Sashe 1
Tabbataccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Root Entry
WordDocument
0Table
Data
TABBATACCEN AL'AMARI...
Littafi na
Haj.
Hafsat C.
Sodangi
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
TUKWICI
Littafin nawa tukwici ne ga kanina Bello C.
Sodangi
SADAUKARWA
Na sadaukar da littafin ga iyayena Alhaji Cindo S. da
Hajiya Fatima Sodangi Allah ya saka da alheri, amin.
JINJINA
Na kara jinjinawa kanwata Khadija Chindo Sodangi
HAKKIN MALLAKA
Hakkin Mallakar wannan littafi abin kiyayewa ne ga
marubuciyar littafin Hajiya Hafsat C.
Sodangi Mrs Yunus Abdullahi Dabai.
GODIYA
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki mai kowa
mai komai wanda ya halicci mutum da aljan don su bauta mishi
tsira da aminci su t
bbata ga shugaban manzanni Annabin
Rahama Annabi Muhammadu (SAW) da alayenshi da
sahabanshi da wadanda suka biwa tafarki na gaskiya har ranar
alkiyama.
BABI NA DAYA
Ni Nafisatu Ibrahim yau ne aurena ya cika
shckaru goma cif tunda aka daura shi, yaune
1/8/2002 ranar da maigida ya shiryawa yan uwa
da abokan arziki na nesa da na kusa liyafar cin abincin dare
don su tayamu murnar ganin zagoyowar wannan muhimmjyar
ranar bana mancewar an daura auren ne ranar wata Asabar
1/8/1992 da misalin karfe bakwai na safc.
Al'amuran da suka
taru wurin liyafar sune suka sanyani tunowa da farkon rayuwa
18, mahaifiyata mai suna Aminatu mutuniyar Tashar Fulani ce
wani kauyc dake can kusa da Tudun Wadan 1Dankade dake
cikin jihar Kano, an yi mata auren fari cikin danginta kamar
yadda al'adar fulani take inda ta haifi 'ya'ya uku sai dai cikinsu
babu wanda ya rayu kowanne in ya isa yaye aka yayeshi sai ya
kama rashin lafiya kamar dai laulayin yayen yake yi sai kuma
rashin lafiya ya zamo ajali, rasuwar danta na karshe shi ya fi
tayar mata da hankali in da har mijinta ya bata shawarar ta tafi
wurin uwargoyonta yar mahaiiinta dake aure a wani gari dadin
kowa kusa da bukuru ta yi bakunta, a ganinshi hakan zai sanya
ta an samu kwanciyar hankali.
Wannan bakunta da Amina ta zo wurin goggonta shi ne
ya jawo dalilin rabuwar aurcnta da mijinta don kuwa daga shi
bata sake komawa Tashar l'ulani da zama ba sai dai ta je musu
bakunta, ita goggo Kande anan inda take zaune tana da miji
mai suna Mallam Audu ya'yansu hudu daya ya rasu, uku suna
nan mata biyu namiji guda daya, matan dukansu suna gidan
miji kowacc tana da abokiyar zama da kuma yayansu shima
namijin Yahuza yana nan zaune a cikin gidansu tare da
matarshi Balaraba da diyarsu AIsha mai sunan goggo Kande,
tana da sana'a ta tuyar masa da miyar taushe ko masa da ya ji
ko kuma mai suya lana yin ciniki kwarai don har sari lake,
bayarwa tun asuba akc fara tuya ba a dainawa har yamma,
saboda haka 'yan aiki garcta masu tayata hidima goggo Kande
ita ce matar Malam Abdu ta lalle daga ita kuma bai kara ba
zamansu zama ne mai bada sha'awa, akwai kauna tarc da
girmama juna a cikinshi.
