← Book details Tabbataccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 14

Sashe 3

Tabbataccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

In kina aikata
kyawawan ayyuka ranar da dattawan unguwa suka Hhadu suka
je dubawa sai su ga ma'auninki ya cika su ce ai yar wane tana
da hankali in kuwa kina shirme in suka je dubawa ba za su
tarar da komai ba, kin ga sai su ganc baki da hankali kin ga ba
van ji dadi ba, wannan dalili ya sa kullum cikin taka tsan tsan
nake saboda ina so in an jc duba sikeli a tarar hankalina ya taru
in muka zauna muna hira dashi na kan tambayeshi baba ka je
ka dubo mun sikelina kuwa?

Sai ya kance ai ina duba miki
kuma naga alamar kina kokari don hankalinki yana ta karuwa,
in na ga zai ragu zan gaya miki sai ki yi maza ki gyara tun basu
gani ba, in ce mishi to.

An kammala bikin Zainab da kwana biyu a ran nan ne
kuma muke shirin komawa makaranta ina can cikin dakin
IHajiya ina kara gyara mata dakinta na ji sallamar Hajiya
Tafisu, wacce ita ce aminiyar Hajiyata kut da kut lajiya Babba
ta mike daga kan kujerar da take zaunc ta koma mai mazaunin
mutum daya ta barwa llajiya Tafisu wannan kujerar wani
lokaci na kan yi tunani in cc ko don girman jikinta ne yasa ake
kiranta Tafisu oho?

A duk lokacin da ta zo gidan nan ni kam
bana gajiya da kallonta akan dolc Ilajiya duk da son zamanta
kan kujera mai zaman mutum uku take hakura ta bar mata
wannan kujerar ina goge-goge na daga ciki ina hango
sharabarta na yi tunani cikin zuciyata na tabbatar in aka
dunkulcni wuri daya ban fi Kafarta guda daya ba, na ji ta fara
cewa ai na zo ne in kara yi miki ban gajiya ai kin birgcni a
bikin nan Ilajiya Ilauwa ai abinda kika yiwa yarinyar uwar da
ta haifc tan ma bata yi mala ko kusa dashi ba, Hajiya ta yi
murmushi ta gyara rama ta ce uhum ai ya zama dole ne in yi
hakan don in nunawa ALhaji ina 1ayashi murnar abinda ya yi
tunda dai yanzu kadan ake so a ga na yi wani abu ace bakin
cikinc kin san hajiya Karama da iya wuri kuwa wai ranar da
Alhaji ya kiramu tare ya gata mana cewar shi la maitala zai
baiwa Zainab me muka gani?

Wai in zan yi abin kirki sai na ce
a'a Alhaji ka rasa wanda zaka baiwa Zainab sai dircbanka?

Shi
ne ya ce shi bai dauki Maitala direba ba, ya daukeshi da ne a
wurinshi don haka kar ya sake jin irin wannan maganar ya
tuntu6i hajiya karama wai madadinta mara mun baya sai kawai
1a ce mishi ita bata da 1a cewa shi ya haili Zainab yana da ikon
yin abinda ya yi niyya akanta ba sai an yi shawara da ita ba, shi
nc ya shiga yi mata godiya yana sa mata albarka a raina na ce
ahau kin kashe kanki baki sani ba, ta kalli lHajiya Tafisu ta ce
ato ta kashe kanta mana Hajiya ita dama ya'ya kwalli uku daya
ne namiji shima gashi nan wani wawa wawa uyu?

Sannan 'yar
ki babbar an dauka an baiwa dircba to me kwaryar sama tus
balle ta kasa ta samu?

Ina ci gaba har yanzu ta duka a aljihun
Alhajin ake, llajiya Talisu ta gyada kai ta ce sai dai fa an
ubawa yarinyar dukiya gaskiya na ga sakcnki ga gida ya ce ya
bata la rinka karbar haya ga mota ya saya mata ta hawa, ga irin
wannan dukiya da ya zuba mata agidan miji gaskiya kin yi sake
hajiya babba ta yi tsaki ta ce ke kuwa wai sai ki ce ina yin sake
kullum ina gaya miki cewa Alhaji da kike ganin in ya sa kanshi
yin abu garama ki rufawa kanki asiri ki bi yanda yake so in
kuwa ba gaka ba to zaki tonawa kanki asiri ne kawai shi yasa
wani lokaci na kan ce mishi ai kai da daai aka shawara da ba
mainasara akc kiranka ba da sai a kiraka Alhaji Lawal ba a
saka ba a hanaka.

