiya da kanla, na
ce to Allah ya kawo ta lafiya ya ce amin.

Hutu ya kare mun koma makaranta cikin shirshiyar zana
jarrabawarmu ta karshe satinmu hudu aka lara jarrabawar mu
ta karshe satinmu hudu aka lara jarrabawa inda muka kwana
talatin cif sannan muka gama, mun dawo gida ana saura sati
uku ne bikinmu tuni mali yawancin saye-sayen an gama shi
komai na kayan daki dai iri ne aka yi mana shi Alhaj
Mainasara ne ya yi shi Umma kuwa al'amarinta babu sassauci
kowane lokaci a cikin habaici take da yada magana ga gori wai
sun rula mana asiri sun maida babana mutum sun suturta shi
amma godiyar da zai yi musu ita ce ta neman mallakcsu ta
hanyar aurar da 'yarshi ga Habibu, maganganu da wulakancin
da Umma ke yiwa mahaifinyata kowanc lokaci ya sa na ji
auren Yaya habibu ya fita mun a rai ana suara kwana bakwai
biki Yaya Habibu ya dawo gida da shirin zama har sai an gama
biki ya ci angwancinshi ya koma Abuja don kuwa zai ajiye
amaryane a sabon gidanshi anan ran nan Umma wuni ta yi tana
tsare dashi ak daki kome takc gaya mishi oho, bayan fitarshi ne
ta aika a kira mata babana ni kuwa ganin ya shiga wajen ta
yasa naje na labe musu don in ji abinda zata ce mishi na
kirakanc in gaya maka aikin ya yi kyau yasin din da ka yiwa
IHabibu ya kamashi ya ce nan duniya in bai auri Nafisa shi ba
ai yi wani aurcn ba, ila ce autar mata a wajenshi to ka yi
kokari bu katarka kuma zata biya zai auri 'yarka sai dai kar ka
mance ni ce uwar Habibuni na haili abina ban kuma amince da
auren ba, zaman da muka yi da kai ya isa ka gane ni, wanda
duk ya yi mun kan kara to sai na yi mishi na ita ce, don haka
ayi aure kar a lasa muje Zubawa wai mahaukaci ya hau kara,
sadaf sadaf na yi na koma dakinmu na haukan gadona ni da
Hauwa na kwanta ina tunanin abinda aurcna da Yaya Habibu
7ai haifar mana ni da iyayena na rargi kaina kan wulakancin da
ake yi musu da na ji kashedin da suka yi mun tun farko
musamman mahaifiyata da duk wannan abin bai taso ba na
luna kalmar da Innata ke yawan gaya mun (inda kwadayi da
wulakanci) tabbas hakan ne ko da yake ni kam Allah ya sani ba
kwadayin abin duniya da sanyani son Yaya Habibu ba sonshi
kawai nake yi, so kuma na hakika, so irin wanda bai
musayuwa da waninshi, so irin wanda zaka iya sadaukar da
farin cikinka don abin sonka ya samu abinda yake so, duk da
irin wannan so da nake yiwa Yaya Habibu ba zan iya zama in
juri ganin wulakancin da mahaifiyarshi ke yiwa iyaycna ba
tunda ta ce ni ba ajin dan ta bane ina ganin ya kamata in nuna
ni 'yar halal cc in nemarwa iyayena mutuncinsu da nakc ncma
insa a ubar musu saboda son uciya irintawa har zuwa
tsakiyar dare kan runtsa ba ina tunanin menene abin yi?

Sai
wajen gabatowar asuba na yankewa kaina abin yi tashi na yi na
jawo jakata yar karama na soma shirya kayana a cikinta na
sanya sarkokina duka biyu ba don in yi ado ba sai don karin
guzuri bandir din dubu goma da Y aya Habibu ya bani sanda ya
je wajena a makaranta su na dauka na dauko takardar da nake
rubuta bayanan da babana ke yi mun ina rubutawa na yanda za
a ji ajc garinmu na riketa a hannu na rataya jakata a kafada na
yi bankwana da gida ana kiran sallar farko na fito na nufi tasha
zan tafi neman dangin ubana.

Sai mu nemi littafi na biyu don jin shin Nafisa zata gano
Inda dangin ubanta suke?

In har tana gano su me ke faruwa
shin ta rabu da Yaya Habibu kenan?

Taku
Hajiya Hafsat C.

Sodangi
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
3b57cdf4f2364cfebbb1c08f0ea571e9
Chapter 14 · 0% Book details