Amina ta yi zamanta wurin goggonta bayan mutuwar
aurcnta cikin dan kan kanin lokaci ta murje ta yi fes da ita sai
sheki fatarta ke yi, baka ce ita doguwa siririya tana da kuduri
mai ban sha'awa, idanuwanta manyane gasu farare sol tana da
'yar siraran hakora masu dauke da 'yar wushirya mai haske,
gata da wadalaccen gashin kai, gidan dake makwabtaka da
nasu goggo Kande gidan wani allajiri ne wanda ake radc-radin
wai duk dadin kowa babu mai arziki kamarshi mutanen
unguwar na kiranshi Alhaji Mainasara amma asalin sunanshi
Muhammade Lawal Alhaji Mainasara mutum ne mai addini
gashi da sanin ya kamata bashi da girman kai irin na wasu
masu arzikin yana mu'ammala tare da 1alakawa mutanen
unguwar suna matukar girmamashi saboda yawan alherinsa a
garesu yana da matanshi na aurc guda biyu Hajiya Hauwa ita
ce uwargida ita ake yiwa lakabi da Hajiya Babba, 'ya'yanta
kuwa suke kiranta Umma tana da yaya guda lara, 1akwas a
cikinsu maza ne babban danta shi ne Abdullahi sai Mustapha
sai llabibu mace guda daya dake dakin ita ce Lubabatu ita
kuwa Hajiya Samariya wacce ake kira Hajiya Kaarama tana da
'ya'ya uku babbar Zainab, sai Zara'u sa'ar Lubabatu sai kuma
dan karamin Muhammadu Nuru, IIajiya Babba ita ce ke rike
da kowa a gidan kasancewar 1ta ce babba sannan macece da ta
iya siyasa sai dai wadanda suka yi mata kyakkyawan sani suna
cewa wai kirkin nata na ganin idon jama'a ne, wasu kuma su ce
fin karfinta mijinta ya yi shi yasa yake hulda da jama'a yake
kuma taimakonsu.
A gidan Alhaji Mainasara akwai ma'aikata masu yawa
tun daga direbobi har zuwa masu baiwa furanni ruwa da masu
gadi cikinsu akwai wani mai suna Mallam Ibrahim aikinshi
baiwa furanni ruwa yana kuma karantar da yaran gidan karatun
Alkur'ani mai girma tare da sauran litlattafan addini, wanda shi
yana aune ne a cikin gidan a can gefe daya.
Gidan Alhaji Mainasara babba ne kwarai ginin bene ne
ta gaban gidan matanshi suna zaune ne a kasa shi kuwa yana
sama ta sashin dama sashin hagu kuwa nan ya'yanshi maza ke
zama idan suka dawo hutun makaranta sai makadeden tsakar
gida anan kicin da dakunan baki suke can gefen karshe inda
Malam Ibrahim ke zaune an ja kaganta da ta shiga tsakani, ka
budc kofa ka shigo cikin gida, hakak nan kana iya shiga wurin
Malam Ibrahim ta ko far waje ba lare da ka biyo cikin gida ba.
Ran nan Malam Abdu ya shigo gida rike da carbinshi
yana ja a hankali da alama daga masallaci yake don yanzu aka
fito sallar Ia'asar kai tsaye ya wuce daki, Goggo tana kicin
tana Kokarin shirya miyar masar gobe bata ga shigowarshi ba
ya dan zauna kadan sai ya lcko yana ceWa ni fa ban cika son a
ga na shigo sannan ayi biris dani ba goggo ta yi maza ta fito ta
barwa yan aikinta tare da Amina cikin 1ana cewa yi hakuri
Malam ban ga shigowarka ba, ta shigo tana cewa sannu da
zuwa Malam ka yi hakuri kasanni na fi son a yi komai kan
idona in ya so in bar musu su karasa ta miko mishi kwanon sha
da ludayi akai ta nemi wuri ta zauna kan tabarma tana cewa ga
fura nan tun dazu na dama maka ita baka shiga ba ya ja
kwanon furar yana sha ya ce e, akwai abinda ya tsareni Alhaji
mainasara ne ya aiko yana son ganina shi ne na je in ji kiran, ta
ce to Allah ya sa lafiya ya ce a'a lafiya ya tambayeni ne game
da yarinyar nan Amina kin san na gaya miki a mitin din
masallaci da muka yi ran nan mun zabi Malam Ibrahim ya
zama limamin mu ta ce haka ka gaya mun ya ci gaba to ai kin
san shi Malam bashi da mace don haka Alhaji Mainasara ya yi
mishi magana kan tunda ga shugabanci an bashi ya kamata ya
yi iyali don akn mmutuncinshi to wai shi Malam din ya cewa
Alhaji akwai yarinyar da yake gani a gidan nan a yi mishi
bincike akanta kin ji dalilin kiran da ya yi mun ya ji in bata riga
ta tati miji ba, na gaya mishi bata 1sayar da wani ba don yau
iddar tata ma bata fi kwana bakwai da cika ba, Goggo Kande ta
yi murmushi ta cc ai kuwa Malam inda wannan mutumi ya auri
Amina zata mori miji don kuwa zala haili kyawawan ya'ya ga
uwa uba ya yi karantar da ita addnin, Malam Abdu shima ya yi
murmushi ya cc to yanzu kika yi magana, ta ce amma mu wani
hanzari ba gudu ba ni la na dauka mutumin nan sadaka yalla ne
ko kuwa?