IHajiya Tafisu ta yi 'yar dariya ta cc dadina
dake iya magana, 1a ce uhu cika mun ciki yake yi hajiya cika
mun ciki yake yi hajiya ta ce koda yakc dai komai ya yiwa
ya'yan karama ai sun musu aka yi dukiyar Alhaji ai tana
hannunki da 'ya'yanki tunda dai kune da gida I lajiya Babba ta
yi murmushin gamsuwa, ta ce ai ni yanzu bani da abinda vance
ukuna sai Allah ya dawo mun da llabibu gida, taliya tukuna
llajiya Talisu ta ce ni wai yaron nan ya rinka zaman turai
kenan ne ba zai dawo gida ba, ai ya shekara kusan biyar yanzu
tunda ya tafi ko?

Hajiya ta cc bai yi biyar ba ya dai kusa zai yi
hudu dai in ajin karshen shekarar nan tuntuni ya aiko ya
kammala karatunshi ya zama cikakken lauya yanzu aikinshi
yake yi a can ko salin can Alhaji yake gaya mun cewar shi
kanshi har mamakin irin dukiyar da Habibu yake aikowa da ita
gida yake yi, Hajiya Tafisu ta gyada kai ta ce ai yaron jarumi
ne tun yana dan kankaninshi shi mai nema ne gashi kuma ya
tsaya ya yi iliminshi aike taki da sauki Ilajiya ni ce dai nan
kullum abin nawa sai cakudewa yakc yi ko dayake kwanan dai
na fara samun kanshi wancan mutumin aikinshi yana da kyau
don gaskiya ina kullar dasu Hajiya tracsult nake sakawa mu
rinka tserc-tsere ni dashi lana fadin haka idon aya kai kan
tebarta ban san sanda dariya ta subucc mun ba IHajiya Babba ta
ce kin ga mun ja'ira ashe ba aikinki kike yi ba sauraron hirarmu
kike yi?

To tashi ki fita Hajiya Tafisu ta ce don Allah
kyalemun yarinyar'yar shafel-sha fel da ita komai nata mai ban
sha'awa ne, ni in banda abin nan ai da yaron nanya zo ya
nemeta Hajiya ta yi baki ta ce da kuwa kin kashe kanki dan
naki ya auri 'yar masu aiki Hajiya Tafisu ta ce a'a bari wannan
magana hajiya ba ki ji ba aka ce dare daya Allah kan yi bature
ta dalilin wannan 'yar tasu sai ki ga sun ama masu mulki ni ina
ce ma Habibu kika ajiyewa ita, Hajiya ta ce wa Allah ya
sawwake ina kar ma ki sake wannan magana wannan yarinya
da tun tana 'yar kan kanuwa ta lalace la soma bin maza gabana
ya fadi, tsoro ya kamani jin irin munanan kalaman da Hajiya ke
yi a kaina ran Ilajiya tafisu ya baci ta ce kin gani bari irin
wannan magana wannan yarinya ina ta isa wani lalacewa tun
ran nan kike cewa wai kuturinta ya dan yi fadi to ba girma ta
fara ba ni fa in ina son mutum bani son a rinka batashi a
gabana, da haka hirar tasu ta lashi mun ci gaba da harkokin
karatunmu kowanne lokaci kuma babana yana yaba karatuna
don tunda nake makarantar firamarc sakamakon bai taba wuce
ta uku ba a yanzu kuwa da nake makarantar sakandire bana
wuce ta shida ko ta bakwai duk da cakudurwarmu da 'ya'yan
kabilu bayan haka makarantar gwamnatin taraiya ta lantan
makarantace da ta yi lice wajen yayc hazikan daliban saboda
haka ina cikin jerin farko da ake ji dasu a ajinmu a wata rana a
lokacin mun kammala jarrabawarmu hutu muke jira a bamu ina
zaune a kwanarmu ni da wata aminiyata mai suna Nafi Sidi
muna hirarmu sai wata yarinya Jimmai Shehu ta z da saurinta
ta ce mun Nafisa kin ji kuwa abinda Lubabatu ke fada game
dake?

Za ta yi mun bayani na ce mata ban ji ba, kuma bana son
ji don haka yi nan ki bani wuri na nuna mata hanyar iita waje
da hannuna ta kama hanya sum sum ta fita ba a dade ba sai
gashi sun biyo Luba a baya tana tafiya tana takunta na takama
sun nufo gurina tun da na gansu na lahimci shakiyanci suka zo
yi mun don Luba ta yi mun ba sau daya ba ba biyu ba, ta ci
mutunCina a gaban yara su yi ta dariya suna isowa sai Lubabatu
ta ce wai kika cewa Jummai in ina son gaya miki magana in zo
da kaina ba in yiwo miuki aike ba?

Ban amsa mata ba sai ta ce
kina ce zan ji tsoron zuwa da kaina din ne dama ce musu na yi
babanki ba dan kasa bane lokacin da aka kori baki a lokacin
mulkin Shagari har dashi aka kora da kyar babanmu yayi ta
kaiwa da kawowa aka kyaleshi ya dawo, Nafi Sidi ta kalli Luba
sama da kasa ta ce to sai me?
Chapter 3 · 0% Book details